“Yes na gane shi kullum nn yke zama”

“Ka sa a dauke shi a kai shi gidan mahaukata”

“Why?”

“Why? Ya zan baka umarni ka tambayeni why?”

Ya amsa a fusace, kamar Yunus din ba abokinsa ba ne, saboda yau yana cikin zafin kai. Bayan ya kashe wayar yaje gaban madubi yan duba idon, idonsa daya yayi kwancin jini a ciki gaba daya gefen idon ya kumbura, abunka da farin mutun har wani ja gurin yai.

  “Ina zaman zamana ta ja min masifa.....”

Ya karasa maganar ta tari sai jini ya biyo baya, daman haka yake yanzu da ransa ya bace sai ya fada tarin jinin sai ciwon kirji.
  Toilet ya nufa aman jini yai ba kadan ba, shi kanshi sai da abun ya dan tsorata shi, har yana zargin wata kila saboda ya sha ruwan sama ne abun ya kara hade masa, wanka yai sannan ya dawo dakinsa ya sha maganinsa ha kwanta.

Sai 4:21 ya farka, sallah ce abunda ya fara gabatarwa sannan ya duba idon nasa kamin ya nufi part din Hajiya. Tana ganinsa hankalinta yai mugun tashin musamman idon nasa wanda ta hango jan jini a ciki.

“Miya same ka Gwarzo?”

“Hadarin nan ne da ya taso ina kokarin shiga, mota sai kasa ya shigar min ido”

“Wannan ba kasa ba ne, hannu ne ga kwancin shi nan a idonka, kaga ni ko shiyasa bana son kana zuwa kana dadewa a waje, na sha fada maka da kun gama aiki ka rika dawowa gida, na san halinka da zuciya wata kila kaje ka bugu wani ya rama”

Hannu ya kama yana kokarin zaunawa da murmushi a fuskarsa.

“Haba Hajiya ai na girmi wannan, Wallahi kaddara ce kawai amman In-Sha-Allah ba zai sake faruwa ba”

“Bari na kira Doc Nura”

“Naje gurinsa ya bani magani ya duba idon”

Sam bata yarda ba har sai da ta kira shi da kanta tai magana da shi ya tabbtar mata da cewar ya dubashi sannan hankalinta ya kwanta.

“And daga yau ba zaka je aiki ba sai nan da one week”

Da sauri ya kalli Hajiyarsa yana sakin baki.

“Amman Hajiya kin san idan ba da ni ba wani abun ba zai yiyu ba”

“Doka ta ce wannan”

Ta fada fuskarta babu alamun wasa.

“Yaro ba san ciwon kansa ba, sai idan ana nuna maka abu kace kai ba yaro ba ne”

Rasa yai abunda zai ce mata, ba zai iya karya dokarta ba, kuma ba zai so fashin zuwa aiki ba, zai iya amfani da bakin gilashi ya rufe idonsa.

“Idan an yi magariba ka kwanta karka tashi sai an yi isha'i, zan dafa maka carrot da allayau da wake yanzu suma suna gyara ido”

A dolen dolensa ya amsa mata da okay, ta tashi ta shiga kitchen da zimmar dora masa girkin, shi kuma ya bita da kallo yana ta tunanin randa Hajiya zata yarda da cewar ya girma san ciwon kanshi.

HALIMATU POV.

A hankali na kalleshi, fuskarsa a hade take sam babu alamar wasa a umarninsa. Na sani ba lallai ne su yarda su canja min aiki ba, balle kuma har su yarda na rika saka wasu tufafin na dabam, Ahmad ba zai min wannan lamanin ba, ko a da balle a yanzu da ba san yadda na baro shi da karfi ba, ba laifi ya nuna kulawarsa tun da har ya taimaka min ba dan shi ba wata kila da yanzu na zama gawa, domin ba kadan Kabir ya makure ni ba.
Tunanin nake ta yi ni kadai ina shafa wuyana da har yanzu ciwon yake min.

“Amman za su iya cewa ba za su yarda na daina saka kayan ba”

“Sai ki daina aikin”

“Idan na daina aikin da me zan kula da kaina? Kamin na samu wani aikin abu mai wahala, kuma ka san bana da mai taimakona a yanzu sai Allah”

GOBE NA (My Future)Opowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz