PART 18

2.1K 139 9
                                    


_______TAGWAYE BY BASMA_BASHIR

👇👇ENJOY 👇 👇

A tseye take, jikinta na rawa sany'i ya shigeta sosai, hijabin dake jikintane yake d'an rufemata jiki yana taremata ruwan da iska ke hurowa kan Varrender'n. Ruwan ta'zo da iska mai sanani dakuma Thunder wanda take matukar tsorata Miemah. Kuka take tana tuna Mahaifiyarta. Ako yaushe idan ana ruwa irin wannan a gida, Kwantawa take gado d'aya tareda Umman nata tala6e har kusa da ita, Umma na ba'ta labari har zuwa lokacinda zatayi tai barci mai kwanciyar hankali. Gashi yau itace aka bari a waje cikin wannan Bakar daren ana ruwa kuma babu wandake kusa da ita.

********
Ata 6angaren Mommy kuwa ta dad'e tana barci mai kwanciyar hankali, a tsakar dare 'Karar Thunder tatasheta, A firgice tataso nan tabud'e window taga irin ruwan saman dake zubowa awaje. Maisha tatuno lokacinda take 'karama tana tsoron ruwa musamman ma ruwan dare, Snow itace kad'ei abinda take sha'awar gani itace kuma likitoci suka hanata wasa aciki sabida yanayin lafiyarta. Ruwan hawaye ne ta sirnano a idanun momy yayinda tatuna irin wahalhalun da Maisha ta fiskanta har na tsahon shekara biyar. Da wannan tunanin tamike babu inda ta tseye se d'akin 'diyar nata inda ta tsameta kwance kan tattausar gadonta tana barci, Kwantawa tai ta rungumeta kamar yedda suka tsaba kwanciya alokacinda take 'karama, Sa'ta a tsakiya suke ita da Daddy su rungumeta tamkar kwai sannan suyi barci. Ahaka mommy tai har zuwa wayewar gari.

Ana Kiran Sallah Maisha tabud'e Ido, ganin Mummy akusa da ita yasa tai murmushi, ahankali tacire hannayenta data d'aura akanta tamike a nitse tashiga ban d'aki ta d'aura alwala tafito tana ta da Sallah Mommy tata'so inda tashige ban d'aki itama tai alwala tafito nan d'akin Maisha tai Sallah tana idarwa suka koma d'akinta ita da Ma'ishan duka.

**********************
Dama ta ko'sa gari yawaye domin tai sauri tashirya zuwa airport sabida irin wannan abunda yafaru da ita ayau wanda ko a mafarki bata ta6a tunanin hakan zata faru da rayuwar taba. Alkhawari ta d'auka cewa bazata 'kara koda second guda a gidan ba ana Kiran Sallah idan an bud'e kofa zatashige ta kwaso kayanta tawuce airport, duk dacewa jirgin se la'asar zata ta'so ahaka zatayi zaman jira har zuwa lokacin. Ai ko tana idar da Sallah aka bud'e kofan Parlour, Kai tseye tashige, tana shigowa kuwa da Momy sukayi karo "Innalillahi wa Inna ileihi rajiun' abunda momy tafara fad'a kenan cikin mamaki tace' daga ina haka? cikin wannan lokacin jiki duk a jike. Zuba mata Ido Miemah tai, 6acin rai yasa ta'kasa fad'an komai haka ta chanza hanya tana wucewa.

"Wace irin rashin tarbiya ce wannan, ki kwana a gidana, Sannan ki ta'so ba Gaisuwa Ina Miki magana kuma kina wani hararata tamkar sa'ar kice ni. "Allah yabaki hakuri" Miemah tafad'a zuciyarta na tafasa tace' Ina kwana. Momy Bata amsa mataba kallonta tai diga sama har 'kasa sannan ta ta6e baki tanacewa' Karki zaunamin cikin gida haka, ki chanza wannan ji'kakkun Kaya ko kifito Rana tabusar dake, Yara ba hankali wallahi Allah ma yasoni da Ma'inata tadawo hannuna tun dawuri da wayasan irin tarbiyar da zata kwaso tadawomin dashi gida tunda dei gashi Y'ar cikinsuma basu ba'ta tarbiyan ba.

Miemah tanajin duk wannan munanan maganganun datake akan iyayenta amma batace mata uffan ba, haka tawuce d'aki kai tseye tafara chusa kayanta cikin akwati.
*****
Tunanin da Mommy take tun wayewar gari itace hanyarda zatabi tafad'awa Maisha dawowar Miemah gidansu, ba'tason abunda zai 6ata mata rai dedei da kwayar zarra, Haka tacigaba da lissafai iri iri aranta. Bayan Miemah ta kammala shirya akwatinta, tai wanka tachanza kaya, Ji'kakkun kayan data cire haka ta chuso cikin akwati tasau'kar kasa, Momy tana zaune a falo tashigo tana Jan 'jakarta tace' Se anjuma. Ta6e baki momy tai tana zuba mata ido "Ina kika kinkimo akwati kike zuwa haka?

Gida" Miemah ta amsa mata kai tseye. 'Bakida da labarin Sa'tar da mahaifinki yai neh? Momy tabita da wannan tambayar.
Miemah ta'san da maganar sabida tana yawo agari kowa yasan dacewa d'an uwan Alhaji Sambo ya saci kud'i kuma an 'kaisa 'kara kotu sedei tarasa gane dalilinda yasa Aunty Safeenah take mata irin tambayar, kodei so take ta'kara chusa wata bakin cikin aranta bayan abin kuny'anda Mahaifinta yai.

Tagwaye (Identical twins) Where stories live. Discover now