PART 16

2.5K 134 9
                                    

Greetings🤚  from the Lead female character "Ma'inah; Hello Tagwaye Fans mungode da nuna mana had'in kan dakukeyi akoda yaushe, Kucigaba da bin labarinmu zakuji dad'i sosai zakuma ku sha ababen mamaki, al'ajabi dakuma tausayi awasu 6angura, Keep on following. Ta ku Ma'inah Sambo Maidugu.

         *************************

  ________TAGWAYE BY BASMA_BASHIR

Bayan Ma'inah ta sha kuka a kofar Part d'in Zaid, Tamike jiki a sanyaye tai 6angarensu duk dacewa tanasan tashige 6angaren nasa domin taduba halinda yakeciki tareda Munah amma babu halin yin hakan sabida ko kad'an bata mance da maganarda Asad yafad'a mata alokacinda tazo gidanba cewa Zaid ba yasan ashigemasa 6angare kuma kowa na bin umarninsa agidan Aunty Rahila ce kad'ei take da damar zuwa tareda shi Asad d'in dakuma d'iyarsa Munah.
Ako yaushe alakar dake tsakanin Zaid da Munah takan ba ta mamaki dakuma rud'ani, tun ranarda Asad yafad'a mata cewa Munah Y'ar Mahaifiyar sace tafara tunanin cewa akwai wata 6oyeyyen lamari tattare da Zuri'ar ta su. Amsoshin datake san samu akansu shine, Wacece Mahaifiyarsa? a ina take? Kuma shin a ina Mahaifinsu yake wanda ako yaushe takanji suna maganarsa amma bata ta6a ganinsaba ko sau d'aya. Shin Zaid shi kad'ei neh d'an Muhammad Zabir kodei yanada y'an uwa? Meyasa Aunty Rahila tamaya gurbin Mahaifiyar Zaid? Wani dalili yasa Zaid yai adopting 'Kanwarsa Munah? Kuma meye dalilinda yasa Zaid yakeda yawan fushi akoda yaushe sabida da dakkan alamu Mutumin 'karki ne bashida hayaniya.

Duk wannan tambayoyin sunada amsoshi sedei a6oye suke babu wanda yasani se su Zuciyar Zabir dakuma Allah Subhanahu Wata'ala.

**** Innalillahi wa Inna ileihi rajiun, Innalillahi wa Inna ileihi rajiun' .  Hayaniyar dataji akeyi cikin falon Aunty Rahila ce takatse mata tunanin, Nan ta kula cewa harma ta 'karaso 6angarensu. Babu abunda kakeji cikin falon se koke koke da alamun tashin hankali a tsorace Ma'inah tasa 'kafa zata 'karaso ciki kenan taji muryar wata Mata tanacewa "How did she mannage to escape? (Ya akayi tabar gidan Ya'rin?) Don Allah Wannan maganar ta tseya anan kada asake Zaid yasani, Kuma dole se an kamota takoma gidan ya'ri.
Aunty Rahila kuwa se aikin kuka takeyi ba ta cewa komai. Nan da nan Gaban Ma'inah yafad'i tafara zazzaro idanuwa tana ha6e hannayenta kwata kwata ta rasa abundake faruwa agidan kuma dei dadukkan alamu akwai matsala babba wacce Kuma ba'asan Zaid yasan hakan. Tausayin Zaid ne ya'kara shiga ranta sabida wannan al'amarin ne yadad'a tabbatar mata cewa akwai babbar matsalar dake damin Zaid wanda kuma idan Allah ya yarda zata shige rayuwarsa domin tayaye wannan matsalar dake daminsa takuma sany'a farin ciki arayuwarsa.

Da wannan tunanin tasa'ke juyowa kai tseye tai hany'an waje, zuciyarta na bala'in bugawa, gabanta na fad'i, jikinta na karkaruwa har takai 6angaren nasa (Zaid). Inda Kai tseye tabud'e kofa tashige. Wannan ake 'kira al_jannatud dhunya mansion ne guda ginin Zamani mai cikeda guraren sauke gajiya da kayan more rayuwa. Sake Baki Ma'inah tai tanabin gidan da kallo cikin tsananin mamaki. Bata ta6a tunanin haka gidan takeba har Sanda tashige taganewa idanuwarta nan taga'ne cewa wannan matsayin da ake nunawa Zaid matsayin sane sabida yanada gata tun agida.
Da wannan tunanin tacigaba da shigewa tana dudduba ko ina tana mamaki har Sanda wani d'an Sanda ya tsei da ita "Madam ina Zakije?   Kai tseye ta amsa masa cewa "wajen Zaid tazo'. Ya San da zuwarki neh?  Kad'a kai tai "A'a bai saniba. 
Daganan mutumin bai sake cewa komaiba, wayarsa yad'auka kurun yakai layin Zaid yana 'kiransa. 
Dasauri Ma'inah ta dakatar dashi "Ba se ka kirashiba Zan koma yanzu. Juyowa tai asulale tai hany'an waje inda wannan securitin yasa'ke tsei da ita Yana mikomata wayar dake hannunsa. Da Idanun mamaki tace Me zanyi da ita?  Yace kuyi magana. Ya amsa mata.

Hannunta na karkaruwa ta kar6i wayan tasa a kunne, muryan Asad taji yanacewa Ma'inah kiyi sauri kikaraso ciki akwai matsala. Wace irin matsala? Tana tambayansa yakatse wayar batareda ya amsa mataba. Haka Mainah tamiko masa abarsa cikin sananin damuwa ta'karaso ciki tana shigan Compound tafara tambayan Security inda zata tsameshi. Yashedamasa mata cewa Yana PoolSide. Sannan yanuno mata 6angaren sabida Pools sunada yawa cikin gidan. Kai tseye ta'karaso wajen.

Tagwaye (Identical twins) Where stories live. Discover now