PART 24

1.9K 149 8
                                    

____THIS CHAPPY IS DEDICATED TO
ASAD ABDALLAH___


Hello fans here is another update 4 u❤️,
Note👇👇👇
Kowa yayi kokari yabada amsarsa a part 23 (previous chapter) sannan kukaranta wannan sha'fin shima kuyi kokari ku rubuto comment dinku a karshe, idan kunyi hakan kai tseye zanyi muku publishing part 25 da 26 alokaci d'aya Kuma kada ku manta da tauraron dake gefen wayoyinku, Vote please😉😉😉 Enjoy 👇👇👇

_____IDENTICAL TWINS BY BASMA_BASHIR

👇👇 ENJOY👇👇

Asad yana idar da Sallah yai 6angaren Aunty Rahila daman cikin damuwa yake sosai, dakyar yai Sallah yana idarwa kuwa ko Addu'a baiyiba haka ya ninke Sallaya yafito masallaci aguje babu inda ya tseya sai 6angaren Mamy da sallama yashigo falo sedei Babu kowa anan, mikewa yai kai tseye zuwa d'akin Mainah a ransa yake Allah Allah yatatar ta tashi sabida idan wani Abu ya tsameta ko kad'an ba'zai ta6a yafewa kansa ba. Cikin wannan tunanin yashige d'akin ko sallama babu, ka ce wurgoshi akayi daga waje. Shigewarsa ke da wuya yai Kacibis da Zaid, mutanen gidan duk suna nan ajere sekace wa'inda suke kar6an sadaqa, ya kallesu d'aya bayan d'aya, Yana maida Idanunsa kan gado kuwa yaga Ma'inah zaune agefen Y'arinyar da ya kade, 'Kara bud'e Idanunsa yai sosai ya gogeta ko mafarki yake, Aiko yana 'kara duba kan gadon ba abunda ta chanza Ma'inah ce take zaune tareda mara lafiyan.

Cikin rud'ani ya juye yana tambayar Zaid" CEO Maisha ce tazo duba jikin Ma'inah? Ya'kara bud'e Idanunsa sosai yace" Amma ai Ma'isha ba'ta irin wannan shigar kuma ako yaushe takansa Jan baki a le66an ba'kinta dahakan kowa ke banbantasu. To sedei kuma abunda ya'kara rud'e Masa kwakwalwa itace" Yariny'ar da ya kade she looks exactly thesame as Mainah babu abunda ya banbantasu daga shigarsu harma da nitsuwar fiskarsu iri d'aya ce. "Kodei Ma'isha ce na kad'e? Asad ya'kara tambayar kansa.

Mu 'kanmu cikin rud'anin muke: Aunty Nasibah takatse masa tunanin tanacewa; Ba Ma'isha bace ka kad'e Asad Miemah ce. "Wacece kuma Miemah?. Ta6e baki Zaid yai yanacewa; Amsarda muke bu'kata gun Mainah kenan, amma ta'kasa cewa komai sa'ta agaba tai tun tuni tana wannan kukan wanda baya 'karewa.

'Kamata yai mukyaleta har zuwa lokacinda hankalinta zai kwanta. Aunty Rahila tafad'a inda kai tseye tamike tareda Aunty Nasibah, Anisa ma mikewar tai jiki a sany'aye ta shafa kan Ma'inah sannan suka fita, Zaid ma mikewar yai tareda Asad dikkansu sunyi Jugumm suna tafiya Yana bin Mainah da kallo shiko Asad yanabin Miemah da kallo ahaka har suka fito.

Suna fita Mainah ta rungume Miemah, ta'kara fashewa da wata sabuwar kuka. Ahankali Miemah tabud'e idanuwarta nan da nan hawaye sukafara zubowa a idanuwarta "Teddy, Umma da Abba suna gidan yari" abunda tafara fad'a kenan, muryarta na karkaruwa tace'" Mominku ta koroni daga gidanta ayanzu ba'nida inda zanje. Share hawayenta tai tareda ajiyar zuciya" teddy kiyi hakuri ki rokanmin mutanen gidan nan su kyaleni incigaba da zama anan ko wanke wanke nayimuku..... Bata 'karasa furucintaba Ma'inah tasa hannu tarufe mata baki, Da mamaki a fiskarta yayinda ta'kara tambayarta" Umma da Abba suna gidan yari kamar ya?

Kai tseye Miemah ta gyad'a kai. Anan ta kwaso dikkanin labarin ta tsanar mata. A wannan lokacin kuka suke sosai abun tausayi suka rungume juna sunata kuka. Sun dade cikin wannan yanayin Ma'inah ce tafara magana" Karki samu damuwa na tabbata Zaid zai barki mucigaba da dazama anan, ke dei ki kyalesu kada ki sany'a damuwa aranki, da Momin da Maisha'n dik mutane ne Suma kuma wataran hakan zata iya faruwa dasu, ki mance da maganar su, ki kaddara su ba komai bane a rayuwarki batun Umma da Abba kuwa zan tsanarwa Zaid da Asad na tabbata zasu taimaka mana, kada kisa damuwa aranki after all we can do it.

Tagwaye (Identical twins) Where stories live. Discover now