PART 39

2.5K 170 49
                                    

           DEDICATED TO ALL MY LOVELY
             FANS, LOTS OF LOVE ❤️❤️❤️

____IDENTICAL TWINS BY BASMA_BASHIR

                          ♥️ ENJOY ♥️

Tukin awa guda ce takai Miemah gida, afisace tafito cikin gaggawa tanemi taimakon securities na gida suka kai Zayyad d'akin Zaid inda batareda 6ata lokaciba aka 'kira Likita yazo ya goggoge wajen ciwon ya d'aura mai drip sannan ya rubutamusu magunguna.

Hatsarin yazo masa dasauki sabida babu karaya ko d'aya ajikinsa, kansa ne dai ya buge sosai amma Insha Allah komei zaiyi dedei. Cewar likitan 'kikwantar da hankalinki.  Miemah tana share hawayen dasuka tarunmata a ido tace' Na'gode doctor   nidei ayanzu banida wata buri face naga Zaid ya farfado ka'min mahaifinsa da Ma'inah sudawo su tsameshi cikin wannan halin, na'san zusufi kowa damuwa.

Allah yasa, Likitan yafad'a cikin sany'in murya inda yadafa jakarsa yanamata sallama 'sai anjuma akula dashi sosai anjuma kad'an zan dawo muga ko akwai wani improvement daza'a samu.

Ahaka hirarsu ta kasance tareda Miemah sannan ya sallameta yatafi, Miemah ta'koma d'aki tazauna tasashi agaba sai kuka take tana fata yabud'e idanuwansu before Mutanen gida sudawo.

        ****************************
Dreba yanajansu cikin Mota kirar Lemozine 2019, motan ta daukesu duka Aunty Nasiba, Umma Aisha da Aunty Rahila suna zaune akujeran baya sai kuma mommy dake zaune tareda y'arta, sosai ta manneta ajiki tamkar jinjira tarike Mainah tana shafamata fiska. Anisa koh sune a tsakiya tareda kannenta babu mai cewa wani Sannu idanuwarsu duk Yana kan wayoyinsu. Daddy, Mahaifin Zaid (Baba) Tareda shi Zaid d'in duk agaba suke zaune, Zaid kam sai sace kallon Ma'inah yaketayi ta window, burinsa ayanzu kawai shine yaga ya mallaketa, takoma Mrs Zaid Muhammad Zabir.

Bayan tukin awa guda dreba yaja mota ya gangaro cikin ma'keken mansion d'insu, ahankali yake jansu har saida suka karaso ciki ya saukesu Mamy a6angarensu sannan yaje 6angarensu Mommy, Umma Aisha tareda Daddy da y'arsu Ma'inah. Zaid ne na karshe a bakin kofa yasaukeshi, yanafita ma'aikatansa dake gida suka taro akansa sunata mamaki, kowannensu yashiga duniyar tunani da rud'ani. Zaid yarasa gane dalilin hakan har saida ya daka musu tsawa "What the hell are you guys doing here? Ko fiskan tawace ta chanza muku..?

Alhaji gaskiya akwai matsala. Sergeant Sani yafad'a babu fargaba yace' kenan wannan na nufin, wani ne yakeson yai wasa da hankulan mu gaba d'aya.  Zaid yai shiru yanabinsu da kallo, kowa da abinda yake Fad'i shiko bai gane abinda suke nufi ba gaba d'aya...

***************************
Miemah tana zaune agefen Zayyad tana hawaye ganin har yanzu shiruu babu motsi tattare dashi, sai adduoi take tofa masa amma babu chanji.   "Ya Allah kabashi lafiya. Abinda take fad'i aranta tun tuni kenan. 'karar wayarta ne yakatsemata wannan tunanin. Ganin momy ce ke kiranta yasa tai saurin share hawayenta tas! Sannan tayi receiving' Hello Mommy.

"Sweetheart ina kikaje? mundawo gida bamu tsamekiba.  Rasa abun fad'a tai, tashiga tunani "Taya zanfara fad'a musu cewa Zaid yayi mumunar hatsari rai ahannun Allah kuma nice sillan, Inaaa wallahi bazan iyaba.   Shiruuu da Mommy taji y'artata tai yasa hankalinta ya'kara tashi 'Miemah lafiya, don Allah kicemun kinanan kalau babu abinda ya tsameki.

Har yanzu Miemah batayi maganaba. Kukan Mommy taji awayan "Miemah kifad'amin inda kike yanzu zamuzo tareda Daddy mud'aukeki mudawo dake gida, Sweetheart speak to me please shiru ba magani bace.  Miemah ta'kasa fad'in komai har saida taji muryan Ma'inah cikin damuwa take magana cewa" Twinny meye ya tsameki? Kodei Maisha ce tasaceki?

Anan ne Miemah tafashe da kuka tafara ambaton sunan "Zaid' bata tsaya sun 'kara wani kalmaba ta katse wayan tacigaba da kuka.

      
***************************
Sake wayan Ma'inah tai yafad'i kasa, inda ta tsaya shiruu tamkar gunki, sanda tai tsayuwar akalla minti biyar sannan tafara zubda kwalla tanacewa' Mommy meye yasameshi, Mommy Zaid, Mommy Zaid, Zaid, Daddy meye ya sameshi?

Tagwaye (Identical twins) Where stories live. Discover now