“Dan Allah Malam ko zaka shiga ciki kace ana sallama da Ahmad?”

“Wai Alhaji... Alhaji ai.... ”

Sai kuma yai shiru ya kalleni.

“To bari a fada musu”

Ya nufi cikin gidan ni kuma na bude gate din daker saboda shegen nauyinsa na fita daga waje na tsaya, kamin ya fito har na matsu bugun zuciyata ya karu ga tsoro ga fargaba da tunanin rashin dacewar zuwana sai suka taru suka tsaya min a rai. A tsammanina Ahmad din zai fito ko mai gadin amman ga mamakina sai kanwarsa ta fito waton Siyama, tana ganina ta saki far'a ta karaso ta rike hannuna.

“Laaaaa In-law shine kika tsaya a waje"

Nima nai mata murmushin daya kasa boye damuwata cike da kunya na ce.

“Bana son shiga ciki ne”

Sai taja hannuna tana fadin.

“Dan Allah shigo ciki magana, sai ku gaisa da Hajiya”

“A a dan Allah ki bari, ba sai na shiga ciki ba amman Ahmad na zo....”

Sai kuma kunya tasa na kasa karasawa, sai tai murmushi.

“Ai baya nan ya tafi jos.....”

Da sauri na kalleta domin ni ba jos yace min ba.

“Jos kuma?”

“Amman ba can yace min ya tafi ba”

Wani abu tai da ido tana yar dariya kamar marar gaskiya.

“Eh na tuna daga jos zai wuce can garin da yace miki zai tafi...”

“Wane gari?”

Na sake tambaya ina ta kokarin gano gaskiyarta, sai ta fara kame kame wanda hakan yasa hankalina ya kara tashi.

“Can inda yace miki, Kadu.... Na....”

“Ni Abuja yace min”

“Eh eh daga Jos din zai je Kaduna da Abuja, daman Abujar ya kamata nace tun dazun sai na fadi wani gari”

Ta karasa tana murmushin rashin gaskiya. Hannayenta na kama biyu na rike cikin wata irin siga ta magiya na shiga rokonta.

“Dan Siyama idan akwai wata matsala ki fada min”

A iya abunda zuciyata ta raya min Ahmad na cikin gidan yace ace baya nan, hakan na nufin Hajiyarsa ta hana shi ganina kenan ko kuma wata matsalar ce ta dabam daga sashenta. Sakin hannayen nawa tai tace.

“Ina zuwa”

Juyawa tai ta koma cikin gidan, ni kuma na tsaya a gurin zuciyata kamar zata fito, hawaye sai wanke min fuska yake ina sharewa, a yanzu kam idan har ta tabbata Hajiyarsa ta shiga tsakanina da Ahmad ban san ya zan yi ba, wata kila akwai matar da take son ya aura ba ni ba shi kuma ya aure ni ba d amincewarta ba, indan sabon da tsanar uwar miji na saba sai dai bana jin cewar zan iya jure wannan idan har ya tabbata abunda nake zargi ne.
 
“In-law Hajiya tace ki shigo”

Dagowa nai na kalleta idona da hawaye na girgiza mata kai.

“A a zan tafi dai, ki ce ina gaishe da Ahmad din”

“Ba zata jidadi ba idan kika tafi ba ki shigo ba, bayan kuma ita da kanta ta bukaci haka”

“Ina tsoro kuma ina jin kunya”

“Akwai maganar da Hajiya take son fada miki dan Allah ki shigo ko kuma naje na kirata”

Na yi saurin dakatarta ita.

“A a dan Allah”

“To muje”

A dole na bita a baya bayan na share hawayena, babu abunda zuciyata take raya min sai irin cin mutuncin da Hajiya zata min ko kuma gargadi, a lokacin ne naji ina ma ace ban zo ba, kamar wata marar gaskiya haka na shiga falon sai na tsaya daga bakin kofar na zauna jikin wata karanar kujera mai kamar ta kwalliya dake jikin kofar, ita kuma Siyama ta nufi dakin Hajiyar, ni kam gabana sai faduwa yake har yawun bakina daker nake hade su, ina jin motsin saukowar Hajiyar gabana ya kara faduwa.

GOBE NA (My Future)Where stories live. Discover now