PART 33

2.2K 121 16
                                    

IDENTICAL TWINS BY BASMA BASHIR.

👇ENJOY 👇

"Inspector babu shakka abunda Matata take fad'i Gaskiya ne. Ta6e Baki Inspector Bashar yai, Ya'kara zuba musu ido "Alhaji ban musa makaba toh amma dei gaskiyan magana bazaku samu damar ganin Miemah ba sai kun gabatarmana da shedu masu karfi wanda zasu tabbatar mana cewa batada hannu wajen kisan Asad, Maisha ce ta kasheshi kamar yedda kuka fad'a.

"Bawan Allah idan bakabarni na'ga Y'ata awannan lokacinba wallahi zan iya rasa rayuwata, so nake in roki gafararta Inspector kadubi girman Allah kakaini wajen y'ata. Wuf!!! tamike cikin zazzafar hawaye ta kwance gabansa "Maisha ce ta kashe Asad wallahi Miemata batada laifi kadaku d'auki hakkin ta.

Daddy ne yami'ke nan ta'ke yana kokarin shawo 'kanta. Amma inaa ta'kasa Jin abinda yake fad'a anan kasa tazube sai kuka da tunani, babu yedda Daddy baiyi da itaba amma da dukkan alamu hankalinta tai nisa.

A fisace ya daka teburin inspector ransa abace ya daka masa tsawa" Musulmine Kai kuwa, wani irin rashin imani ne Wannan kana ganin matata tana cikin wani yanayi Amma ka 'kasa bata abunda take bu'kata.

Doguwar nunfashi Bashar ya sauke inda ya kad'a Kai" Alhaji kayi hakuri Miemah tana d'akin horo Kuma gaskiya abu d'aya ce Tak! Zata iya fidda ita cikinta shine idan kun kawo shedar dazata gamsar damu cewa batada hannu wajen wannan case d'in.

"Shut up" Daddy ya damke collar rigarsa inda ya had'e hakoransa yana magana cikin zafin rai" Idan Matata ta rasa rayuwarta tsanadiyarka, Inspector wallahi wallahi i won't spear you. Dasauri Bashar yaja da baya "ASP Nasir, Security. 'Daga murya yai Yana ambaton sunan Security.

Shiruu Daddy ya tsaya awannan lokacin Yana binsa da kallo, Sanda ya'kure Masa Ido sosai sannan ya bankado kofa yafitce, yana fita yai kacibus da mutanen gidan Zabir "Zaid, Ma'inah, Mamy, Aunty Nasiba dasauransu. Bai tankamusu ba, duk sunamasa magana amma babu amsarda tafito daga bakinsa, "Ma'inah kije ki kula da Mahaifiyarki yanxu zanje inkawo shedarda zata fidda Miemah daga wannan sharrin da aka kalamata. Yashafa kanta sannan yabar wajen.

Jiki a sanyaye Ma'inah ta gyad'a kai. A zuciyarta take farin cikin dawowar Mahaifin nata gida sabida ta' san koda wasa Daddy ba'zai ta6a barin Miemah awannan wajenba coz itama amasayin y'a yad'auketa.

"Ma'inah meye kikeyi awaje kowa ya shige ya barki. Sai yanzu tadawo cikin hayacinta inda tahango sauran chan cikin office.
Come on Ma'inah kizo mukarasa ciki don Allah", Kam kace kobo Anisa ta janyo hannayenta aguje suka shige offishin tamkar wa'inda suka fado daga sama.

Ma'inah be careful" Zaid ya mike nan ta'ke ya riketa ayayinda take kokarin fad'uwa, A tsawace yajuye 6angaren Anisa "Meyesa kika janyo Ma'inah haka, What's if she fall?
Zunbura baki Anisa tai tana binsa da kallo cikin 6acin rai, azuciyarta take tunanin "How dare him meyesa zai kunyatani a cikin bainin jama'a".

"Ma'inah, Mahaifiyarki tana chan ba'kin cell tana kuka, yaukuma bansan dawace irin kisisina tashigo mana nan wajen da itaba". Da wannan maganar Aunty Nasiba ta karaso inda suke inda ta'kara dacewa "Kowa ya'san dei Safeenah ba'ta jituwa da Miemah wace gulmar ce takawota nan wajen tanata damin mutane da koke koke sekace wacce tarasa iyaye.

Momy kuma? Meyakawota nan? Kuma meyesa take kuka. Kije kiji daga ba'kinta, Fad'ar Mamy. Kad'a kai Ma'inah tai "A'a Mamy barta kawai na'san duk yedda akayi momy da Maisha sunada hannu kuma babu shakka su suka kalawa Miemah wannan sharrin sabida haka bazan ta6a bin bayanta ba. Da 'karfi Aunty Nasiba ta kad'a guud'a "yeuwa y'ata gaskiya wannan mahaifiyar ta'ki bata kamaceki ba. Shiruu Ma'inah tai yayinda take kokarin hana hawaye sau'ka daga idanunta. It's Okay, Zaid ya janyota gefe "kada ki hana kanki kuka Ma'inah coz it will affect you... Yana fad'an wannan ta rungumeshi kai tseye tafashe da kuka.
***
A yanzu y'an sanda sun taru awajen trim! Daman interview ce takawosu, Mamy da Aunty Nasiba sun amshi tambayoyinsu cikin nitsuwa hakama Anisa da Mainah, akarshe Zaid ne yabasu nashi bayanan sannan shima ya amshi nasa tambayoyin.

Tagwaye (Identical twins) Onde histórias criam vida. Descubra agora