PART 26

3K 155 61
                                    

___IDENTICAL TWINS BY BASMA_BASHIR

                  😥Long Chapter😥

                        😍ENJOY😃

                         👇👇👇👇

Asad ya gangaro da motarsa Alhaji Zabir Mansions first gate, Nan yatarar da hayaniya anata rigima, Dasauri yafito, sai ko yaga Mommy da Maisha ce suke rigima tareda Y'an Sandansu.  "Lafiya sergent meke faruwa anan?.  
Wannan mutumin da ya'kira sergent ne ya nufo inda yake ransa a 6ace sosai yace' barka da dawowa Sir, Ma'isha ce tazo tareda mahaifiyarta, muka hanata shigowa bisa umarninda aka bamu daga sama, Oga yace kada abarta tashigo, Shine fa yanzu mahaifiyarta ta'kira oga awaya tafad'a masa. Duk dacewa mun bata dama ita kad'ei tashige banda Y'arta, Ta 'kira oga tafad'a masa wai zamu kashesu karyan banza tin tuni sai rigima suketayi anan suna hayaniya.

Shiru Asad ya tseya yana sauraransa har tseida yagama magana, yajuye 6angaren Mummy yana murmushi "Hajiya kiyi hakuri fa mutanen ne haka suke wallahi, kuma da gaske ne Zaid ya hanasu barin Maisha tashigo gidan, toh amma ai tunda dei tare kuka taho babu wata matsala zaku iya parking motocinku anan sannan kushige motata insaukeku acikin gida..... Bai 'karasa furucinsaba, Mommy ta katseshi' Saboda me zamu bar motocinmu anan wajen, Kai ma ashe d'an rainin hankalin ne, wato so kake kanuna mana ka'fimu kusanci da gidan ko toh wallahi karyarka tasha karya.  Da wannan maganar ta janyo Maisha kai tseye tabud'e kofar mota suka shige gaba d'aya.  Ganin Asad yana tseye awajen masu gadi basu musaba nan ta'ke suka danna remote aka bud'e musu kofa.

Shima Asad biyosu yai abaya da motarsa, shiyasa ma suka samu suka 'karaso cikin gidan babu wanda yatseidasu. Suna isowa garrage sikayi parking. Mommy ta'yi mamakin ganin Ma'isha da akwatuna birjik tamkar barin gidan nasu tai, Matsowa tai har kusada ita tanacewa" Isha lafiya meyesa kika kwaso wannan akwatunan? ni atunanina fa zuwa kikayi domin kiziyarci Y'ar Uwarki ki sabida ku deideita tsakanin ku.

"Momcy nifa dawowa nai, Ta amsa kai tseye. 'Dawowa kuma Maisha angayamiki nan d'in gidan bariki ne Wanda kowa zai dawo idan yaga dama, toh maza ki maida akwatunan nan naki cikin mota mushigo mugaishesu sannan mukoma gida cikin Kwanciyar hankali.  
Zumburo baki tai "Nifa Momcy gaskiya bazan komaba haka kawai duba irin tsarin gidan nan fa dan Allah ki 'kara dubawa ai duk wanda yasamu yana rayuwa awannan irin gidan shikam sedei yaroki samun lahira sabida duniya dei kam yasamu kina gani Masha Allah...

Ta6e baki momy tai tana binta da kallo har saida tai shiru' Maisha nace ki maida wannan akwatunan naki cikin mota kada mutanen gida sufito su tsamemu anan. Tafad'a atsawace.  "Toh Mumcy daman ai dalilin da yasa Daddy yadawo da Ma'inah nan shine kada muhad'u a gida d'aya Kinga kenan kawai sai ku kuma gida tareda ita nidei gaskiya nan dei kam naga wajen zama.  Da wannan maganar taja akwatunanata inda kai tseye tafara tambayan securities 6angaren Zaid.

Bakin ciki da 6acin rai ce sosai tacika Momy ayanzu, Ta'san halin d'iyar tata kuma Babu yedda zatayi tachanza mata ra'ayi dazaran tayi deciding abu. Haka tabarota awajen tai cikin gida, falon Aunty Rahila ta'karaso kai tseye tana shiga sukayi Kacibis da Miemah ayayinda take gudu Anisa na biye da ita abaya tanason takar6i wayar Miemah taduba wani abu. Tseyawa sukayi dikkanin su alokaci d'aya. 

"Inna lillahi wa Inna ileihi rajiun Miemah? Momy ta 'kara bud'e idanuwarta sosai tareda Salati "Iyeee Many'an mata su Miemah anga arziki koh, ina ke ina zama a irin wa'innan kantamemiyar gidan, lallai ansamu waje harma anfara gina 'ka6a, wato dei an Kwan biyu ba'aci Koko da tuwon dawa ba.

Hajiya Safeenah maraba, yaushe kika shigo gidan na'mu? Aunty Rahila tafito daga d'akinta adeden lokacin, 'Toh ya kika tseya achan baya kishigo ciki man. 
Mommy ta'kasa kauda idaniyarta daga kan Miemah se mamaki taketa yi "Iyee Hajjaji sannu fa daman ance matsiyata sunfi ganin darajar arziki kinga yedda kikayi 6ol6ol.

Tagwaye (Identical twins) Where stories live. Discover now