PART 27

2K 137 14
                                    

Sorry for d late update, Assalamu Aleikum 🙋 Thank u so much for voting and commenting in the previous chapter❤️BRAVO❤️.

THIS CHAPTER IS DEDICATED TO ALL TAGWAYE FANS😍 LOTS OF LOVE.

❤️ENJOY ❤️

Maisha Tasha wedding gown mai matsifar kyau, wacce da'ka ganta, kallo d'aya za'kasan naira na aiki awajen. Ta'sha kwalliya pes! Gwanin sha'awa, Aka kashe millioyin dukiya akayimata gyaran jiki, gasu kunshi, gyeran gashi abar azo agani.

Farin cikin datake ayau ba'a misaltuwa, hakoranta awaje suke sharr! tunda safe taketa zumud'i ta matsu a d'aura auren sabida hankalinta ta'kara kwanciya, atunaninta wannan plan na auren Zaid data d'auka itace best plan a rayuwarta. Kai Harma ta tsanarwa abokananta aka fara kiranta ana tayata murna.

A zaune take cikin wata kantamemiyar d'aki a 6angaren ZMZ Suites, tasa computer agaba tanabin video'n CCTV camera wanda ke nuno mata duk abubuwanda suke faruwa wajen d'aurin aure. Tsit ta zauna tana kallo, Maisha yau harda charbi a hannu tana ja tanakuma Addu'a aranta "Allah sa agama d'aurin auren nan lafiya, sabida dazaran an d'aura, shi Zaid ba matsalarta bane sabida na mijine, minti guda zata janyo zuciyarsa ba'ki d'aya takoma 'kanta, Adduarta kawai a d'aura auren cikin kwanciyar hankali, kada ma yasani har sai ba'yan ankammala komai.
****
Tana bin video'n dai. Harma an shirya wajen sosai, kujeru aka jejjero ko ta ina dasu dardumai, dadei sauransu, many'an mutane sunata pasowa cikin gidan da motocinsu, wasu ma harda escourt polisawa suna biye dasu abaya tsabar masayi. Maisha sai 'kara walwala take, ayau jinta take asama, farin ciki tamkar zai kasheta, sabida tunda take rayuwa a duniya bata ta6ayin farin ciki irin hakaba. Ayau dei burinta ya cika ta'samo miji na gari wanda kuma ta tabbata zai d'are mijinda Mainah zata kwaso sau d'ari. Daman ance haka Tagwaye suke, d'aya kanfi d'aya nasara da sa'mu. Ayau dei Allah yarigada yanunawa Duniya cewa ta'fi Ma'inah Daraja da matsayi a idanun jama'a, tinda da kaddarar Uban giji yau zata chanza daga Maisha takoma Mrs Zaid ko Gimbiyar ZMZ.

Cikin wannan tunanin na farin ciki ta kwanta kan gadon tsit! tana kallo dei abar sha'awa. har barci 6arawo ya tsaceta daganan video'n nata taringa tafiya ita kad'ei.

*****************
Zaid Yana barin Sha'shin Mahaifinsa, 6angaren Mamy yanufa, kai tseye yaja motarsa fuuuuu!!! tamkar barin garin zaiyi gaba d'aya, Yana shiga Hajiya Rahila Mansion yai parking adedei kofan parlour yafitce aguje, y'an Sandan wajen duk sun tsorata Sabida basu ta6a ganin Zaid cikin wannan irin 6acin Rai hakaba.

Da 'karfi yake kwalawa Mamy kira tun awaje harma ya'karaso cikin falo, Ya tabbata dei Mamy itama batasan da wannan d'aurin auren ba, duk wannan abubuwnda suke faruwa Kuma plan d'in Maisha ce babu tantama and she must pay.

"Allah 'karama yawan rai ango kasha kanshi, Hajiya Rahila sun fita tun tuni sadei idan zaka kirata ta waya, Ango..... Bai karasa kalmarda yake kokarin furtawa ba, Zaid ya d'aga masa hannu ✋ Excuse me, I don't have your time. Abunda yafad'a kenan yai tafiyarsa, mutumin tseyawa yai shiru yana mamaki, sabida tun ranarda Zaid yabayyana Mainah amasayin budurwarsa ba'a sa'ke ganin 6acin ransa ba, to yaukuma da'ake d'aura aurensu meye ya6ata masa rai haka? Ta6e baki yai yana binsa da kallo har ya6ace masa.

Zaid na fita yanufo motarsa, zuciyarsa na bala'in konawa ya ja Motar Kai tseye yafara tuki wanda sai Allah yasan inda yanufa, azuciyarsa yake nanata "Mainah I'm so sorry trust me I love you so much, and I will never compire my feelings for you to anyone else, not even your twins Sister infact Maisha she is the worsed person I've ever known.

****************************
"Yara ku more rayuwarku, ku sha'kata iya San ranku Allah ne yabaku arziki y'an Ga'ta.
Aunty Nasibah kenan, tana kwance kan wata tattausar kujera anamata massage, yayinda idanuwarta suke kan su Anisa wa'inda tun tuni suketa wa'sa cikin ruwa suna swimming. Ita Miemah bata iya ba, dashike tunda ta'taso bata ta6a shiga ruwa ba, Aneesa ce take fama tun tuni tana koyamata. Mainah koh bata dad'e sosai cikin ruwanba ta fito, dayake yau wani iri takeji aranta tamkar Zaid yana cikin damuwa gashiko basuyi wayaba ko sau d'aya bare suga juna.

Tagwaye (Identical twins) जहाँ कहानियाँ रहती हैं। अभी खोजें