PART 30

1.8K 123 6
                                    


_____IDENTICAL TWINS BY BASMA_BASHIR

Innalillahi wa Inna ileihi rajiun', laa haula Wala kuuwata illabillahil azizul hakeem', Hasbunallahu Wani'imal wakeel,:

Sai addu'oi mommy keta nanatawa tun zuwan Sojoji gidansu, tana tsaye a ba'kin kofa kafafunta duk suna 'karkarwa, ayau jitayi tafara da'nasanin shugwa6a Maisha dakuma bin bayanta datakeyi tun tana kankanuwa, A zuciyarta take 'kara sanyawa Ma'inah Albarka yedda ha'laiyarta duk suka banbanta data Y'ar uwarta.

Cikin wannan zunzurutun damuwa da tunani momy takoma d'aki. Sai aikin leke leke take tana Allah Allah aranta kada sojojin nan sugano Gaskiya adawo gun Maisha a kamo mata y'a. Wannan tunanin take har sanda ta kwaso dikkanin kayayyakinsu tana kammalawa wayarta ta lalube jikinta duk rawa take yayinda tasa layin Ma'inah Kai tseye tadanna, abugu d'aya Ma'inah ta d'aga "Yi maza kitaho gida," abunda tafad'a kenan, bata jira amsarda Ma'inah zata maido mataba ahaka ta katse wayarta.

Daga nan d'akin Maisha tawuce arazine tafad'o ciki aiko babu kowa cikin d'akin Maisha ta'kara tsere mata "Inna lillahi wa Inna ileihi rajiun' Zama tai anan tafashe dawata sabuwar kalar hawaye, Maisha zata doura mata hawan jini takuma yi tsananin mutuwarta, Ko a Ina taje? Ko me taje kullawa kuma???.

****************************

"Dallah Malama kada ki raina mana hankali mana wannan uban aikin damukayi miki yaci ace kinbamu dubu hansin amma meye zamuyi da dubu ashirin"? Cikin Sananin sauri Maisha tace' Dan Allah kuyi hakuri dubu ashirin gareni wallahi amma idan na'samo cikon zan biyaku, kun tabbata dei aikin yayi kyau.

Wani kato cikinsu ne yafashe da dariya 'ai yanzu na shedamiki Hajiya Turai babu wanda tafi tsana a duniya irin d'anta Zaid sabida dasunansa mukasa y'an Sanda sukaje suka kamota yanzu hakama nasan bata gama mamakin butulcinda d'anta ya aikata mata ba sabida alokacin da aka kamatanma cewa take Zaid da mahaifinsa zasuyi da'nasanin idan tafito.

Tapi Maisha tabuga, tapin Farin ciki, washe hakora Tai tanacewa' Shegu d'aya ba'yan d'aya sai na gurbata rayuwarsu ba'zasu ta6a zama cikin farin ciki ba har abada yanzu kuma saura babbar shedaniyan MA'INAH nagama da Miemah nakuma gama da Zaid.

******************************
Cikin wata barkaceciyar d'aki aka jefo Miemah, d'akin duk datti ga wari da kazanta, tinda aka kamota babu wanda yata'ka wajen bare tasamu damar tambayan abinda ke faruwa, abinda ke Kara d'aure mata kai Kuma shine sauyawarda momy da Maisha sukayi ayau ta tabbata basuda Gaskiya, A zaune take shiru a bakin kofa Babu abinda yacika zuciyarta sai tsanar Mommy da Maisha tana Kuma mamakin sharrin dasuka Kara 'kala mata awannan karon.

*******************************
Tun lokacinda Mainah taji cewa Miemah ce tayi kisa ta'kasa yarda da batun, kwata kwata ta 'kasa gaskanta maganar hakan yasa sukayi fad'a da Zaid sosai sukayi hayaniya agida yace idan zata kara musa maganarsa tabar masa gida sabida yafi karfin yafad'a tafad'a, Wannan yasa Ma'inah tabar gidan kamar yedda ya umarceta. Aunty Rahila dasauran mutanen gida duk basuda bakin magana, da'man idan ran Zaid ya6aci babu mai chanza masa shawara.

Tana ofishin lawyer ayayinda momy Ta'kira cewa 'tai maza tazo gida"Amma bata damu da maganar ba, hankalinta duk nakan Y'ar uwarta wacce aka kama batasan hawaba bare sau'ka.

*****************************
Momy tashafa awowi dadama tana zaman jiran Ma'isha Amma Babu alamarta haka ta lalubo wayarta ta'kira Daddy, kame kame takama batasan inda zata fara 6ollo Masa da maganar ba.

"wace irin magana kakeyi haka Alhaji dan Allah nidei kawai kahad'o Mana Urgent flight dani da Maisha da Mainah zamu taho America mu tsameka.

Muryar Daddy ya'nuno mamaki sosai yayinda ya'kara tambayarta' Safeenah wallahi na'san akwai abunda kike 6oyemun, sabida babu yedda za'ayi haka kawai kicemun zaki dawo America tareda Yara kusameni, Gaskiya akwai matasala, fad'amin menene? Momy ta'rasa inda zata fara 6ullomasa da Maganar" Bukatarka nake kuma Gaskiya bazan iya jurewa ba.

Ya'rigada ya'gane wannan maganganun datake duk karya take jeromasa, "Toh why not kizo ke kad'ei banda Yara, sukuma meye zasuzoyi? Jikin momy na rawa awannan lokacin ta rasa inda zata 6ullo Masa, gabanta har fad'uwa take koda taga'ne cewa Daddy ba'zai ta6a gamsuwa da wannan fake maganganun datake tsaromasa ba, ajiyar zuciya tasau'kar kai tseye tafara furta Gaskiya d'aya ba'yan d'aya duk ta fad'a Masa har Sanda ta'kai inda y'an Sanda suka kamo Miemah Sannan Daddy ya dakatar da ita.

Dakata Safeenah, Yai saurin katseta Ma'isha ce tai kisan sannan kika rufamata asiri aka kamo Miemah? Cikin hawaye momy ta gyad'a Kai "Toh yazanyi kaima kasan bazan tonawa Y'ata asiriba na gwammace duniya nan duka su wahala akan jinina Ma'inah da Maisha su wahala....

Daddy yayi shiru nawasu lokaci, sannan yasaukar da ajiyar zuciya yace'
SAFEENAH, MAISHA BA JININKI BACE, Ki gafartamin na 6oyemiki sirrinda baikamata na 6oyemiki ba amasayinki na MAHAIFIYAR MIEMAH...... Dakata Alhaji, chak!!! hawayenda suke zubowa a idanuwan momy suka tsaya "Meye kake nufi? Alhaji kada son Miemah yasa ka aikata laifinda Allah zaiyi fushi da kai, wace irin magana kakeyi haka?

Akwai wata tsohuwar takardar da na ijiye cikin wata kwali a karkashin gado na, wannan takardan tun ranarda kika haihu na rubutata kuma ina ganin ayau ce anfaninta tazo, wannan takardar ce kad'ei zata iya gwada miki gaskiya ayanzu.

Sake wayan momy tai jikinta duk na rawa yayinda takoma d'akin Daddy, tana gumi sosai ayayinda tabude wannan kwalin

................................ ...............................
................................ .............................
................................ ................. ..........

Momy tana gama karanta wannan littafin jiri ya kwaso ta Nan da nan ta zube awajen ta Suma.

🚫PART 31 SPOILER🚫
Maisha ce ke zaune agefen momy dake kan gadon Asibiti, a kwance take ba'ta magana bare motsi, jikinta tsit! Tamkar matacciya, likitoci sai aiki suketayi akanta Amma sunyi iya ba'kin kokarin babu mafita.

Hannayenta dika biyu Maisha ta damke tana hawaye"momcy Dan Allah kitashi kada kimutu kibarni Dan Allah momcy Kitashi sabida ni. Cikin wannan yanayin suke har tsaida hankalin momy tadawo jikinta Amma abinda ya daurewa Maisha kai shine umartar likitocinda tayi cewa akoreta daga wajen ba'tasan ganinta kusa da ita.

Maisha ta rasa ga'ne dalilin hakan, lissafi duk tagama a 'kanta amma bata ga'no dalilin dazaisa momcy take gudun Maisha'n ta ba sai dai idon gamuwa tai da ta6on hankali.

🚫PART 31 SPOILER END🚫

TRUST ME 👇👇👇
#NEXT CHAPTER IS GONNA BE GREAT 👍 KEEP FOLLOWING ❤️.

BANIDA LOKACI SOSAI SHIYASA WANNAN SHAFIN TAI KA'DAN AMMA DA YARDAN ALLAH ZANYI KOKARI A SHAFI NA GABA.

PLEASE KU'DAN 'KARA HAKURI EXAMS MUKEYI SHIYASA BANA UPDATING AKAI AKAI.

VOTE
COMMENTS
SHARE

DUK MAI FAHIMTAR WANNAN LITTAFIN SOSAI YA RUBUTO ALBARKACIN BAKINSA.

Tagwaye (Identical twins) Where stories live. Discover now