PART 13

2.3K 157 15
                                    

                   #New policy#
                       👇👇👇

                   No comment
                   No update ⛔
                              👇

Idan Kuna bu'katar Update a ko wace Rana tse ku kasance kuna comments aduk shafinda narubuta hakan ne zai 'kara bani 'karfin guiwa wajen tsara littafin yedda Mai karatu zaiji dad'inta Sosai. Wannan dalilin yasa nakawo sabon do'ka a littafin: "No Comments No Update" ma'ana idan babu Comments bazanyi updating wani shafi ba Saboda aganina 6ata lokaci na nakeyi babu mai biye dani, then maybe I will just stop writing if u dnt like the story "TAGWAYE".
Thank you so much I hope you will all cooperate❤️❤️❤️

_______TAGWAYE BY BASMA_BASHIR

Hannu ta d'aga musu "Hello, Ina yininku, tai musu sannu cikin wata tsiririyar murya" toh yanaga kun tseya anan, ku 'karaso sama man anan falon Daddy yake? Ko dei ba'kin Momcy ce. 
Asad ne ya amsa mata cikeda fara'a yace"Tare mukazo da 'kanwarmu Ma'inah, jikin Alhaji Sambo mukazo dubawa.

Wani dammm!!! Taji azuciyarta, daman ashe wannan ne Saminu yake kokarin tsanarda ita, toh ashe shiyasa yace Daddy ya 'kai Ma'ina gidan daula ita  kuwa ko oho ya barota anan tana shan 'bakar wahala da azaba.  Cikin matukar kad'uwa da mamaki tace' Taya alakarku tahad'u da Ma'inah? Kuma a ina kuka santa wanda har kanawani zagewa wai ita 'kanwarku, Anyway banama yi dakai Zaid dakai nake magana meye yahad'aka da Ma'inah?  Manna mata hauka yai tamkar ba dashi akeyiba, ko motsi baiyi ba bare yad'aga Ido yakalleta, iPhone X_plus dake hannunsa yacigaba da daddannawa.

Ma'isha bata 'kara tan'ka musuba haka  tahauro aguje tana kwala ihu, sunan Ma'inah take ambata har takai Falon Daddy, Momcy ce take wajen tareda Daddy suna tattaunawa se dariya suke suna nishad'i "Ma'inah tana nan third floor hauro ki tsameta' Momy tafad'a cikeda fara'a ta'kara dacewa Ni kaina nayi farin cikin ganinta sosai jeki tsameta Y'ata I'm sure you miss her...  Da'kata momcy🤚 Daddy kunsan wa nagani a parlour kuwa.  Girgiza kansa yai alaman a'a.  Toh Zaid Muhammad Zabir, ZMZ Bulders CEO dakansa tareda Assistant d'insa Asad Abdallah su nagani a parlour'n mu yau.   Zaid Muhammad Zabir kuma. Daddy yami'ke cikeda mamaki yaushi suka zo kodei tare suka taho da y'arinyan nan Ma'inah.  Bai tseya Maisha ta'kara wata maganaba nan ta 'ke yatafi se wani rawan jiki yake yana zumudi tamkar yau aka farayin ba'ki agidan.

Sake ba'ki Maisha tai tana kallonsa "Iyee su Daddy many'an 'kasa ashe dei anrigada anyiwa Y'ar gata future planning ankaita chan gidan masu arzikin duniya tana shan sha'ani, Ni ko anbaroni a nan gidan 'kasa.  Shiru tai tana jiran amsa daga wajen Momcy. Mikewa tai itama tamkar bata saurari mitar da Maisha take ba, cikin fara'a da tsannanin Farinciki tabi sahun mijinta "Yau munyi babban Baki a gida ZMZ Builders CEO dakansa ba aika ba maraba marabanku.  "Mumcy ki tseya ki saurareni man Daddy ya'ci amanata, yaci zarafina Kuma ya fifita Ma'inah sama dani Momcy please kidawo gareni ke kad'ei ce mai gaskanta damuwata mummy kada kibarni. Zubewa a 'kasa tai inda tafara rusa kuka tana da'nasanin rayuwarta, Ma'inah you destroy my life wallahi se  naga bayanki and you will never be happy I promise.

Share hawayenta tai "I need to be strong and I need to earn Momcy's trust again' jiki a sanyaye tahaura falon sama nan tahango Ma'inah achan tana tseye adedei window tana lekowa kuma da dukkan alamu Zaid take gani sabida ko kiftowa idanuwarta ba 'suyi.  Idanuwarta suna hawaye yayinda takure mata ido tana bakin ciki, zuciyarta na tafasa tse huci take tamkar kare 'Mainah why did you have to take everything from me, wani laifi na aikata kike sa'kamin da wannan Bakar sakamakon.

Ma'inah batasan hawaba bare sau'ka, Jin Maisha kurun tai abayanta kamar daga sama inda tafara bubbugeta da sandar dake hannunta tana janyo gashin 'kanta tamkar igiya daganan suka ta' da fad'a. Falo duk sun wargaza glasses duk Maisha ta parpasosu kan Y'ar uwarta kujera duk sun tangale up side down, har TV tayi kokarin cirowa amma ta 'kasa se ihu suke suna fad'a kamar gidan dambe. Daddy Ma'inah take ihun 'kira amma babu amsa ganin sunyi sama sosai babu mai sauraransu "Mommy, Daddy harma da Zaid tafara 'kira a yanzu.  Ma'isha Koh ranta se 'kara 6aci take tana 'kara jibgeta.

Gudu Ma'inah tafara, ganin Maisha zata iya hallakata sabida kome ta'samo akanta take jefowa. Ahaka har suka sauko bene ta biyu. Ma'inah tana gaba, Ma'isha na baya tana binta da Sanda har tasauko 'kasa.  Daddy, Mommy, Asad da Zaid duk mikewa sukayi cikin tsananin mamaki Kuma alokaci d'aya.  Jinin dake jikin Ma'inah ne yamatukar tsorata Daddy inda ko minti d'aya bai 'karaba ya sume awajen.  'karshen Sandan data sauko akan Ma'inah ne yafitar da ita daga cikin hankalinta Wanda Maisha tasa duk 'karfinta tasaukeshi adedei 'kan ta.

Bibbiyu tafara ganin duniyar, Idanuwanta suna duhu duhu daga nan tafita hankalinta, Nan ta'ke Zaid ya'karaso wajen, dahannayensa yarike'ta just like a protective charm bai barota ta 'karaso kasa ba, chak!!! yad'aukota tamkar jinjira.  Ma'isha na jiran jin abunda zai fad'a amma babu infact hankalinsama gaba d'aya suna kan Ma'inah dake hannunsa. Aguje yakaita Mota inda ahankali yakwantar da ita abaya, yafara tuki. Dakyar yarike sterin yana tuki tamkar mai L. hannayensa suna karkarwa, yana nunfashi sama sama, ya 'kasa rike hawayensa zubewa suke tamkar fanfo se yau yaga' ne matsayin Ma'inah awajensa wanda ako yaushe idan yasata a idanuwarsa yakanji wani iri wanda shi kansa baisan dalilin hakanba. San Ma'inah yake har cikin jijjiyoyin jikinsa, Soyyayyarta tarigada Tashige zuciyarsa tun Rana ta farko dasuka fara ganin juna Kuma har cikin ransa ba'zai jure rashintaba.

Asad ne yad'auko Daddy amotarsa tareda momy suka tafi dashi asibiti, inda aka baro Maisha agida ita kad'ei tana jujjuyi da idanuwa ko kad'an batayi da'nasanin abunda ta aikataba akasarima aganinta daga wannan du 'kan, Ma'inah zatasan inda zata tone 'kasa tai Kashi, Daddy ko suman dayayi dedei ne alhakkin tane yafara bibiyarsa tun ayanzu, baimaga komai ba tukunna. Da wannan tunanin tawuce d'aki inda kai tseye tafara tattara 'kayanta dama sauran abubuwanda ta mallaka wandake gidan. Hoton Zaid da Ma'inah take gani a idanuwarta ta 'kasa ganin komai se fiskokinsu musamman lokacinda yad'aukota suna barin falon, yedda yakure mata Ido dakuma irin tashin hankalinda yabayyana a fiskarsa tamkar Romantic Moment a series film na India.   Se Slow Motion idanuwarta suke ganemata dakuma wakar da akasaka alokacin Duk dei atunanin nata.

Akwatin kayyakin data tattaro ta Ta' ka cikin masifar 6acin rai ta watso su 'kasa, d'aya bayan d'aya tafara wargaza su tana rangad'a ihu tamkar sabuwar mahaukaciya. "Banda Zaid, Ma'inah Banda Zaid zaki iya tsato kowaye aduk fad'in duniyar nan amma banda Zaid shi narigada nai planning future'n mu tare. Doguwar nunfashi ta saukar 'You really made the wrong decision this time Ma'inah Sambo Maidugu zakiyi da'nasanin shiga rayuwata.

          **********************

IYA ABUNDA YA SAWWAKA A YAU KENAN 🤗 KEEP ON FOLLOWING ❤️❤️❤️❤️

           🚫PART 14 SPOILER 🚫❌

Jakarsa yake turowa yana ja se jujjuyi yake yana gannin bayansa tamkar gudun wani yakeyi. Mutanen Airport kowa kallonsa suke kaman mara gaskiya.

Karo sukayi da 'Yarsa Miemah yayinda yabud'e lifta yana kokarin shigewa ita kuwa tana fitowa. Kallonta yai sama da 'kasa tana Jan 'jakarta alamun yanzu tasauko daga jirgi all the way from Maiduguri. "Me kike anan? Tambayarda yafara mata kenan. Cikeda Farin ciki tafi're sama tarungumeshi ''Abba tun shekaran jiya mukayi magana da Kawu Sambo he is so worried about me na fad'a masa  lafiyata 'kalau amma ya 'karyatani yace ba'zai yarda da maganataba har tse nazo gida Abuja sannan ne za'muje wajen likita yatabbatar masa da maganata har kud'in jirgi shi ya aikomin.....

Zufa Saminu yafara sharewa daga fiskarsa "Inna lillahi wa Inna ileihi rajiun y'an nan kin tona'min asiri na shiga uku. 

        *******************
Na tseyar masa da gidana Million Goma, na mallaka masa takardun gidan da komai harda makullai amma mutumin nan baisan ko wacece ake 'kira Maisha ba, yayi min wa'sa da hankali million Uku kachal yahad'ani da ita yai tafiyarsa yanzu ba'nida wani gida ka san cewa na bar gidan iyayena gashi nadawo nan kuwa ko ina a rufe, Nayi masa Miss Calls kusan arba'in bai d'agaba, me yake nufi, 7 million naira kud'adena dake wajensa yanzu.

Gyad'a Kai Auwal Wiski yai yana hura sigarin dake ba'kinsa yayinda yace "Na fahimceki Maisha cool down yanzu me kikeso ayi masa????

      ************************

THANKS FOR READING 👍 HOW WAS THE CHAPPY?

                      NOTE;
               👇👇👇👇👇

             NO COMMENTS
             NO UPDATE 😈

HAVE A NICE DAY 💕💕💕

Tagwaye (Identical twins) Where stories live. Discover now