PART 31

2K 168 26
                                    

IDENTICAL TWINS BY BASMA BASHIR___

Karfe biyar da rabi ta yammaci Ma'inah da Barrister Ibrahim suka karaso police station, Sunko isa adedei lokacinda yakamata. Zaid dasauran abokanansa da Yan uwa harda sojojin kasashen waje duk sun kai ziyara wajen, inda sukasa Miemah asakiya Yan jarida sunata tapka rahotuna tareda aikin d'aukan hotuna masu yawa, awannan zuwansu ne Miemah tasamu damar jin laifinda ake tuhumarta da shi, duk dacewa ba' tada hannu wajen kisan Masoyinta Asad, Miemah batamu'sa ba, Kai ko kalma guda bata 'kara furtawaba, jikinta tayi matukar sany'i tamkar 'kankara, kwakwalwarta tayi matukar kad'uwa dajin wannan mumunar labarin. Tsabar mamaki da kad'uwar da tayi ko hawaye basu sauka a idanuwarta ba tsit take zaune a tsakiyarsu babu abinda ke motsi a jikinta sai zuciyarta dake matukar bugawa tamkar ganga, idan kayi mata kallo d'aya zaka sheda tana dab da kamuwa da masananciyar ciwon zuciya idan ma ba'ayi sa'aba bugawa zuciyar tata zatayi tabar duniyar gaba d'aya.

Inna lillahi wa Inna ileihi rajiun' Furucin Ma'inah kenan ba'yan ta shige cikin ta'ron mutanen taga irin Halinda Miemah ke ciki, ihu tafara bugawa tana neman taimako "Dan Allah ki taimakawa yar Uwata. Tana kuka sosai yayinda tarike hannayen Mamy tanacewa' Mamy ki taimakamata wallahi mutuwa zatayi, yanzu ma hankalinta ba'ta jikinta Mamy please Dan Allah ki taimakamata Miemah ce fa yarki wacce kike alfahari da ita.

Duk ta'gama surutanta Mamy bata tankamata ba, juyowa tai tana nunamata Zaid yayinda hawaye suke sirnanowa a idanuwarta tace" Y'ata kije wajensa kinemi alfarma kila ko kya dace yabari akaita asibiti.   Sam Ma'inah ba'tasan zuwa wajensa sabida abubuwan dasuka faru tsakanin su, Wanda har tsanadiyar hakan yakorota daga gidansa, Amma awannan karon yazama dole taje domin taceci ran Y'ar uwarta Miemah.

Sunkuyowa tai adedei inda yake" Zaid. ✋ Excuse me Ma'inah get the hell out of my side I don't have your time. Da wannan shima yajuye yai tafiyarsa inda hawayenda suka dad'e cikin idanuwarsa suka fara gangarowa kai tseye.

Barrister Ibrahim ne yataho wajen adedei lokacin inda yake rarrashin Ma'inah "Ba komai Ma'inah yanzu zan barki anan, Niko zan koma office domin na'samo mana appeals emergency,   Idan nasamo wannan yazama dole ayi mana uzuri duk lokacinda tai rashin lafiya shari'a tabamu damar kaita asibiti.

Mikewa Ma'inah tai kamar yedda ya umarceta inda takoma chan gefe tazauna abar tausayi tana kuka jijiyoyin wuyanta duk sun fito suna nuna irin bakin cikin datake ciki awannan lokacin.

Zaid ya'kasa matsowa daga inda ya tseya tun tuni yake tsaye wajen motarsa yanabin Ma'inah da ido, kamar yedda take 'kara zubda hawaye haka shima yake zubarda nasa hawayen tamkar d'an karamin yaro. Kasa jurewa yai "I can't see her in pain, Tseyawa yai ya'kara kuramata ido "Ma'inah meyesa kike d'aurawa kanki laifin wani, Ina sonki Ma'inah kuma ba'nasan ganinki cikin damuwa.  
Ahaka ya'karaso inda take, Yana isa ya daura kafafunsa a kasa babu fargaba yace "Ma'inah please forgive me, I'm sorry🙏, Cikin sassanyan murya kamar yedda ya'saba.

Duk dacewa Ma'inah taji abinda yafad'a kauda kanta tai, takoma d'ayan 6angare tacigaba da kuka. Mikewa yai yabiyota "Ma'inah please talk to me meyesa kikemin haka? Mikewa tai tana kokarin barin wajen kuma, Nan ya rungumeta tamkar 'Da da Uwarsa "I love you Ma'inah.

Bai rufe bakinsaba ta bankadosa daga jikinta "And I hate you Zaid, Da karfe ta'kara fad'a" I hate you Zaid Muhammad Zabir ko a hany'a kaganni I plead with you kada kanuna ka ta6a sanin Ma'inah Sambo Maidugu and that's Final.  Tana fad'in wannan tajuye da niyar tafiya inda ta'kara jinsa a jikinta ya la6e tamkar jinjiri, sabuwar hawaye yafashe "Ma'inah please tell me how can I live without Asad, Ma'inah how? Asad ya tafi yabarni, Ma'inah bazan iya rayuwa batareda shiba. Kema so kike ki gujeni sabida yar uwarki ce ake tuhuma wajen kisan aminina, Yes na rabu da Asad amma bazan iya rabuwa dakeba, fad'amin sokike abar Miemah tatafi haka kawai batareda an d'au hukunci ba? kiyi tunani sosai Mainah idan munyi hakan munyiwa Asad adalci kenan?

Tagwaye (Identical twins) Where stories live. Discover now