PART 5

3.2K 166 18
                                    


_______TAGWAYE_BY_BASMA_BASHIR

Asubahin farko Ma'isha ta tashi, bayan ta 'yi sallah, 'karfe biyar ta shirya zuwa office, Jiya daman cikin zumud'i takwana da Farin cikin samun aiki ababban confaninda kowa ke burin shiga aduk fad'in Duniya.  Daman chan kuny'a take idon 'kawayenta ko samaranta suka tambayeta aikin me takeyi, Amma ayanzu ta samo irin aikinda take burin samu, wanda babu mai raina mata aduk cikin abokananta da samarai.

Motarda tafi kyau aduk cikin motocinta ta za6a, afarkon zuwanta office.
Alokacinda tafito motoci basuyi yawa akan titinba, daman saurin kada motoci suyi yawa yasa tashirya tunda wuri tafita don gudun Go_Slow.

****
After a very long drive.
'Karfi biyar da rabi ta'karaso. "Wow Al_jannah tud_dunya" Gaskiya wurin yayi ba laifi.

Sake baki tayi tana kallon tsarin ginin Confanin wanda ko achan America se wane da wance suke Gina irinta.  Tamkar bakauyiya tashige tanata kallace kallace, Inda wani Security ya tse da ita "Madam from where, tseya daga nan lokacin shiga bayyi ba, se 'karfe shida?"

Se yauzu hankalinta yadawo, ta rufe baki ahankali tachanza launin tafiya tana rangwada cikin yanayin birgewa "Excuse me security ina ne ofishin Oga Kashim Sa'ad Mahmud?"

Sake bakinsa yayi shima, cikin mamaki yace; Madam kina nufin ba kida labari cewa Oga Kashim Sa'ad Mahmud ya tseyar da wannan Confanin?"... 

Tseyarwa kuma? kaman ya? Ma'isha ta ta6e Baki tana tambayarsa cikin rud'ani.

Kai tseye Ma'aikacin ya amsa mata cewa; Kashim Sa'ad Mahmud ya tseyarwa Zaid Muhammad Zabir wannan Confanin wanda yanzu takoma ZMZ Builders.

"Zaid Muhammad Zabir" Ma'isha ta nanata a hankali "Who is he?" Ta tambayeshi a bayyane...

"Ke dallah Malama dakata haka, ke y'ar jarida ce? ko aikanki akayi kizo kiringa Mana irin wannan wawan tambayoyin naki, kawai malama inzaki koma gida ki koma domin yau babu aiki Sabon CEO zaizo daga Beijing (China) ganin confaninsa, idon baza ki ko'ma ba kuwa se musan yedda zamuyi dake ka'min Tawagar CEO su'iso Sabida Zaid bashida lokacin kananan kwari irinmu.

'Kai 'dan tala'kawa ka'iya bakinka, wallahi na fi'ka tashanci, nima y'ar tasha ce na fika iskanci wallahi, Banza mai gadi'.  Ta zunburo masa baki tana nunashi da d'an yasa: Wawa d'an wahala, anan zaka 'kare wallahi.

Daga nan ne, Mai gadin yafara ma'ka mata ashar, Ma'isha ma dei Y'ar tsiyan ce ba ta barin bashi. Haka suka cigaba da zagin juna har y'an Sandan cikin Confani sukaji hayaniyar tasu. Nan da nan sojoji da y'an sanda suka taru awajen.

"What are you guys doing here? 'Katon Muryan wani Soja ne ya daka musu tsawa. Inda a firgice Mai gadi ya d'aga hannunsa sama yanacewa; Kayi hakuri sir, I surrender wallahi ba laifi na bane. Ma'isha koh ko tseyuwarta bata chanzaba ballentana idanuwanta sununa tsoron y'an sandan dasuka kewayesu, a tseye take tana musu wani banzan kallo da gefen ido.

"Ke, mekiye anan ke Kuma? 'Dan Sandan yajuya 6angaren Ma'isha.

"Gyad'a nazo tsaya. Ta amsa masa Kai tseye; Domin na san ko da bakuje makarantaba idan kunga mutum da Paper a hannunsa yana shigan company kunsan abunda takawoshi; Ta amsa da muryar mannin hauka, rashin biyayya da tsananin tsiya. 

'Daga hannu sergeant yayi zai tsinke ta da Mari kenan akaji jiniyar sojoji, hayaniyar mutane dana motoci many'a da 'kanana sunata gangarowa hany'an company. Daga nan y'an sandan duk suka watse suna koran mutane a kan hany'a anata tsanarwa cewa CEO Zaid yakusan 'karasowa, ya sauko a ZMZ Hotel cikin awanni 'kalilan zai 'karaso cikin company.

Da sauri Ma'isha tashige motarta tana nunfashi sama sama, haushi kamar zai kasheta dama so take wannan sojan yasa hannu yamareta, da kuwa yau zaiga bala'i, wallahi se Abuja ta kama da wuta.
Da wannan tunanin taja motarta kan hany'a aiko tana haurowa titi taga babu hany'a. Y'an Sanda da Sojoji sun rufe ko ta'ina Motoci ne Many'a Many'a a wurin. 

Tagwaye (Identical twins) Where stories live. Discover now