Ta karasa tana fashewa da kuka, Hajiya ta tashi daga kujerar da Siyama take zaune tana rarrashinta.

“Haka Allah yake ikonsa, haka na rasa mahaifinku a lokacin da nafi tsananin bukatarsa, amman da nai hakuri sai komai ya wuce, na koma ina farinciki kamar ba ni ba, idan muka yi hakuri sai ki ga Allah ya sauya mana da wani abun na daban”

Siyama ta rike hannun Hajiya tana ta kuka, haka take a duk lokacin data suna Baby, domin ta zame mata kamar kawa kusan abubuwa da yawa a tare suke duk kuwa da kasancewar ta girma sosai amman ta dauke ta kamar kawarta.

Magani ne first abunda ya fara sha a lokacin da ya shiga part dinsa sannan ya cire tufafin jikinsa ya shiga bandaki ya sakarwa kansa ruwa, ya fi karfin 30m ruwan na dukan kansa sannan yai wanka ya fito daure da towel, zuwa yai gaban madubi ya tsaya yana kallon kansa. Ba rama kadai ba har bakin rai mutuwar Baby Namra ta kara masa daman can dariya ba babinsa bace balle yanzu da yake jin abune mai wahala wani abun dariya ya kusance shi balle har yai ta, a nan ma ya dade yana kallon kansa kamin ya saka kayan bachi ya kwanta.

Da wuri ya farka saboda akwai abunda yake son yi a office, ko da ya fito part dinsa cikin shirin zuwa office ya fito ya shiga part din Hajiyarsa 7:13am. A kitchen ya sameta tana hada musu breakfast, tana da mai aikin amman ta fi ra'ayin girka musu da kanta musamman shi da tasan ba ko wane abincin yake ci ba, gashi da kyama komai tsaftar mace idan hankalinsa ba kwanta ba sai yace ba zai ci abunda ta dafa ba.
 
“Yau da wuri ka tashi gashi ban gama hadawa ba”

“Akwai abunda nake son yin a office fin ne shiyasa”

Ya fada yana daukar cup ya hadawa kansa tea.

“Zan tafi yanzu idan komai ya zama Ready a fada min na aiko direba ko kuma na dawo na ci”

“Okay Allah ya maka albarka”

“Amin”

Ya amsa da dan murmushi kadan a fuskarsa sannan ya fito cire da kofin tea ya nufi motarsa ya bude ya shiga, yana mata key mai gadin ya bude masa gate ya fice, da hannu daya yake driving dayan hannun kuma na rike da  cup din yana kurbawa a hankali.
Yana kusan isa kamfaninsa ya rage gudun da yake yana ta kallon Halimatu ta cikin bakin gilashin motarsa, shi be san abunda take a nan ba kusan kullum indai yayi sammako sai ya ganta idan kuma zai tashi ma yana ganinta tana bawa mahaukacin nan abinci, ko miye alakarsu oho! Ko da yake ita din ma ai kallon mahaukaciya yake mata, shi ganinta da yake kusa da kamfaninsa ma bata masa rai yake domin bayan mutuwarsa babu wacce ya tsana irinta, sai dai duk haka idan ya ganta a gurin sai ya tsaya ya kalleta sai dai idan ya ganta ya rika jin haushinta yana jin haushin kansa, duk ranar da be ganta ba har jira yake ga ko zata zo ta bawa mahaukacin abinci.
To ko shine uban yayanta? Wata zuciyar ta tambaye shi. Oho mata ma ko wanene can ita ta sani Allah yasa ma wata rana ya makureta.... Ayyana a ransa sannan ya karasa kamfanin da kansa ya shiga cikin ana ta miko masa gaisuwa amman ko kallonsu be yi ba balle ya amsa sai wani sham kamshi yake.

HALIMATU POV.

6 MONTHS LATER.....

Al-hamdulillah Al-hamdulillah Al-hamdulillah, da sannu rayuwa ta soma sauya min ta inda ban zata ba, domin ko a mafarkina ban kawo cewar zan samu aiki a kamfanin nan ba, duba da irin mutanen da sukai applying sai dai komai na Allah ne cikin ikon da yarda ya amince aka dauke ni aiki a kamfani, aiki a gurin yamin dadi ba dan komai ba sai dan Kabir kusan ko wace Safiya ta Allah nakan siye abinci a hanya ko kuma na siyo na dafa naje masa da shi idan zanje aikin, haka ma idan na dawo indai akwai canji a jikina zan siya masa abinci na tsare shi sai an tabbatar ya ci ya koshi sannan na dawo gida, hakan kuma na karamin faranta min rai yake ba, har ta kai a yanzu idan ya gama cin abinci na tashi sai ya tashi ya bi har bakin gate din kamfanin sai idan security din sun hana shi shiga sannan ya zauna a gurin ko kuma ya koma can a inda ya saba zama ya zauna har sai na gama aikin ya fito na bashi abincin.

GOBE NA (My Future)Where stories live. Discover now