PART 17

2.8K 150 11
                                    


   ________TAGWAYE BY BASMA_BASHIR

             
              👇LONG CHAPTER👇

           ***************************
      
                         ENJOY👇👇                

Daddy ya'kasa barci, dare guda yashafa yana tunani dakuma mamaki alokaci d'aya. Ya rasa ga'ne dalilinda yasa Saminu yai masa irin wannan karyar da babu fasali, Bai ta6a tunanin san kud'insa ta'kai hakaba duk dacewa dei yarigada yasan yana matukar ki'shin dukiyar dayatara amma bai ta6a tunanin zai yi anfani da irin wannan hany'an sabida abun hannunsa ba.

Wannan tunanin Daddy yake har zuwa wayewar gari.

👇BORNO STATE : MAIDUGURI 👇

Sha biyun dare ko ina shiru kakeji babu motsin d'an Adam bare aljanu cikin gidan. Saminu tare da Matarsa yake cikin d'aki suna barci mai kwanciyar hankali. Shegiyar 'karar datake fitowa daga waje yasa duk suka taso a razine. A tsorace Aisha tarirrike mijinta yayinda take zaro idanuwa tana Kuma tambayarsa abindake faruwa shima kwata kwata yarasa meke faruwa cikin gidan 'Innal lillahi wa Inna ileihi rajiun' Addu'ar datazo bakinsa duk karancewa yake jikinsa na rawa. 'Karar dasukaji kuwa matsowa take tamkar sautin 6alle kofa. Yai ajiyar zuciya yami'ke cikin sananin tashin hankali yahasko wutan d'akin sannan yaja kofa yafice cikin duhu yaji an chapke wuyarsa ankuma rufe masa baki da wata aba nan yafara ihu cikin wuya babu wandake jinsa. Nan ne mutanen suka kunna wuta Saminu ya d'aga Ido ya kallesu, wasu katti ne sosai sunkai su goma fiskokinsu kuwa duk arufe suke tamkar Yan fashi.

Zagayeshi sukayi da bindigogi, inda yake zaune a tsakiyarsu wannan lokacin idan ka yanke jikinsa dawuya kasamo jini sabida a tsorace yake raz!!!. 'daya daga cikin sune yai magana cikin wata katon murya yace "Tasowa zakayi kakawo mana cikon kud'in gidan Maisha daka tseyeta million Uku saura million Bakwai sabida million Goma kukayi. Idan Kuma kaki yanzun nan zamu parpasa kanka da bindiga.

A wannan lokacin ne Aisha tafice daga d'aki ta lekosu a tsorace ta rapka ihu tana kuka nan da nan jikinta yafara d'aukan zafi tana rawa 'kar_Kar_Karr, Dakyar tabud'e Baki tafara magana "Dan Allah Kar kukasheshi kudubi girman Allah ku kyaleminshi. Bata karasa kalamanta ba d'aya daga cikin mutanen ya janyota, aka d'auremata ba'ki itama suka jefota kusa da mijinta.

Nan ta zauna tana mamakin abunda mutanen suke nema gunsu, tun tuni take kokarin magana amma babu hali dashike duk an d'aure bakunansu. Falon suka wargaza babu abinda suka gani sannan Kai tseye suka shige d'akunan gidan suma duk sun binciko babu abindasuka gani. Sannan ne suka dirko Babbar Falo inda suka tarar dasu anan wajenda suke ko motsi basuyiba bare suyi kokarin guduwa ko kiran y'an Sanda.  "Kai!!! Ina ka ijiye kud'aden gidan Maisha? D'aya daga cikinsu yadaka masa tsawa yayinda yai pointing insa da bindiga babu tsoro ya gyara bindigarsa deden sakewa yace; Zaka kawo kud'aden ko kuwa.
Aisha kuwa se kuka take tana tsananin mamakin maganganun da mutanen sukeyi "Alhaji wasu kud'ad'en Maisha ka d'auko Dan Allah kabasu sutafi wallahi zasu kasheka.  Tafad'a cikin nunfashi d'aya.
'Kasa magana Saminu yai jikinsa na rawa yanakuma had'a gumi, tunanin dayake dei itace Ina zai samo Million bakwai shida ko sisi yanzu bashida ita, gidan ma da'ake magana ya tseyar da ita ya biya basussukanda kotu kebinsa. "Inna lillahi wa Inna ileihi rajiun' sunan Allah yafara ambata tareda addu'oi yana kuka dakuma Salati duk alokaci d'aya.

"Paaaaaaaaaa!!!!! 'karar bindigar da mutumin ya sake kenan, Kwantawa Saminu yai flat ya sume adedei lokacin duk dacewa bindigar a sama aka sake ba akansaba. Aisha kuwa nunfashinta ne ya tsinke Raz!!! Zuciyarta ta'kara tashi tana tambayan mutanen wasu kud'ad'e suke magana. Ai kuwa Labarin gidan Maisha duk suka kwaso alokacin suka tsanar da ita. Mamaki ce sosai ta bayyana a fiskarta "Shine kwata kwata batasan da maganar ba, Toh ma shin Maisha ce ta aikosu gidan kenan sabida a anso mata kud'aden ta. 

Tagwaye (Identical twins) Where stories live. Discover now