“Wani guri ina? Ya ganku a inda be dace ba ne?”

Tambayar da Hajiya tai masa tana kallonsa cike da son jin irin amsar da zai bata. Dan murmushi yai ya shafa kansa.

“No akan wani marar lafiya ne da nace zan dauki nauyin maganinsa, kuma ita ta san mutunen shiyasa muka je tare tai ma familynsa magana shine kawai”

Dariya Siyama tai.

“Oh kishi yake dan ya ga kana sonta”

“She's just my friend”

Ya amsa ba tare da ya kalleta ba.

“Yeah i mean friend, like friend....”

Ta maimaita tana yi ma Hajiya kallon gulma.

“Gwarzo ai baya son bazarawa, shiyasa na nema masa auren Khadija ai, budurwa ce kuma mai tarbiya”

Kallon Hajiya kawao yai ya dauke kai be ce uffan ba.

HALIMATU POV.

Da tunanin Abraham na shiga gida, rokon da yai min ya karya min zuciya, indai har mutum zai hada ka da Annabi ya roki abunda kasan zaka iya masa anya ya dace na tsallake? Ko da musulunci da yace zai yi? Ko dan ya tuba da gaske? Sai dai me? Har gobe bana son jin wani kalami daga bakinsa bana kaunar ganinsa kuma bana tunanin zan koyi soyayyarsa balle har na iya kamar yadda yake tunani.
To me zanyi? Na yafe masa be bar ni ba, na san idan ma na daina kulashi hakan ba zai wadatar domin kuwa ba kyaleni zai yi ba, to ko dai na kai kararsa a wani gurin ne na fallasa sirrinsa?
A hankali na sauke ajiyar zuciya ina ta tunanin mafita, hakika ina neman abokin shawara wata zuciyar na nace min na fadawa Mama ta wani bangaren kuma ina jin tsoron yadda hankalinta zai tashi, gashi daman ba lafiya ta isheta ba ga kuma rashin mijinta ina ganin kamar idan na labarta mata hakan zai iya janyo mata matsala, amman ai bani da abokiyar shawara sai ita bana da wanda ya fita, ko ba komai na san dole zata tambayi waye Abraham kamar yadda ta bukata dazun. Har na unkura zan tashi da zimmar shiga har uwar daka na labarta mata komai sai muk ji sallamar mata biyu tun kan na ga mahaifiyar Aminu na gane cewar ita ce saboda yanayin maganarta.
  Bayan Inna ta amsa musu suka nufo falon Mama suna ta doka sallama, ni da Mama dake can cikin daki muka hada baki gurin amsa musu, komawa nai na zauna Mama kuma ta fito daga dakin sanye da Hijabinta. Kallo daya zaka yi ma Hajiya ka fahimce cewar tana cikin tashin hankali, daman can haka take Allah ya zuba mata son yaya musammn Aminu bata kaunar abunda ya same shi, yana daya daga cikin dalilin daya saka ko fada mukai ko na kai kararsa sai ni ta ba ni laifi.
Sama sama suka gaisa da Mama har take mata ya karin hakuri, amman idonta na kaina tana min wani kallo kamar na mamaki.

“Halima gurinki muka zo”

“To Hajiya Allah yasa ba laifi nai ba”

Na fada ina kallonta sai ta dan tabe baki tana murmushin da ni kaina na san be kai zuci ba.

“Akan maganar Aminu ne da kika sa aka kama, yanzu abunda kika yi kin yi daidai kenan? Ko ba komai ai uban yayanki ne komai Aminu ya lalace sai kin fi kowa jin ciwo, haka komai Aminu yai arziki sai kin fi kowa jindadi, saboda yayan da ke tsakani, yanzu daidai ne ki saka sojoji su kama shi bayan kin san ba za su masa da sauki ba?”

Da fari murmushi nai kamin mamaki ya biyo baya ya na jin kalamanta na rainon waya da take akai.

“Aminu ba ni yai fada ba, kuma ba ni na saka a kama shi ba”

“To bakinku dai daya kenan? Shi yace ba da shi yai fada ba da ke yai, ke ma kin ce haka, yanzu ina gaskiyar magana a nan...”

Mama ta tari numfashinta tana kallona.

“Ba haka zaki ce ba Halimatu, ki fada gaskiyar abunda ya faru, kuna hanya ne na ganku ya fara fada yana kiranta matarsa yana masifa da shi wanda suke taren, sai kuma gashi ya buga kanta da murfi mota a kokarinsa na ya jnyota daga jikin motar mutumen sandiyar haka ya fasa mata goshi dai kina gani a goshinsa, shi kuma wanda suke tare yaji haushi ya saka soja suka kama shi”

GOBE NA (My Future)حيث تعيش القصص. اكتشف الآن