PART 8

3K 133 2
                                    


_____TAGWAYE BY BASMA_BASHIR

'Karfe bakwai da rabi ta_dare Ma'isha tafito gidan Zaid tareda securities d'insa, Inda suka rufe dukkan kofofin gidan Ka'na sikayi mata gargad'i cewa kada tasa'ke zuwa wajen kuma koda wa'sa basason su'kara ganinta a hany'an gidan bare har tayi tunanin shigowa ciki, Sabida oga yayi musu federal warning akanta.

Uffan... bata tan'kamusu ba, haka tacigaba da tafiya a gefen titi tana watsa cingam tam'kar Y'ar arna, daga shigarta har izuwa k'anta, babu dankwali, gashinta ne ke zu6e Baki wuluk har izuwa tsakiyar ba'ya.

💥💥💥💥💥💥💥💥
Ma'inah kad'ei ce a gida tinda safe take shiga da fita babu kowa, ta rasa inda momy tashige yau, ko irin dawowar datake cin abincin ra'na batayiba, gashi yenzu har karfe takwas da rabi tayi babu alamarta ko Daddy.

Wayarta dake cha'ji taciro kai tseye takai layin Momy Inda a bugu d'aya ta amsa; Ma'inah kizo gidan Ishah kisatmemu nida Daddinki muna chan.... Daga nan takatse wayar, Muryarta ta nuna cikin damuwa take sosai yayinda take magana. Hakan yasa Ma'inah bata 6ata lokaciba, Dasauri tashirya, Inda Driver Bashar yaja'ta zuwa Ma'isha Sambo Maidugu resident.

Suna isowa tasauko, aguje ta'karaso cikin parlour, anan tahango momy a d'akin Ma'isha tana rusa kuka tamkar rasuwa akayimusu. Kai tseye Ma'inah ta'karaso inda take, jiki a sanyaye tace; Momy me yafaru kike kuka?

Janyota momy tayi, cikin tsananin damuwa ta rungume ta, tanacewa; Y'ar uwarki tayi hatsarin mota yanzu akabugowa Daddy'n ku akafad'a Masa.
Cikin Sananin kuka tarike hannayen Ma'inah dika biyu tanacewa; I really don't want to lose her, you two are the only thing I have, Ma'inah dan Allah kifad'amin cewa Ma'isha zata dawo gareni, wallahi bazan iya rayuwa batareda ita ba, she is my daughter I love soo much....

Share mata hawaye Ma'inah tayi, yayinda take kokarin ri'ke nata hawayen dasuke ko'kuwar gangarowa cikin kwayar idanuwarta; Daddy fa? A ina yake? Iya tambayarda tayi kenan.

"Ban saniba, yana amsa wayar da akayimasa yatafi batareda yafad'amin inda yake zuwaba;. Momy ta amsa cikin nunfashi d'aya. Yayinda tamike Kai tseye tasa hijabi tafice, Inda Ma'inah tabiyota a baya tana tambayarta Inda take kokarin zuwa. Uffan batafad'a ba, Motar ta tashige fuuuu.... Tafara tuki full speed tamkar barin garin zatayi.

Ma'inah ma motar nata tashige, Inda Bashar yake biyeda Motar Momy har tseda suka kai City Hospital.

Fitowa sikayi alokaci d'aya. Momy na gaba Ma'inah na bi a baya, ahaka har sika kai d'akinda Ma'isha take.
Kai tseye sika shigo Inda suka tarar da Daddy tseye akofar d'akin yana zuba addu'oi da salati.

Meye ya tsameta? Momy ta tseya Inda take tana tambayarsa cikin mutuwar jiki. Ahankali ya janyota Inda yake yayinda ya rike hannayenta dika biyu yanacewa; ki gafartamin Safeenah inaga rashin kulawar dakike fad'a cewa ba'na baiwa Ma'isha ya tabbata domin likitoci sun tabbatarmin cewa Rashin Kulawa ce da Stress yakaita gayin hatsari, Amma abun tashin hankalin kuwa shine Farfad'owar ta dasunan wani mutum wai shi ZAID tata'shi, na rasa waye wannan mutumin Zaid.

Zaid: Ma'inah tayi saurin katse shi cewa; Zaid dei wanda nasani dawuya Ma'isha tasansa domin Babban attajirine Kuma Ogan mu a office, na tabbata bashi bane, domin wanchan Zaid da alama baya kula mutane bare Mata.

****
Suna kan tattaunawan, Likita yafito inda yashedamusu cewa aiki dei yayi kyau kuma da yardan Allah babu wata matsala anjuma kad'an za'azo a sallamesu sukoma gida. Sedei akwai bu'katar abata cikekken kulawa sabida bai kamata ta ringasa damuwa a ranta ba.

Nan ne suka 'karaso ciki, Ma'inah ta tseya a dedei kofa tana lekowa, Daddy da Momy kuwa Kai tseye suka nufo gadonta, Tana doura idanunta akansu tamike dasauri tana hawaye yayinda ta rungumesu dikkansu biyu tanacewa; Momcy meyasa kuka barni nikad'ei nafito har nagamu da hatsari. Believe me or not I'm your only daughter meyasa kuke za6in Ma'inah kubarni, Daddy I don't understand. why I'm I always your second class daughter, wace laifi na aikata kuke sa'kamin da wannan hukuncin? Tafad'a cikin nunfashi d'aya.

Tagwaye (Identical twins) Where stories live. Discover now