PART 34

2.2K 154 20
                                    

     Thank you so much FANS, 4 voting and commenting in the previous chappy, I really appreciate😍😍😍.  Allah yabarmu tare❤️

        TAGWAYE👨‍❤️‍💋‍👨 BY BASMA_BASHIR

                           👇 ENJOY 👇

Miemah ki gafartamana wallahi da na'san cewa kece ainihin Y'ar Uwata da tun tuni na ta'kurawa Daddy ya dawomana dake gida, sabida tunda nake rayuwa a duniya ban ta6a sanin yedda soyayyar Y'ar uwa ta jini takeba sai yau, Babu irin wulakanci da cin amanarda ban fiskanta gun Maisha ba, Kuma na tabbatar miki cewa momy 'kanta idan ta'san da wannan sirrin tuni ta janyoki a jiki. 

Miemah tana share hawayen dake kokarin sirnanowa daga idanunta yayinda tasa murmushin karfin hali tanacewa"Babu komai haka Allah ya kaddara, ni kaina ako yaushe nakanji ajikina tamkar akwai alaka Mai karfi dake tsakanina dake, Ma'inah wallahi tun da muka taso tare duk duniya babu wacce nafi ji da ita irinki Kuma idan muna tare jinake tamkar nafi kowa sa'a a duniya....

I feel thesame way sister,. Ma'inah ta katseta" Wataran har kuka nike, ina ma ace kece Y'ar Uwata ba Maisha ba.

Allah Sarki, Cewar Miemah inda ta rike hannayen Y'ar Uwar nata duka biyu tanacewa' Maisha ta ta'kurawa rayuwarmu Kuma bamuda mikiyin dayawuce Maisha a duk fad'in duniyar nan Sabida haka daga yau, ni da ke zamu fara d'aukan fansa, dazaran muna tare Maisha bazata 'kara ta'kurawa zuri'ar mu ba promise.

Dasauri Ma'inah tasa d'ayan hannunta a saman ta Miemah " Yes Promise, Daga yau zamu rayu cikin farin ciki da annashuwa babu wanda zai kara d'aga mana hankali, zamu farantawa iyayenmu sannan muyi rayuwa kamar yedda kowace zuria suke rayuwa cikin kwanciyar hankali, Dubun Maisha ta cika bazata Kara addabanmu ba dazaran muna tare. 
  Haka suka rungume juna suna dad'a farin ciki da annashuwa.

        *************************
Zaune take gaban television a Babbar falon kasa inda take bin wata shirin wasan kwaikwayo mai suna Kwana_casa'in wacce ake nunawa a tashar Arewa24.  Sallamar mijinta ta amsa a tsorace ta mike "Saminu lafiya? saurin meye kakeyi haka Ina Kuma zaka?.

"Inji dei wa'innan munafukan basu dawoba, ke kad'ei ce agidan. Cikin sananin rud'ani Aisha ta gyad'a kai "Ehh ni kad'ei ce, Saminu su waye kuma munafukai? Bai amsa mataba janyota yai kai tseye suka fito waje, Maisha na ganinsu ta fice daga motarta tanacewa' Saminu don Allah kataho mutafi mutanen nan zasu dawo su tsameni anan.  "Sorry my dear bani minti biyu' Cewar Saminu inda yajuya 6angaren Aisha yanacewa" meye kika tsaya yi anan bazakije ki baiwa yarki hakuri ba, Ni dei ta yafemun saura ke.....

"Dakata Saminu daman sabida wannan kake wani rawan jiki haka, to kasani niba shashasha bace irinka, nina haifeta ko ita ta haifan, anki abada hakurin yi abunda zaka iya.   Bata kaiga karshen furucintaba Saminu yarufeta da mari a fiska "Shashasha kawai banza, ahaka zaki kare ma'kira, algunguma.   Kuka Aisha tasaka "Saminu wallahi Allah zai sa'kamin, kaje Kucigaba da aikata halinku da kai da d'iyar ka kuma kusani Allah yafi'ku wataran sai kunyi da'nasani da yardan uban giji.

Fashewa da Dariya Maisha tai achan baya, tanacewa' Saminu wai meye take fad'i ne don Allah shareta mutafi 6atamana lokaci zatayi da banzan maganganu.   Hushi Saminu yake tamkar kare yayinda yajuye rai a6ace yanacewa" Kuma daga yau kin rabu da zuri'ar ki har abada, kisani dani da Maisha bazamu 'kara dawowa nan gidan ba na sakeki saki uku, d'aya, biyu, Uku  igiyar aurena dake ta'kare anan wajen.

"Ta'fi nono fari, tafi man Saminu sai me, kafi jirgi tashi kuma kafi ruwa gudu kada ka kara dawowa so what? Bai tan'ka mataba, juyowa yai kamar yedda tafad'a yai tafiyarsa, ko ajikinsa dashi da Y'arsa suka shige mota Fuuu!!!!  Suka tashi tamkar barin gari zasuyi.  Anan wajen Aisha tafa d'o sai kuka take tana istigifari "Ya Allah wace laifi na aikata a duniya, Inna lillahi wa Inna ileihi rajiun' Allah mun tuba, Ya Allah duk inda Saminu yakai y'an nan ta'wa ya Allah ka baiyanota ga hukuma ta fiskanci hukuncin wannan gagarumar laifinda ta aikata maka, Ya Allah ka gafartawa wannan bawan Allah "Asad" Allah kasa mutuwan shi yafi alkhairi agareshi.

Tagwaye (Identical twins) Where stories live. Discover now