PART 25

2.2K 118 22
                                    

Another one🤭🤭🤭👇👇👇❤️❤️❤️

  
_____IDENTICAL TWINS BY BASMA_BASHIR

                         ENJOY 👇👇👇

Tsit! Zaid yazauna Yana bin Mainah da kallo har Sanda ta gama bayyana mata ko Wacece Miemah, dashike musamman yau ya'kirata har zuwa falonsa kuma babu kowa anan daga shi sai ita sai kuma securities d'insa, Ma'inah ta sake jiki dashi ayau sosai sabida Babu abunda tarage masa a labarinsu kap! Ta kwaso d'aya bayan d'aya ta tsanar masa. Zaid ya matukar tausaya masu sosai wannan labarin nata yasa soyayyar Ma'inah ta'kara shiga zuciyarsa sosai. Itama Ma'inah ayau ji tai babu wani mahalukinda zata iya soyayya dashi a duniya bayan Zaid tunda tazauna idanuwansa take gani tareda mamaki sabida bata ta6a ganin kyawawan idanu ko a mafarki makamancin idanun Zaid ba, Ga'shin jikinta har tashi suke ayayinda tad'an sauke idanuwarta zuwa d'an 'karamin le66an bakinsa shima dei 'kasa kau da idanuwarta akansu tai, tana 'kara mamakin kyau'n sa.

Gyara muryarsa yake tun tuni, Sabida ya lura Ma'inah ta dad'e tana kallonsa, ya 'kara gyara murya Amma har yanzu bata kauda idanunta daga kansaba, Murmusawa yai shima yakure mata Ido. 
Tana ganin wannan murmushin nasa wanda suka dad'a bayyana dimples din fiskarsa, batama san lokacinda murmushin ta bayyana a fiskarta ba itama "Masha Allah" tafad'a yayinda ta'kara kurewa dimples d'in nasa ido. 
"Miss Ma'inah how do I look? Zaid yafad'a kai tseye.
Cute, Mainah ta amsa masa babu tsoro ko fargaba.  Mikewa yai kai tseye yazauna kusa da ita, inda ya d'aura hannunsa kan kafad'arta, nan Mainah ta sheki wata irin kanshinda tunda take rayuwa a duniya bata ta6ajin irintaba. Yana wannan murmushin nasa yace" Thank you so much Mainah. Ya'kara kuremata ido sosai yayinda yad'aura hannayensa kan tattausar fiskarta Wanda take sheki da haske tamkar auduga ya kashe muryarsa kamar kullun cikin nitsuwa yace: Mainah you are the most beautiful creature in the whole universe. Sanda yaja wata doguwar nunfashi sannan ya'kara cewa" Zaid Muhammad Zabir is the most luckiest man alive, na gode Ma'inah ke ce tsanadiyar farin ciki na I love you so much.

Bai karasa kalamansa ba Mainah ta rungu'meshi tana farin ciki sosai ji tai tamkar a mafarki, shima Kai tseye ya d'oura hannayensa abayanta yanakuma rad'amata a kunne "Yea Ni ne Zaid Muhammad Zabir ba Mafarki kikeyi ba Mainah Sambo Maidugu.   Itama akunnensa tace'" Masinjarka Koh? Shiru yai nad'an wasu mintuna sannan yayi dariya akunnuwarta ya rad'a "Kinsan meyasa nad'auraki a masayin masinjata sabida inaso akoda yaushe mukasance muna tare dani dake no third partner.

Murmusawa tai inda ta'kara sauke 'kanta kan shoulders dinsa tana feeling over protective.

    ***************************

"Kai d'an talakawa, banza shashasha wallahi na'fika iskanci zaka bud'emin kofa ko kuwa?"   Ta6e baki securitin gidan Zaid yai ya'kara dubata sosai "Hajiya kince sunanki Ma'isha.  Bai karasa kalmarsaba ta katseshi; kwarai kuwa da gaske sunana Maisha Sambo Maidugu, kada kuma kasa'ke kirata da Mainah sabida babu abinda yahad'a mu da ita ka fihimta sosai, idan ma jahilcin ce tai maka yawa you can repeat after me "Ma'isha Sambo Maidugu. 

Dakata Hajiya gaskiya indei Maisha ce ke da gaske, toh Oganmu Alh Zaid yace kada abarki kishigo, we are sorry madam kawai kikoma inda kika fito. 

Fitowa Ma'isha tai daga motarta, cikeda masifa tarike rigar wannan security babu tsoro a fiskarta tace' wallahi Malam ka kiyayeni ni nan dakike gani Matar Ogan naku ne dakansa wallahi idan kana kokarin rainamin hankali. 

Matarsa kuma? Yayi aure neh?
Ba'a saniba "Maisha takatse shi; so kake kasamu damar magana dani ko, toh wallahi nafi karfin ka kaje chan gidajen getto kanemi matsiyaciya irinka kui magana, kawai Malam idan zaka bud'emin kofa kabud'e Dan rainin hankali kawai. 

Haka Maisha da wannan securitin suka fara hayaniya har Sanda mutumin yakusan dukanta tana turinsa shima haka yake turinta sunata masifa. Nan da nan Sauran securities na ciki duk suka fiffito, Sanda suka nuna mata bindiga sannan ta gane hankalinta inda yake.  Ogansu ne yafito "What the heck is happening here?

Tagwaye (Identical twins) Where stories live. Discover now