MATAR DATTIJO page 23

1.7K 65 0
                                    

💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
          *Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*

*dedicated to Ummy xie ina godiya da abin arzikin da kika yi min*

23

kwanci tashi asarar rai, komai aka sawa rana wata rana sai yace, yau ya rage saura kwana uku na tare a gidan dattijona, tun safe na tashi ina kukan rabuwa da innata nice har da su birgima, wani irin kaunar gida ne naji ya kamani sai na tsinci kaina cikin rashin son nisa da innah da baba.
innah ce ta shigo dakin da nake rarrashina ta fara yi gami da kwantar min da hankali, kiyi hakuri niimatullah duk ya mace yar gidan wani ce, mu ma duk haka aka rabo mu da gidajen iyayen mu tun ban kai kamarki ba gashi nan yanxu har abin ya xame mana jiki, kiyi hakuri ibada xaki tafi Allah xai baki kada, cikin kuka nake magana  ni na fasa samun ladan innah a barni a wajen Ki na cigaba da xaman, ko kuma ki biyo ni gidan da xan xauna.

Cike da kulawa ta dube ni,imar ai ba a haka Niimatullah yadda na Saba kema haka zaki saba a hankali, kukana na rika yi har da majina.

A dai-dai lokacin ne malamar da ke min gyaran jiki ta iso, gaisawa suka yi da innah cike da kulawa take min magana.
"niimatullah me ya same ki kike kuka haka har da su majina" idanuna cike da hawaye na dubeta, malama dama idan xa a yiwa mutum aure dole ne sai ya bar gida? Dan Allah ki roki dattijo ya kyale ni a wajen innata.

Dariya ta rika yi sosai lallai niimallah da sauran ki, a ina kika taba ganin an yiwa mace aure ta xauna a gidan su, ko a garin gaba-gaba ba a taba yi ba ballanta a wajen masu hankali,  dole sai kin bar gidan innah ta haka ne xaki fi samun ladan da kowace matar aure take samua gidan mijinta, idan aka barki a nan me aka yi kenan ai anyi ba ai ba.

Kuka na cigaba da yi ina shura kafata ni a lallai baxan tare a gidan dattijo ba,kiran wayar innah aka yi da sauri ta mika hannu ta dauka, dattijona ne ya kirata yake fada mata cewa ya iso tare da wadanda zasu jera min kayan dakina baya so ya ka isu gidan kai tsaye ba tare da an samu wani wakili daga bangarena ba, saboda gudun gorin matarsa, godiya innah ta rika yi masa har da dan kukanta tana sa masa albarka.

Yan uwan mamana daga bichi duk sun iso don haka aka samu wasu suka tafi jera min dakina

  dakin innah muka shiga inda aka fara gyara ni, bayan ta gama shafa min wasu abubuwa ne ta bani wani abu a kwalba wanda take fada min cewa tsumi ne da ke karawa mace ni'imar jiki, har sai da ta koya min hadinsa, inda ta fada min cewa xan samu sassaken baure da kanumfari da citta kadan da mazarkwaila da minannas da kuma, xan fara dafa sassaken bauren ne idan ya dahu na tsame shi na xuba kayan hadin da ta lissafa min a baya, idan ya dahu na sauke ta koya min ne kasancewar tana so na dauwama ina yin shi. godiya nayi mata duk da cewa ban gane abinda take nufi ba game da amfanin abinda ta fada min.

Bayan na kammala shan wannan tsumin da ta bani lalle ta dakko ta matsa lemon tsami ta xuba gishiri da kuma man zaitun kadan murje min jiki ta shiga yi sannan ta fada min amfaninsa don gyaran jiki ne, kuma ta fada min larabawa da mutanen sudan sukan yi amfani da wannan hadin don gyaran jikin su. tayi min amfani da turaruka masu kyau da kamshi duk wata gaba ta jikina sai da aka shafa mata turare.

Daga karshe ta dakko min wani hadi na musamman wanda ta fada min cewa na gyaran breast ne kuma muddin mace ta juri amfani dashi breasts dinta baxa su taba faduwa ba, shi ma ta fada min cewa larabawa ke amfani da shi, amma bata koya min hadin ba saboda tace sirrin sana'arta ne.

bata kammala gyara ni ba sai wajen sallar Magariba nayi kyau na fita, kana matsowa wajena xaka ji ina tashin kamshi na musamman, daga karshe taja kunnena a kan daina amfani da ruwan sanyi wajen tsarki ta koyar da ni dafa ganyen magarya da lalle, tace na rika amfani da su a lokuta da dama saboda rigakafi ne na kamuwa daga cutar infection.

Ba karamar godiya nayi mata ba, innah kuwa sai sa mata albarka take yi saboda malama tana iyakar kokarinta wajen ganin na xama sarauniya a wajen dattijona.

bayan nayi sallar isha'i na koma daki na kwanta saboda ba karamar gajiya nayi ba, ga tunanin barin gida da ya sanya jikina yin sanyi, ji nayi kamar xaxxabi ke shirin kama ni, innah na gani ta shigo kiran sunana tayi niimatullah tashi kije soro mijinki yazo yana son magana da ke.

Bata fuska nayi haba innah bacci fa nake yi kice masa kawai bana nan, kallona innah tayi tare da hararata bana son gaddamar nan fa niimatullah tashi kije kika sani ko abu mai muhimmanci xai fada miki, raina a bace na tashi na nufi soron, a tsugunne na same shi da alama ya gaji da tsayuwa ne shi yasa ya xauna.

karasawa wajen shi nayi tare da dan taba kansa a hankali ya dago ya dube ni yana murmushi sai an ja min aji xa a xo ko niimatullah?

Cike da shagwaba nake masa magana, ba kai bane ka tashe ni ina baccina mai dadi, tashi tsaye yayi yana dubana tare da yin murmushi

ke da kin kusa xama tawa wata rana ma baccin xan hana ki yi gaba daya, cike da mamaki nake kallonsa Allah baka isa ka hanani baccina ba tabdi jam kayi kadan yaro.

Murmushi yayi tare da lakace min hancina, xaki ga nayi kadan yarinya saura dai kwana uku Ki shigo hannuna don haka ki daina tsiwa da cika baki, kallon shi nayi kamar xan kuka, Allah tunda haka kace sai na fasa auren tunda xaluntata xaka rika yi.

Hannuna ya riko yana min murmushi ina matukar sonki baxan iya xaluntarki ba babyna, kuma da nace zan hana ki bacci ai ba wani abu bane duk soyayya ce xata sa hakan, amma fa kema a lokuta da dama kina hana ni bacci, da sauri na dube shi yaushe na hana ka bacci banda sharri fa.

dariya ya rika yi min wallahi kina hana ni niimatullah ko baki sani ba? da sauri na amsa masa da eh fada min lokaci da ranar da na hana ka.

cikin salon soyayya yake min magana, idan dare ya tsala na juya ban ganki a gefena ba sai tunanin ki da shaukin ki su hana ni runtsawa, ko yau din nan ban yi bacci ba saboda begen ki.
Turo baki nayi Allah ba kada kunya dattijon nan, murmushi yayi tare da kai hannu xai kamo ni, da sauri na kauce, zaki ga ba nida kunya yanxu baki fara ganin komai ba my ni,ima sai kin shigo fadata.

hakuri na shiga bashi, kayi hakuri to kana da kunya mantawa nayi na fada, murmushi yayi tare da riko hannuna ina sonki niimatullah ga tsiwa ga tsoro.

cike da shagwaba na fara yi masa magana ka fada min abinda ya kawo ka kaga sauro har ya fara cizona, dan murmushi yayi gami da shafa farin gemunsa wanda ya sha gyara, yi hakuri mai niimatullah nima ba a son raina na kira ki yanxu ba don nasan kin gaji da yawa, dama xuwa nayi mu yi magana a kan abubuwan da xa a yi a lokacin bikin mu.
langwabar da kaina nayi ni babu abinda xan yi kawai innah ce xata gayyato kawayenta, ni kaga ko kawayen ma ba nida su.

Murmushi yayi to ni dai sai an yi ko baki da su sai kin nemo su duk inda suke, bata fuska nayi xan yi kuka
A'a ni dai ka bar kudinka tausayinka nake ji kaga ka kashe min kudi masu yawa, yau ma ka siya min kayan daki ka bar hidimar haka kada kudinka ya kare mutane su ce wayo nake maka.
Dariya na bashi sosai kina burge ni da yawa idan kika xaro wani zancen, waye xai ce xaki min wayo kin ganki fa yar karama, harar shi nayi ka daina kallona haka idan na tashi girma sai na fika kiba

xaulayata ya rika yi, duk nacin da yayi a kan ya hada min dinner naki yarda, da xa mu yi sallama ya kirgo kudade masu yawa ya bani wadanda baxan iya fadar adadinsu ba kasancewar ban tsaya na lissafa ba sallama yayi min ya wuce gida.

Innah na dankawa kudin ko komawa ta kansu ban yi ba,saboda babu wani abu da zan yi da su, komai innata tana iya bakin kokarinta wajen ganin ta faranta min.

*jeeddahtulkhair😘*

MATAR DATTIJO CompleteWhere stories live. Discover now