PART 28

2K 131 14
                                    

____IDENTICAL TWINS BY BASMA_BASHIR

"Allahu Akhbar, Kai Masha Allah, Allah Mai halitta fine girl ohhh, my princess, Mrs Asad Abdallah AKA Miesad, Sarki sai Allah babu abin bautawa da gaskiya sai shi".
Duk wannan surutan Asad shi kad'ei yaketayi tamkar mahaukaci, Kyau'n Miemah ta rud'ar dashi, tun tuni yake la6e cikin flawowi yana sa'ce kallon Miemah dake chan cikin ZMZ Atlantic Garden tareda Mainah suna tsintan flawowi. A ransa yake Allah Allah takawo masa flawar datake tsinta amasayin kyautar masoyiya zuwaga masoyi.

"Man meye kakeyi anan kamar wani criminal?
Tin tuni Zaid yake masa magana amma duk hankalinsa ba'ya wajen. "Asad are you ok? Ya'kara tambayansa cikin rud'ani yayinda yad'aga ido yanabinsa da kallo, sai yanzu Zaid yaga'ne inda hankalinsa yake "Miemah ta sace Zuciyar abokin nawa koh? Yafad'a cikin sany'in murya kamar yedda ya'saba. 
Dasauri Asad yamaida kallonsa ga abokin nasa in a very serious tone yasauke murya chan 'kasa yace' Look Zaid I love her, Kuma wallahi the truth is I can't live without Miemah.

Shiru Zaid yai, yanakuma binsa da kallo a nitse Yayinda yakecewa' Bazan iya rayuwa dawata y'a mace ba ko ita wacece ba'yan Miemah, a ranar danafara sany'ata cikin idaniyata sai nadena ganin sauran Matan amasayin mata, zuciyata batada wata tunani sai nata, idanuwata basu kallon wani hoto bayan fiskarta atakaice dei I'm in love bro. Sedei inaga kamar Miemah bazata ta6a bani had'in Kai ba, sabida halinda iyayenta suke ciki....

'Kar kace haka abokina.... Zaid ya katseshi; Asad Kar'ka samu damuwa batun Iyayenta because I have already Promised my wify (Ma'inah) cewa Iyayen Miemah zasubar gidan yari nan bada jimawa ba, so wannan ba matsala bace, ka'fi kowa sanin ko wanene Zaid Muhammad Zabir komai nafad'a just consider it done.  

Asad kam shiru yai yana kad'a kai, Sai yanzu yaji kwanciyar hankali, inda ya sauke Doguwar nunfashi tareda hamdala. Rungume abokin nasa yai Kai tseye "Thank you so much bro, you are the best.

     **************************
"Teddy (Ma'inah) dan Allah tashi mutafi gida tun tuni kike wannan kukan wanda ba'ta 'karewa, munfa kai kusan awa guda cikin wannan wajen.

Har 'kasa Miemah ta sunkuyo tana rarrashin Mainah, Amma tamkar zuba petrol cikin wuta tana kuka sosai Babu fa'shi.  Tinda Anisa taba'su labarin Hajiya Turai, Mainah ta'kasa rike hawayen ta, tausayin rayuwar Zaid dakuma Sonsa ta'kara shige zuciyarta sosai. Tunanin hanyarda zatabi tafad'awa Momy da Daddy batun auren nasu take, sabida ko ayau Zaid yabukaci aurenta amincewa zatayi kai tseye.

Dakyar tamike jiki a sanyaye ta tattaro flawowinta, itama Miemah ta kwaso nata suka kama hany'an gida.  A kafa suke tafiya suna hira abarsu, Sanda sukayi tafiya mai nisa, ka'min sukai 6angaren Aunty Rahila sai ga wata santaleliyar mota ta shige gabansu. Basuyi wata mamakiba dashike shi Zaid ba'ya hawan mota sau biyu, idan dei yafita da sabuwar mota sedei kuma wata sabuwa a Leda, ba'zai 'kara fitowa da wanchan ba.
Kawai sunaganin motan Babu tantama Zaid ne aciki, Mainah har taji wani iri aranta yanayinda batama ta6ajin irinsa arayuwarta ba dasauri sauri zuciyarta tafara bugawa.

Asad ne yafito, ya'sha wanka Masha Allah, yanafita wajen takama kanshin turaren jikinsa. Alokaci d'aya suka 'kira sunansa da mamaki "Asad? Nan da nan suka 'kara duba lambar motan (ZMZ) arubuce abayanta da manyan baki.

Sake fiskarsa yai yawashe hakora yana dariya, "Sabuwar motarda abokina yabani kenan amasayin kyautar taya murya" yafad'a yana 'kara murmushi. Ta6e baki Mainah tai tad'aga giranta sama tana kallonsa "Murna kuma?

Yawani had'a fuska, yaci serious ayayinda yakecewa' Murnar samun Mata, na'samo matarda takwanta min arai kuma dayardan Allah itace matarda zan aura nan bada jimawa ba.

Miemah dei Babu abinda take fad'i sai murmushi, Ma'inah ce sarkin surutu har buga tsalle tai tana tayashi murna "Who is this lucky girl Masha Allah, Wacece surukan ta'mu?

Tagwaye (Identical twins) Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon