“Allah dai yasa ba su mata komai ba”

“Aa bakinta dai ne suka fasa, ina jin ko sun buga mata abu ne”

“Ayyah, Allah dai yasa ba su taba ta”

Wannan karon sarai na fahimci gun da tambayar Hajiya da dosa, ba lafiyata take nufin an taba ba, martaba take magana, da farko na ji ba dadi wata zuciyar na fada min cewar danta take tayawa kishi ko kuma take yi ma fargaba, ta wani gurin kuma tana da gaskiya domin mai kaunar ka ne kawai zai iya kulawa da wannan. Ba ita kadai ba na san mutane da yawa ma za su kawo wannan tunanin a zuciyarsu wata kila har da Abdulhamid din.

“Aa ba su mata komai ba, bakin ne dai suka taba”

Inna ta bata amsa sai Hajiya ta dora da bayanin yadda aka kawo ni asibiti.

“Ni ai ina kwance sai ga kiran Hassan, tsoro duk ya kama ni domin be saba kirana irin wannan lokacin ba, gashi kuma yace min zai yi tafiya har ya kira ni ya ce min su isa, cikin tsoro na dauka sai na ji shi ma hankalinsa a tashe muryarsa har rawa take wai na kira Husaini na fada masa yaje asibiti,na ce wace asibitin lafiya, a nan ya fada min wai makocinsa ya fada masa yan fashi sun shiga gidansa har sun yi harbe harbe”

A nan Inna ta tari numfashinta da cewar.

“To ya akai ya san sun shiga?”

“Ai makoncin nasa ma sun shiga gidansa suka karbe zinari, kuma suka shiga gidan da ke kallon na su Halimatu shi mai gidan ma sun kashe shi, to shi wannan wanda ya kira Hassan din shi ya kira yan sanda kin san shi ma dpo ne, ko da suka zo har sun gudu sai ganin gate din gidan Hassan akai a bude, shi ma na makocinsu a bude iyalai sai kuka suke”

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u, to wai turo su akai ko me?”

Inna ta tambaya sai Hajiya ta tabe baki

“To waya sani, shi dai wannan Alhaji ance ba su karbi komai ba kashe shi kawai sukai wai sun ce ransa kawai suke so, shi kuma na wannan Alhaji Munir din sun karbi gulagulai da kudi, shi ma Alhaji Munir din sun fasa masa kai ai, ko da suka kawo Halimatu Asibitin nan kansa na jini shi ma an bashi gado aka ce”

“Subhanallahi, ko shine na ji Anty na cewa na leka na ganshi? Allah sarki Allah ya tona asirin ko su waye”

A zuciyata na amsa da amin, ina ta tsarguwa da kallon da Hajiya ke min.

“Amman ke ba su dauki komai a gidan ba ai ko?”

Na girgiwa Hajiya kai alamar a'a

“Ikon Allah sai suka fasa miki baki kawai dan zalumci, kai mutum.....”

Ta karasa da fuskar tausayi, ni kam tuni hawaye sun cika min ido har sun fara wanke min fuska. Ban sake maida hankali akan duk wata fira da suke da Inna ba, domin tunani ya rabu biyu, makomata na ke hangowa da kuma kokarin wanke Abdallah da zuciyata ke yi. Anya zai iya aikata kisa? Taya mutum mai aikin kamarsa ma zai iya shiga fashi da makami? Me zai kai shi shiga? Yes wata kila ba shiga yai ba gaba daya ba, what if labawa yai a cikinsu saboda ya samu biyan bukatarsa? Can kuma wani bangare na zuciyata ya jefo min wata tambayar? Miyasa sai Abdallah na ke zargi? Mi zai saka dan'uwa yai ma matar dan'uwansa haka? Miyasa be min a lokacin da nake gidan Aminu ba sai a nan? Saboda a can yana ganin zan iya fitowa wata rana kamar haka na aureshi amman a yanzu babu wannan damar? Na riga na auri dan'uwansa dan uwan ma twins brother dinsa....
   Na kasa yarda cewar shi kadai din ne, zuciyata kuma ta kasa natsuwa cewar ba shi din ne ba, na kasa zargin kowa sai shi.
  Sai da Hajiya ta fice sannan na samu natsuwa da sukunin mikewa tsaye na nufi gurin windows domin ba Hajiya kadai ba, Inna bata cikin dakin a wannan lokacin, tsakanin kalaman Hajiya da zargin Abdallah da kuma tambayayin da mutumen yai min da kalaman Hajiya sai na rasa wanne zan fara tunani? Wasu abubuwa na ji suna min yawo a cikin kai ga wani uban nauyi da zuciyata tai. Kaina na jingina jikin window ya lumshe ido ina jin kamar zan samu mafita a nan. Ajiyar zuciya na sauke ya fi a kirga sannan bude idon da ke cike da hawaye ina ta kallon mutane da ke kai kawo harabar asibitin, duk wanda na hango burge ni yake domin na san damuwarsa ba ta kai kamar tawa ba, murmushi nake hangowa a fuskar wasu wasu kuma dariya na ke gani a fuskarsu abunda ni na gagara samu.
Wani na soma hangowa kamar Kabir kamar ba shi ba, sai da na kara maida hankalina sosai gurin kallonsa da yanayinsa na hauka da yake ciki ya tabbatar min da Kabir din ne, har yanzu tsingiltar take yana tafiya ya nufo cikin asibitin, sai ga securities din da sauri su ka zo suka rika shi suka fitar da shi daga asibitin.

GOBE NA (My Future)Where stories live. Discover now