PART 23

2.1K 149 16
                                    


SORRY FOR THE LATE UPDATE, FANS INA YINKU SOSAI DA SOSAI ALLAH KUMA YABARMU TARE, FINALLY HERE IS AN UPDATE👇 ENJOY🙏🙏🙏🙏

*************************
_____THIS CHAPTER IS DEDICATED TO ZMZ, ZAID MUHAMMAD ZABIR

___IDENTICAL TWINS BY BASMA_BASHIR

Dariyan Maisha kakeji tin awaje.  Acikin d'akinta take ita kad'ei Yau ba kowa agidan na'su dashike tin asubahi momy tashirya zuwa wajen aiki ayayinda tabar Maisha agida ita kad'ei tana abunda taga dama.
Waya take da abokinta Reza_Michiel tun tuni babu abinda take sai matsifar dariya tamkar mahaukaciya.

"Reza wallahi Ina yinka sosai ba kad'an ba, momsy ta 'koro mutuniyar ai wallahi aikinku yayi Kyau sosai, Wai ni ina'ma kuka samo kayan y'an Sanda kukazo mana gida tamkar mutanen arziki...?   Shiru tai nad'an wasu mintuna sannan ta'kara fashewa dawata sabuwar dariya "Ai kuwa Momcy ta gamsu da Shirin na'mu, shiyasama ta'kori Miemah daga gidan mu, ayanzu dei bamuda wata matsala, dani da Momcy na muke gida muna zamanmu cikin kwanciyar hankali.

Ta6e baki tai "aww wannan shegiyar, Mainah ta rigada tabar gidanmu tun tuni ayanzu Momcy 'kanta tarigada ta mance da ita dama tun farko  Daddy ne yake rawan jiki akanta momcy bata ta6a nuna mata kulawar uwa ba ko sau d'aya d'an gwara Daddy shima yanzu baya nan kaga kenan I'm the boss".    Shiru tai tana sauraronsa sannan tace'" A'a a ranar damuka fara had'uwa da CEO ai abige nake sedei ka sanni ai da Kisisina tuni na chanza masa kamanina na'sauya daga Maisha nakoma Ma'inah dashike ka'san muna kama sosai wallahi Bai gane ba, Amma dei abun Farincikin shine tun ranarda yaganni I feel Yana Sona Kuma Insha Allah shine mijinda zan aura.

Fiskarta ta nuna 6acin rai sosai yayinda takecewa; Reza wace irin magana kake haka ka'san ni Kud'i ce matsalata dazaran iyayena sunyi karayar arziki na gwammace na mutu akan inzauna dasu amasayina na y'arsu, Kai Allah ma yakiyaye sabida ko ran d'an Adam zan iya kashewa kawai sabida kud'i,
Ka'san dei Naira ba wa'sa bace mutumina. Kuma babbar maganan shine bazan iya rabuwa daku ba dazaran kuma Iyayena sunyi karayar arziki ai dokar kungiyar ta'mu ce dole murabu.

****
Mommy ta dad'e da dawowa, tun tuni take la6e a ba'kin kofan d'akin Maisha take sauraron duk abubuwnda take fad'i a waya, Aiko Sanda tajira Maisha takammala surutanta tas! sannan taja kofa tashige d'akin tamkar daga sama tafad'o.  Wuf!!! Maisha ta mike tana zazzaro idanuwa yayinda ta gyara murya, tanacewa" Momcy yaushe kika dawo gida? Na samman kince yau zaku dade sosai a wajen aiki. Tafad'a muryarta na karkaruwa domin ayadda taga fiskar mumsy'n nata ta tabbata babu shakka taji duk maganganun dasukayi awaya kuma dei da alamu ranta ta6aci sosai sabida har kwalla tagani a idanuwan ta.

"Isha zauna" Momy tafad'a cikin sanyin murya. Babu musu Maisha tazauna agefenta kamar yedda tafad'a tai ta'gumi tamkar mutuniyar arziki.  "Tarbiyar danabaki kenan? Momy ta'kara tambayarta cikin nitsuwa.  Girgiza kai Maisha tai muryarta na karkaruwa tafara magana "Momcy amma toh ai' Bata karasa kalmarba Mommy ta katseta "Rufemin Baki Maisha daman ashe Yan Sandan dasukazo nan gidan jiya had'a baki kikayi dasu sabida kawai idan wannan yariny'ar me ma sunanta... Miemah tadawo gida sai in'korota? Isha meyesa kike irin haka? Atunaninki San danake nunamiki ta fi ta Ma'inah? Wallahi kinyi kuskure babba sabida duk d'aya kuke awajena, dashike ba'nasan tarbiyarki ta lalace sabida jinina ce ke, Im your Mother, ni ko kinfi kowa sanin babu abunda nafi so da 'kauna a duniya irin Y'ayana wato dake da Ma'inah. Believe me child Momcy zata iya sadaukar da rayuwarta kawai sabida ku, Amma sometimes I wonder,  Kwata kwata ha'laiyar ki ta banbanta dana Y'ar uwarki she never disappoint me, Ma'inah ta banbanta dake Maisha I don't know why she is really sweet tanasan kowa kuma batada wannan Ki'shin naki, she always makes us  proud as her parents, Amma banda ke? meyesa kika za6i wannan rayuwar Maisha? Believe me or not I love you so much shiyasa ako yaushe idan kinyi laifi nakan danna zuciyata sabida bansan ai miki kallon wacce batada tarbiya, Maisha kin tura mahaifinki bango shima tun yana danna zuciyar nasa har kika Sany'a masa hawan jini ayanzu Babu yedda zaiyi, Dani da Mahaifinki duk munsan kina shaye shaye Maisha idanfa baki dena wannan munanan ha'laiyar nakiba Zaki iya sanyamana hawan jini dikkaninmu mu mutu a tsanadiyar ki.

Tagwaye (Identical twins) Where stories live. Discover now