PART 6

3.4K 174 29
                                    

  ____This chapter is dedicated to
          Fatima_Umar; Thank you so
           Much😍😍😍
          For taking your precious time
          Voting and commenting💖💖__

      ******************************

______TAGWAYE BY BASMA BASHIR

Daga nan babu inda Ma'inah ta tseya se gida, inda tayi parking motarta tashige, zuciyarta na bugawa tana zura idanuwa tamkar wacce aka sako daga gidan ya'ri.  Kana ganinta ka san akwai tsoro atattare da ita kuma ko kad'an hankalinta ba'a kwance take ba.

Ahaka ta 'karaso falo tana tafiya jugum... Jugumm tana tinani 'kala 'kala a zuciyarta 'Inna lillahi wa Inna ileihi rajiun' shine taketa nanatawa tana ko'karin kauda tinanin Zaid dayake shirin addaban rayuwarta.

"Sannu da Dawowa Ma'isha ga abincinki nan mun kammala, na shirya Miki a dinning"  Mariya tafad'a. yayinda a firgice Ma'inah ta kad'a kai tanacewa 'Banajin y'unwa ki tattara abincin ki mayar dasu kitchen;  Tana fad'an wannan tahauro sama, inda tashige d'akinta a gajiye ta fa d'a kan gado, tana rintse idanuwa babu wanda tafara gani se Zaid 'Auzu billahi Mina Sharrin Shaidhanin Rajim'.   Daga nan tamike a tsorace d'aura alwala tafito tanata nafiloli wanda ita kanta batasan adadinsu ba tana rokon Allah.

            **************
'Karfe shida ta_yammaci Momy tadawo daga wajen aiki. Tashigo tana waya da Ma'isha ; A'uzubillahi baby kice dei yaukam bakisamu interview'n ba...

'Momcy ke dei bari. Mutanen chan ba suda mutunci wallahi saura kad'an muta da fad'a dawani soja awajen, kinajima Momcy wai Kashim ya tseyarwa wani Confanin anya zan samu aikin kuwa?'

Zaki samu Isha'ta kin manta nasiharda Momcy take miki ako yaushe 'Do not loose hope', Kuma don Allah Isha kidena wannan halin naki na fad'ace fad'ace kinsan wasu mutane ba mutunci ne dasuba, zasu iya su dake ki Kuma ko ajikinsu....

Ta karasa kalmar ne akan gadon ta inda takecewa; Isha kiringa bin duniyan nan a sannu kinji.

'Kuttt! Ma'isha tafashe da dariya momcy kema kinsan d'iyar ta 'ki ne ba ta d'aukan 'Shit, I love you momcy bye bye. 
Anan ta katse wayarta, Inda Momy tashige bathroom tayi wanka tareda d'aura alwala, Tana fita tayi sallah raka'a Uku  Mangriba, tareda Nafiloli. Bata ta'shi kan sallayar datake ba, tad'auki addu'oin "Askar" tana 'karantawa. Alokacin Daddy yayi sallama yashigo "Safeenah yau na ga Ma'inah ta sauya ko meke damunta?

"Ma'inah kuma? meya tsameta?" Ta ajiye littafin dake hannunta tana tambayarsa cikin rud'ani.

Mikewa Daddy yayi yana girgiza kansa alaman abunda yake tunani ya tabbata 'Wato ke Safeenah kwata kwata na fahimta baki damu da Ma'inah ba, Ki tuna y'arkice ya kamata kifini sanin halinda take ciki Amma ko ajikinki....

Dasauri momy takatse shi 'Dakata Abban Ma'isha taya zaka zargeni da laifinda nasan ban aikata ba, kafi kowa sanin irin son danake yiwa Ma'isha da Ma'inah su kad'ei na mallaka taya zan kaurace musu kuma taya zanki ba'su kulawata bayan sukansu ni kad'ei ce Uwar dasuke alfahari da ita...

"Idan Ina Miki maganan Ma'inah ba nason kikawo min sunan wata Ma'isha saboda naga kin d'au dukkan soyyayar kin d'aura akanta bayan dukkansu Y'ay'anki ne kuma alhakkine akanki, dole ki kula dasu dukkansu biyu......"

Hawaye momy tafara zubarwa "Amma dei Kai kanka ka san dalilin dayasa nake bin Isha a sannu kuma ba'nason ganin 6acin ranta saboda irin rayuwar data taso aciki ka 'fi kowa shugwa6ata kuma wannan Chanjin rayuwar datayi hanyace ta 6acewarta, inba ahankalin muka bitaba wallahi da tuni ta 'kauracewa hany'an kwarei Kuma Isha gyaran Likitoci ne ba cikekken lafiya gareta ba. Ma'inah kuwa Allah yasani Ina santa har cikin zuciyata kuma Ina bata Kulawa dedei 'karfinda Allah yabani.

Tagwaye (Identical twins) Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon