“Ya isa”

“Why?”

“Ba sai ka kai ni kofar gida ba, zan sauka a nan”

“Okay Lims komai kike so shi zan miki”

A gafen hanyar ya faka motarsa yana kokarin fita ta bude mata tai saurin budewa ta fita, sai da ta rufe motar sai ya sauke gilashin motar ya kira sunanta.

“Lims...”

Jimm tai kamar ba zata juyo ba sai kuma ta waigo ta kalleshi a tsorace.

“I love you...... I love you so much.... And i know i love you.....”

Kasa cewa komai tai kuma ta kasa matsawa daga inda take, kamar yadda ta kasa dauke idonta daga barin kallonsa, kallonta yai for few seconds sannan yai reverse ya juya ya koma inda ya fito, sai da ya fita daga unguwar sannan ya dauki hanyar gidansu cikin wani irin farinciki marar misaltuwa, abunda be taba saka ran samu ba. After yayi parking habarbar gidan ya fito yana wasa da makullin hannunsa ya nufi part din Hajiya. Kamar ya san shi suke jira yana shiga Siyama ta taso ta sauri ya rumgume shi.

“Congratulations”

“Thank you Sis”

Ya saketa ya nufi gurin mahaifiyarsa kamin tace komai ya rumgume ta.

“Na gode Hajiya, you're such a wonderful Mom, thanks for everything”

Ya saketa ya zauna kusa da ita yana kallonta.

“Na fi kowa farinciki a yau, kasan saboda me? Ka nemo matarka da kanka, kuma wacce kake jin ta kwanta maka a rai, duk a baya ma ma san kana nemo amman sai matsala ta shiga ciki, to wannan karon bana fatar sake faruwar wani abu, a duk macen da zaka aura na kan jin kamar zata malleka ka ta kwace ka ne, amman wannan yarinyar ina jin natsuwa sosai a tare da ita, na dade ina maka fatar auren bazawara musamman irin wannan mai hakuri, domin wasu zaurawa wahala ce take fito da su daga gidanjen mazajensu wasu kuma kishiyoyine suke fito da su, duk mace da zata taba aure ta fito tai zaman zawarci ba tare da ta zubar da mutuncinta ba, hakika wannan matar abar girmamawace domin zawarci abu ne mai tsada kuma mai wuyar sha'ani, duk mace da tai zaman aure ta fito tai zaman zawarci to tayi rayuwa ne guda biyu mabanbanta, akwa challenges da yawa a rayuwarta, tun daga kan uwaye yan uwa masu neman aurenta yayanta mijin da ta fito gunss ko ya rasu, zaka tarar ta fuskanci kalubale, wanda a gaba idan za tai aure zata jure hakuri domin samun ribar auren, akwai fa'ida sosai a auren bazawara Gwarzo sai a yanzu zaka sani”

Ya hade yawun bakinta sannan ta sake kallonsa tana murmushi.

“Abu na biyu kuma ina tunanin lokaci yayi daya kamata ace na bar ku kun tafi duk inda kake so kai da matarka kui rayuwarku yadda kuke so”

Yayi saurin girgiza mata kai.

“Nonono Hajiya, Wallahi ba zan iya ba a yanzu ne kika fi bukatar na zauna a tare da ke, ko ba komai Siyama mace ce zata tai aure, gidan wani zata je ni kuma aurowa zan yi na kawo, akwai abubuwa da zaki bukata wanda dole ni ko matata ne za mu yi miki, ba ki da wani zabi daya wuce ki bar mu mu zauna a tare da ke”

“Idan kuma ita bata so fa? Wasu matan basa son zama da iyayen miji na sani, musamman ma irina”

“Me zai hana ta so? Halima tana da hankali, zata so zama da ke Hajiya, kuma ai kowa da part dinsa ba part daya ba ne, to me zai saka dukanku ku takura?”

Murmushi tai.

“Allah yai maka albarka ya hada kanku ya sa wannan auren alheri a tsakaninku”

Shi da Siyama suka amsa da amin.

“Na fada mata yai magana da mahaifiyarta domin sanarwa duk wanda ya dace, saboda ina son a cikin satin nan na san an tsayardar maganar”

“Ouhhhhh Yaya da sauri haka?

GOBE NA (My Future)Where stories live. Discover now