PART 7

3K 155 18
                                    

  _____TAGWAYE BY BASMA BASHIR

A hankali take tafiya, tana tinani iri daban daban, ahaka har tahauro saman bene, inda tashigo wani ma'keken waje mai suna (CEO Villa). 

Kai tseye tawuce wajen secretary office dake dap hannun da'marta, awurin tahad'u da ta'ron jama'a kowa da takardu ahannu, daga turawa, larabawa harmada ba'kaken.
Layi sukabi, in an orderly manner aka kar6i credentials d'insu dika Sannan suka koma wuraren da aka tanada musu suka zauna, Ana 'kiran sunayensu d'aya bayan d'aya suna shiga interview a ofishin CEO, har tseda aka akai sunan mutumiyar 'Ma'inah.

***
Ma'ina Sambo Maidugu. Seketerin  yadanna kararrawa ma'ana lokacin interview'n ta yayi.
Kai tseye aka bud'e mata kofa tamike jikinta yana d'aukan zafi tashige tana ra6e ra6e. Rasa abun fad'a tayi muryanta na karkarwa tace; S.. San.. Sannu, ina wuni.

Se yanzu Zaid yajuya da kujerarsa na ta'ya inda ya d'aga ido ya kalleta 'You again? Yafad'a cikin tsananin mamaki.

Kanta na kasa ta gyad'a kai " I'm sorry Zaid kayi hakuri wallahi na'fi kowa bukatan wannan aikin I'm sorry kawai ka kaddara bamu ta6a had'uwa ba na'tabbata idan...

Excuse me.... Zaid yadakatar da ita; kin cika hayaniya and I hate talkatives saboda haka I don't think zamuyi aiki tare dake just get out.

Kuka Ma'inah tasaka, cikin sananin damuwa tasauke kan guiwowinta tana rokansa "I'm Sorry please ka taimakamin, ko wace irin aiki kabani nayarda zan kar6a hannu bibbiyu kayi hakuri ban....

"Excuse me, ya isa haka🤚 Yana fad'an wannan yad'auki littatafanta yaduba kai tseye yasa hannu inda yamikomata wata takarda yanacewa; Welcome to Zaid Muhammad Zabir Builders Company daga yau ke ce Masinja'ta bcoz I don't think you will fits in any other position bayan wannan Sabida haka nabaki za6i "TAKE IT OR LIVE IT".

Ma'sinja? Ma'inah tasa'ke tambayarsa cikin rud'ani " I'm a mater's graduate kasa'ke duba credentials d'ina da kyau kila ko baka duba mai kyau ba, please go through them again. By the way na manta banyi introducing Kai naba, sunana Ma'inah Sambo Maidugu....

I don't care; Zaid ya katseta cikin sananin 6acin rai, Inda ya watsa mata takardun nata dika a 'kasa yanacewa; Ki kwaso tarkacenki kiyi waje after the count of 5, And I mean it, kai tseye kiyi gida ba'nason insake ganinki anan cikin Company na.

One1..... 2.... 3....

Sunkuyawa tayi tana hawaye masu tsananin zafi yayinda ta kwaso littatafanta d'aya bayan d'aya tafice cikin sananin kuka da damuwa. Wajen receptionist tayi, Kai tseye tami'ka mata godiya mai zurfi Sannan tace tayi 'kokari idon CEO yafito shima taba'sa hakuri ko ta'ji sanyi aranta. Daganan tayi hany'an waje,  Inda Tashige motarta tana tuki cikin hawaye, tunani, damuwa da sananin da'nasanin kuskuren marinsa datayi jiya.

*****
Tuki take ahankali har takai gida, Gabantane ke fad'uwa yayinda take karasowa cikin gida, daker tasamu  tashige ciki, ahaka tawuce d'akinta inda anan tazube kan gado, Sanin babu kowa agida awannan lokacin yasa ta'kara zagewa tana kuka iya sanranta, tinanin hanyarda zatabi taka're kanta wajen Daddy take amma da dukkan alamu babu alaman wata mafita haka zata cigaba da 6oye sirrinta har tse lokacin bayyanarsa ta'yi.

      💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖

Ta 6angaren Ma'isha kuwa tinda safe tafita tareda momy seyayya a wata babban boutique dake kusa  da  gidanta. Momy ta tseyo mata kaya masu kyau da tsada,  sun tseyo jakan office dama sauran abubuwan bu'kata duk nazuwa aiki, daga nan ne suka dawo gida, Inda momy tashirya dawuri tatafi wajen aikinta.
Ma'isha kuwa ta sha'fa tsahon lokaci tana kwalliya agaban madubi, bayan ta kammala tsap! tashirya cikin wata d'amemmen 'bakar wando wacce turawa suke 'kira pencil trouser, da wata Farin Riga mai doguwar hannu. Da bakin Gele tayi d'auri akanta, daga nan tad'au key'n motarta tafice tana rangwad'a.

Tagwaye (Identical twins) Where stories live. Discover now