“Ni kaina Hafiza na rasa ganene dalilin Aminu na yin haka, mutumen da can ma be kula da yaran ba, har cewa yake na tara masa yara har hudu da kurciyarsa, yanzu kuma shine yake nuna musu kulawa abun yana bani tsoro”

“Ko ma minene nufinsa ba zai samu nasara ba, matukar dan ya cutar ke ko su zai yi”

“In-Sha-Allah, ba zai samu wata dama ta yin wani abu ba”

“Amman Anty miyasa kika daina zuwa gida? Baba ma kwana biyu ciwon kafafuwansa sai tashi suke?”

A take gabana ya fadi hankali kuma ya tashi abunka y'a da uba.

“Subhanallahi amman shine ba a fada min ko a waya ba?”

“Ba ke kadai ba ko su Anty Murja da suke nesa ya hana a fada musu wai za a daga musu hankali kawai, kin san ciwon nasa idan ya tashi yau ciwo gobe lafiya haka yake masa shiyasa”

“Allah ya bashi lafiya”

“Amin, Mama da Inna sai zancen ki suke su suka ce na zo da su Namra ma mu duba ki lafiya kike? Kuma gaskiya na ga alamar ba lafiya ba”

“Kamar ya?”

Na tambaya ina kokarin kirkiro murmushi.

“Haba Anty kalle ki fa, duk kin rame kin koma kamar ba ke ba, ke da kika da jikinki mulmul ma sha Allah amman yanzu ko ki na fi ki ki ba, duk kin yi baki kin lalace Gaskiya akwai abunda yake damunki”

“Babu abunda yake damuna Hafiza”

Ina fadar hakan na juyo na fito daga kitchen din domin bana son ta cika ni da tambayoyi. Ina fitowa Namra ta fara bani labarin Daddynsu yana zuwa gurinsu yanzu har ma siyayyar da yai musu, tana cikin lissafa abubuwan da ya siyo musu sai Adnan ya karbe daga nan sai Aiman har da Amal ma labarta min take abubuwan da Daddy yake musu, wani irin farinciki da annushuwa nake ganin a fuskar yayana, da alama hakan da yake musu a yanzu yana musu dadi, ko ni da nake babban na so mahaifina a kusa da ni balle su da suke kanana kuma babu ni a kusa da su. A nan Namra take nuna min new friend dinta mai irin sunanta.

“Momi kin tuna lokacin dana bata a gidansu aka kai ni, kin suna ita ce yarinyar gidan”

Sai a lokacin na tuna har na wayi fuskarka.

“Momi Daddynta yana sonta sosai komai siya mata yake, kuma har shi yake zuwa daukarta idan zata koma gida”

“A ina kika hadu da ita?”

“A school din mu take ita ce tana so na friend tace ita bata da friends kuma Momi ita ma sunan Mominta Halima, amman ta rasu.... ”

Hannu na mika mata alamar ta zo, sai ta taso daga inda take zaune a kan Center tebur ta nufo inda nake sanye da English Wears dinta kanta babu dankwali balle ayi maganar hijabi.

“Kin ganeni?”

Na tambaya bayan na rike hannunta, sai ta gyada min kai tana murmushi irin murmushin nan na yara masu kiriniya.

“Momi na fada mata yau za mu zo gidanki shine tace tana son ta ganki, tace daddynta ya kawota kuma ya kawo ta”

Namra ta fada da mamaki a fuskarta, domin ita bata tashi cikin irin wannan gatan ba, da mahaifinta zai mata abu ko kuma ya nuna mata kula balle har ya dauketa ya fita da ita.

“Daddynta yana sonta sosai Momi har da waya ya siya mata, yana bata chocolate komai siya mata yake, kuma gidansu har da motar wasan yara ya siya mata da lilo irin an scul dinmu”

Ta sake fada, ni kuma sai nai murmushi na shafa kanta domin na san abunda yata take ji, kwatankwacin abunda nake ji idan na ga wata mace ta yi dacen mijin aure.

GOBE NA (My Future)Where stories live. Discover now