Ya yi shiru idonsa tab da kwalla, uffan Hajiya ba ta ce ba har ya mike tsaye ya saka wayar aljihun shaddarsa da ya zuba hannayensa aljihu ya nufi upstairs. Wani irin abun na rashin jindadi ke masa yawo a zuciya, haka yake samun kansa a duk lokacin da ya tuna da matarsa Halima, wacce yake yawan fada mata cewar daga ita ya gama so, mace da yake ganin babu mai hakurinta da kirkinta a duniyar nan.

Ajiyar zuciya ya sauke sau uku zuwa hudu sannan yaja wani dogon numfashi ya busar a bakinsa. Ya kai hannunsa ya murda kofar dakin Baby Namra ya tura ya shiga ciki. Agaban plasma take zaune rike da drawing book da pencil a hannunta tana drawing wani bird da ake nuna a kids channel. Daga bakin kofar ya tsaya yana kallonta zuciyarsa fal da kaunar yarsa, sannan ya karaso kusa da ita yana ayyana abubuwa da dama akan rayuwarsa da nata.

‘Ko da na ayi aure zan yi ne kawai saboda ke, saboda ni da ke mu samu kulawa amman ba dan zan taba son ko wace mace a duniyar nan ba’

Kanta ya shafa yana murmushi kamar yadda ita ma ta dago ta kalleshi tana murmushin.

“Daddy what”

“Ba komai”

Ya fada yana cigaba da kallonta, ita kuma ta maida hankalinta gurin tv ta cigaba da abunda yake. Wayarsa ya ciro ya nemo number Rayyan.

“Rayyan”

“Ranka ya dade”

“Yusuf ya kira ni wai kudin wata sun kare, na ce masa za ku yi magana akan na year sai ka bashi zai fi”

“Okay amman ban gane Yusuf din ba”

“Wanda yake Exclusive City, kudin Vip nake nufi”

“Okay ina da number shi ai bari na kira shi yanzu”

“Okay ya fada maka ko nawa ne na shekara sai na bashi”

“Consider it done”

Daga haka ya yanke wayar ya cigaba da kallon abunda yarsa take zanawa.

HALIMATU POV.

daga karshe na yanke shawarar fadawa Abdulhamid gaskiya, na san duk yadda zai ji zafi da tashin hankali ba zai kai kamar lokacin da abun ya faru ba, kwana biyun nan na lura yana cikin damuwa wata kila saboda abunda Abdallah yai masa ne a kwana baya duk da be fada min ba amman ni kaina na lura da hakan, abunda zuciyata take yawan fada min idan ban fada masa gaskiya ba, idan ya ji a wani gurin ba zai ji dadi ba ba kuma zai fahimce ni ba. Amman kuma ta ina zai ji? Wa zai fada masa bayan babu wanda ya san wannan sirri daga ni sai Allah sai kuma kawata Hajara?

Doyar da nake ferayewa na aje na rike wukar kamar ita ce zata sama min mafita.

“Zan fada masa gaskiya, ina jin kamar ba zan samu peace of mind ba idan ban fada masa ba, ina jin kamar na ci amanarsa ne”

Ni kadai nake magana da kaina a kitchen kamin na aje wukar na wanke hannuna saboda wayata da na ji tana ringing. Cikin hanzari na nufi inda wayar take, a lokacin da na kai hannu na dauki wayar sai na kasa picking din call din ganin number mai kiran duk kuwa da ba suna, Aminu ne na san ba wata magana mai dadi zai fada min ba, wata kila haukansa zai min ko kuma ya min gargadinsa na iska da ya saba, sai da ya jera min four miss calls sannan na daga, nai masa shiru tare da hade rai kamar yana a gabana.

“Hello Halima”

“Ya akai?”

Na tambaya ina kara hade fuska kamar ance yana ganina.

“Sai an yi wani abun zan kira? Alaka fa har yanzu bata yanke a tsakaninmu ba saboda yara”

“Babu wata alaka a tsakanina da kai Aminu, kuma bana fatar wata alakar ta sake kulluwa a tsakaninmu, wacan da mu kai a baya ma ka dauka cewar labari ne”

GOBE NA (My Future)Where stories live. Discover now