“Ah daman baka wuce ba?”

“Cewa yai na jiraki har ko yaushe ne na dawo da ke”

Murmushi nai na bude mazaunin baya na shiga na zauna ina tuna gargadinsa na dazun cewar na rika saka niqab. Muna isa cikin asibitin na kiran sallah azahar, ko da na shiga dakinsa na samu Siyama zaune saman kujera rike da wayarta sanye da rigar likitoci.

“Matar Yaya sannu da zuwa”

Na amsa ina murmushi.

“Yauwa sannu kanwar yaya ya kike?”

“Ba kalau ba tun dazun nake jiran driver ya kai ni gida wai sai ya dawo da ke sannan za akai ni Hajiya Siyama guda gida”

Ta fada tana hararar bandakin, daga can cikin bathroom din ya amsa mata da.

“Ba a dauko Hajiya matar Alhaji ba ke Hajiya kanwar Alhaji sai a dauko ki? Waya ce ki bari saurayin na ki ya barki, ko wani ya hanaki fitowa da motarki?”

Ta matsa kusa da ni tana min rada.

“Haka fa yake idan ya samu lafiya ba ma zaman lafiya ni da shi...”

Nikam kasa cewa komai nai sai dariya nake.

“Lims gulma ta take ko?”

“A a”

Ina amsa masa ya fito daga bandakin fuskarsa na ta haske irin ta sabon ango. A take ta dauki jakarta ta mike tsaye tana fadin.

“Ni dai na tafi Allah ya bada sauki”

Na amsa da amin ina binta da kallo shi kuma ya kabbatar sallah, hakan na bani damar tashi na shiga bandakin nai alwala na fito na jirashi har ya gama sannan na gabatar da tawa. Da kansa ya zuba mana abincin a plate daya spoon ma daya ya saka ya dora abincin gafena nikan sai kallonsa nake domin na lura tun jiya yana kokarin aikin da hannun.

“Hannun ba ya maka nauyi sosai ne?”

“Ba sosai yake min ba ina sai jin kamar jijiya ta rike ne”

Ya debo abincin da kansa ya kai mu a baki sannan shi ma ya ci. Shi yai feeding dina har na koshi sannan na karbi plate din na aje, sai kuma yaja ni jikinsa ya rumgume.

“Mata da miji idan suna zaune ba a zama nesa da juna ki koyi wannan yana kara soyayyar da shakuwa ko wani gurin muka je za mu rika tunani da kewar junanmu”

Yana gama fadar hakan ya saka hannunsa cikin hijabina yana kokarin kaiwa kirjina.

“Ba bari muji da akai wanka sun wanku”

Ya fada cikin rada sai nai saurin raba jikina da nashi.

“Baka da lafiya amman sai rashin ji kake....”

“Ahen ahen ahen please nahhhh”

Yayi maganar ta sigar shagwaba kamar wani dan 3 years sai marairaice min yake yana tabe baki irin yadda yara suke idan suna son abu. Nikam abun dariya ma ya bani wannan kuma ai ya zama ba jinya ba, duk yadda nai kokarin nisa da shi sai ya ce min ba haka ba. Sai da mutane suka fara shigowa sannan ya shafa min lafiya.

A yau kam na ga yan'uwan Ahmad sosai a asibitin wata kila saboda gobe zai bar kasar ne yasa suke ta zuwa kamar ana turowa idan wannan ya fita wata ko wani ne zai shigo, duk basa shigowa hannu sake masu kawo abinci ko siyayya wasu kuma idan za su fita sai su ba ni kudi, mun gaisa da wasu da yawa daga cikinsu ya gabatar da mu kuma ya gabatar ni a gurinsa kowa sa cewa yake sun ji abu daga sama wai ba sanarwa.

“Amaryar ce sai da haka shiyasa, sai da dabara”

“Ato ko dai kwace kai wa wani ne?”

Cewar wata tabashiyarsa tana dariya.

GOBE NA (My Future)Where stories live. Discover now