PART 3

3.7K 242 18
                                    


   ____TAGWAYE BY BASMA_BASHIR

       FLASHBACK_CONTINUES
                💖💖💖💖💖

Alhaji Sambo da Safeenah kwana sukayi ido hudu babu wanda yayi gengedi cikin su bare barci. Tunanin hanyarda zasubi su 6ullowa Ma'isha maganar komawa 'kasa Nigeria suke, dakuma hanyarda zasubi su sufad'amata batun Y'ar uwarta Ma'inah. A Daren suka kammala duk shawarwarinsu.

****
Da sassafe bayan sallar asuba Momy da Daddy duk suka koma d'akin d'iyarsu Ma'isha suka kwanta tare da ita, tamkar barci suke har zuwa lokacinda ta saba tashi (Karfe goma) ta_safiya.

*****
A hankali tataso domin kada tatashesu, Cikin sananin Farin ciki ta rungumosu sannan tayiwa kowa kiss "I love you sooo much 😍parents, and thank God you all love me back" Da wannan managar tamike cikin Farin ciki tawuce bathroom anan tayi brush, tawasa ruwa ajikinta sannan tafito.  Aiko tana fita taga babu kowa a d'akin se Nanny (Saratu) wacce take kula da ita tun tana 'kan'kanuwa.

'Na bar Momcy da Dad anan kan gadona suna barci, a ina suka je? Ma'isha tafad'a cikin rud'ani 'Ke Saratu kurmace ke? ba tambayarki nakeyiba?'

Murmusawa Saratu tayi 'Kwantar da hankalinki Y'ata, Momy da Daddy suna nan Parlour suna jiranki.....

Ma'isha ce tayi saurin katseta 'What? wa kike 'kira Y'arki, God Forbid, Over my Dead body, Ni ba Y'ar kowa bace fa ce Y'ar ga 'tan Gidan Sambo Maidugu, I mean Y'ar Safeenah da Sambo got it? Kuma babu wanda yabaki damar 'kiran Momy na da Daddy na dawannan sunan dakikayi kuskuren 'kiransu ayanzu domin ni ce kad'ei nakeda damar wannan. Dirty Woman, yi maza kiciromin kayanda zan saka..

Duk wannan maganganun da tayi Saratu bata tankamata ba, Jan bakinta tayi, tayi shiru kamar wacce ba ta wajen domin ta 'fi kowa sabuwa da halin Ma'isha, kuskure kad'an zasuyi tafad'awa mahaifinta ya sallamesu. 'Spoil Brat' Tafad'a ahankali yayinda take bud'e wardrobe d'in Ma'isha..

Doguwar bakar Riga ta sany'a Wanda sukayi dedei da farar fatar jikinta, inda Kai tseye ta gudo Parlour tana neman Momy da Daddy

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

Doguwar bakar Riga ta sany'a Wanda sukayi dedei da farar fatar jikinta, inda Kai tseye ta gudo Parlour tana neman Momy da Daddy. 
A tsakar falon tayi Kacibus da akwatunan kayyakinsu wanda already anrigada anyi packing komai, da dukkan alamu dei ita kadei ake jira.

Washe baki tayi tanacewa "Momcy Ina kuma zamu? Kodei Allah ya amsa addu'a tace?

Daddy dake fitowa daga cikin d'akinsane ya sany'a bakinsa cikin maganar tasu inda yake tambayarta addu'ar me kikeyi? 
Juyowa tayi tana cewa; Haba Dad ai Kai kanka yakamata ka ga'ne cewa na gaji da zama guri d'aya, ko mantawa kayine tunda nata'so ban ta6a barin 'kasar nan ba, shiyasa ako yaushe nakanyi addu'a kan Allah yakai 'sahon rai insamu inga bala'gata kaga awannan lokacin babu wanda ya Isa yahanani yin abunda naga dama a Duk fad'in duniya because narigada na samo Freedom....

Ya Isa haka Maisha: Mommy takatse ta '"Maza kutaso mutafi, kuma kisani wurinda muke zuwa ayanzu ba lallai bane kisake dawowa nan Sabida bakida tarbiyyarmu ta hausa, 'Dabi'un ki duk kin kwaso sune anan d'abi'un arna Baturai, wa'enda ko kad'an babu imani a zukatansu. 
Da wannan magana tamike ranta a6ace tarike hannun d'iyarta suka wuce.  Ma'isha 'kasa magana tayi domin tunda take bata ta6a ganin 6acin ran Momy ba se yau.

    
NIGERIA***********************

Ta 6angaren Ma'inah kuwa babu wani wanda yafad'amata dawowar Iyayenta Nigeria, asalima tun jiya take ganin Umman ta cikin damuwa kuma kamar akwai abunda take 6oye musu ita da Miemah sunyi kokarin tambaya but she is not interested. Abba kuwa baya zama a Maiduguri bare yasan halindasuke ciki a gari, ko yaushe Yana Kano yana kokari da sana'oinsa.
***
Had'a baki sukayi akan su ringa sany'a mata ido ko zasu ga ne damuwar dake damunta wanda ko kad'an ba tason susani. 
'Karfe hudu ta_yammaci Umman tasu tafice cikin damuwa taja motarta tatafi. Ma'inah da Miemah kuwa bin motar nata sukayi da adedeita sahu inda ta tseya ba'kin wani babban ofishin Lawyoyi tashige Kai tseye.  Ma'inah da Miemah suka sallami Mai adedeita sannan sakabi sahunta, a ba 'kin kofa suka la6e suna sauraronsu.
Muryan wani dattijo ne yafara magana "Mrs Saminu muna sane da zuwanki nan domin kinbi duk ofishin Lawyoyi kina basu 'karanda ke kanki idon ke lawyer ce dawuya kisaure irinsa. Sambo yanada arziki kuma ki yarda ko kar kiyarda yarigada yabiyamu kud'i masu yawa Daman yasan irin haka zata iya faruwa.

Muryar Umma sukaji tana kuka "Lawyer kataimaka, Wallahi Ma'ina tarigada tazama Y'ata domin Ni ce nashayar da ita Kuma shi kansa Sambo yace yabani itane har abada, believe me daga baya ne yachanza magana dasukaga Y'arsu dake chan batada tarbiya Kuma tafara kauce hanyar musulunci. Kuma Ma'inah tarigada ta saba da y'ata Miemah bazasu iya rayuwa babu.....

Umma bazan koma wajen Momy ba; Ma'inah tashige ofishin tana hawaye masu zafi. Miemah dake la6e a ba'kin kofarma shigowa tayi tana kuka "Umma baza'a rabamu ba koh, Dan Allah Umma kifad'amusu cewa Teddy na ba'tason rabuwa damu Sabida ita y'arkice Kuma 'Kanwata ko Umma.

Bata 'karasa furucinta ba, Ma'inah ta rungumota "Teddy wallahi babu inda zanje ina nan taredaku da Umma dakuma Abba....

"Ku dakata; Wani dattijo yamike yanacewa; Mrs Saminu yakamata ki kwaso Y'ay'anki kutafi gida Sabida nan ofishine ba wajen shirya Fina finai ba.

Jikin Umma a sanyaye tamike, tashare hawayenta sannan ta rike yayanta suka fita ofishin suna kuka kaman wa'enda aka kaiwa sa'kon mutuwa. 
"Karfe biyar zamuzo gida mudauki Ma'inah musata a jirgi takoma Abuja Gidan mahaifinta" wani saurayi yabiyosu da maganar sannan yakoma cikin office.

ABUJA NIGERIA******************

Daddy is this my house? Wow thank you Dad I love you sooooo much: Ma'isha tafad'a cikin mamaki; Mommy you don't have to worry, I will be happy here as far as our family is complete karku damu na yarda muzauna a Nigeria nidei matsalata kawai bansan ganinku cikin damuwa...

Duk wannan maganganun datake, Mummy Bata Tankamataba, Sabida hawayendake kokarin zubomata Wanda ko kad'an ba'tason su su6uce.

Princess we have a surprise for you "Daddy yayi ajiyar zuciya yafad'a. Shima yana komarin rike hawayensa. 

What surprise? Daddy meyasa kake kuka? Mumcy meyasa daddy yake kuka: Ma'isha ta tambaya cikin rud'ani, awannan lokacin itama hawayen suna kokarin tsirarowa a idanuwarta domin tunda take bata ta6a ganin Iyayenta cikin damuwa irin hakaba.

Safeenah ce tayi saurin katseta "Ma'isha ki gafartamana"
Ta 'kasa rike hawayenta awannan karon. Rungume y'arta tayi tana cewa: Alhaji maybe this is not the right time, yakamata ka shiryamana Viza gobe mukoma America.

Inaa, Shine kad'ei abunda Sambo yafad'a Sannan yafice.

****
Bai dad'e dafitowa ba, yadawo tareda Ma'inah:  yayi ajiyar zuciya yanacewa
"Ma'isha Surprise, this is your twin sister, mun 6oyemiki wannan maganar ne sabida yanayin lafiyarki, kinsan ba muson ganin 6acin ranki. We love you so much Ma'isha shiyasa bamu fad'amikiba tun a farko ba...

            💗💗💗💗💗💗💗💗💗
Ma'isha ta yi matukar kad'uwa dajin wannan sirrin  dasuka dade suna 6oyemata. A ranar babu irin halinda batanuna musuba.
Nunamusu tayi zata iya kashe kanta dazaran sun had'ata gida tareda Ma'inah saboda duk duniya babu wacce tafi tsana irinta. Hakan yasa Sambo ya tse mata gida takoma chan tareda masu kula da ita, Ma'inah koh tazuna tareda Iyayenta, duk dacewa ba 'tasan hakan tilastawa kanta tayi Sabida kada ta6atawa Iyayenta rai...

  ********FLASHBACK ENDS*******

TAKAITACCEN LABARIN MA'INAH DA MA'ISHA KENAN, KUBIYONI CIKIN LABARIN KUJI YEDDA ZATA KASANCE.

DO NOT GIVE UP, KEEP ON FOLLOWING LABARIN TANADA ABUBUWAN TAUSAYI, MAMAKI DAKUMA AL'AJABI AKWAI KUMA BABBAN DARASI WANDA ZAKU FAHIMTA IDON LABARIN TAYI NISA.

KUBIYOMU A TAGWAYE PART 4 INDA ZAMU FARA LABARIN TUN A FARKO. MA'ANA CIGABAN PART 1 KENAN.... THANK YOU

YOUR VOTES AND COMMENTS MATTERS ALOTS....

HAVE A NICE DAY

Tagwaye (Identical twins) Where stories live. Discover now