MATAR DATTIJO page 33

1.4K 60 0
                                    

💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
          *Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*

*wannan shafin gaba daya sadaukar wa ne gare ku masoyana*

1-Maearyerm malakso
2-Meela
3-Maryam Bello
4-Jamila d.Gada (Ummu Yasmin)
5-Maman khaleesat
6-Rukayya Sufyan
7-Maman hanan
8-Ummu Islamm
9-Aysha Abdullahi
10-Habiba maman abulkhaeri
11-Aysha Musa
12-Maryam Aminu
13-Aminatu Aliyu
14-Huraera
15-Ummey
16-Sa'adatun hydar
17-Nafisa muhammad
18-Rahma
19-Amina Sunusi
20-Maman Fatyma
21-Khadija Abubakar
22-Ashphat Omar
23-Dija Misku
24-Shamsiyya Faruk
25-Maman mubeenah
26-Ummu hamxa
27-Maman Ummi
28-Aisha Ibrahim
29-Maryam Bello yar pot
30-Maman Amatullah
31-Maman Anas
32-Laelah
33- Sakinatu Umar
34- samira bishir
35-Respectable
36-Zee M
37-fulanee
38-Aisha b nuhu
39-Hajara lawan
40-Maman Aysha
41-Hajjo
42-Aminatou boulkassoum
43-Maryam Auwal
44-Hauwa'u hafizu alkali
45-Hauwa'u T usman
46-Amsopy
47-Ummu hanan
48-Maman Seeyam
49-Maman Amatullah
50-Rasheeda
51-Maman Ra'iz
52-Aisa yer meduguri
53-Belau sokoto
54-ummyn al-ameen
55-Salma Nura
56-Ummu hanif
57-Ummu Ameera
58-Mom khairat
59-Queen feedy
60-Mymmyn farhan
61-Ubiyyat A Tahir
62-khadijah ummi
63-Aysha Sulaiman Ahmad

33

Bai wani dade a dakina sosai ba ta rika kiransa a waya ya dawo gareta, fuskarsa cike da damuwa ya dube ni, xan koma wajen momyn munir tana kirana, bata fuska nayi tare da yin gefe da kaina, ba tare da na bashi amsa ba na cigaba da tunanina.

matsowa yayi daf da ni tare da dago fuskata kiyi hakuri nima ba a son raina xan tafi na bar ki ba, daga yau saura kwana daya na dawo gare ki da fatan xaki shirya min tarba mai kyau, don kin san ke din ta daban ce komai naki na musamman ne,  fuskata a kasa na amsa masa da to.

A sanyaye ya tashi ya fita, bin sa nayi da kallo ina tunanin irin matsalar da xan shiga idan baya kusa da ni, ji nayi kamar nasa masa kuka ya dawo dakina, xafi xuciyata ta rika yi, wani kishi ne ya taso min ji nayi kamar na rusa ihu da sauri na rika karanto innalillahi wa inna ilaihi raji'un ban taba tsammanin haka xafin kishi yake ba, kwantar da kaina nayi tare da lumshe idanuna ina tunanin mijina, na saba kwana a kan kirjinsa da jin harbawar numfashinsa yau kuma da pillow xan yi matashi, hawaye naji na shirin xubo min, a ranar cikin damuwa na wuni tun daga xuwan da yayi min da safe bata kara barinsa ya leko wajena ba.

Da misalin karfe tara nayi wanka na fara shirin kwanciya bacci, sallama naji an yi min a falo cikin hanxari na fito don ganin mai sallamar,  daya daga cikin yayan dattijona na gani, cike da ladabi ya gaida ni tare da cewa dadynsa na kirana,cikin sakin fuska na amsa masa da ina xuwa.

Hijabi na saka har kasa, kasancewar kayan bacci ne a jikina, kulle kofa ta nayi sannan na nufi wajen dattijona, a bakin motarsa na tarar da shi yanayin sa kawai na kalla nasan yana cikin damuwa.

cike da nutsuwa na karasa wajensa, a hankali ya dago ido yana kallona tare da cewa ai na xaci baxa ki xo ba Amaryar dattijo, murmushi nayi me xai hana ni amsa kiran mijina sai dai idan ko ba ni da lafiya ne.

Daga min hannu yayi tare da cewa matso nan xa mu yi wata magana, A hankali naja jikina na karasa gare shi tare da kwantar da kaina a wuyan shi, farin gashin da ke kewaye a fuskar shi na shafa kasancewar nayi missing din shi, cike da soyayya ya fara min magana.

Ina cikin wani yanayi Niimatullah,matar nan ta kasa kulawa da ni kuma ta hana ki kula da ni na rasa yadda xan yi da rayuwata, shi ne nace ki taimaka kixo ki taya ni hira a nan ko xan samu sauki da sauraren muryar ki.

cike da shagwaba na bashi amsa, ni dai baxan iya ba tunda ba lokacina bane dakina xan koma nayi baccina, ka koma wajenta ka lallabata nasan xa tayi maka duk abinda kake so.

ina kammala fada masa na kama hanyar komawa bangarena, jawo ni yayi ya hada fuskata da tasa da alama yana cikin yanayi,  kamar xai yi kuka yake min magana.

Baxa ki tallafi mijinki ki tsamo shi daga fadawa halaka ba ko, da kika ce na koma wajenta yanxu haka kofar dakinta a kulle yake ina kike so naje naji dadin rayuwata,ke da kike sona kuma xaki juya min baya Niimatullah wane yanayi kike tunanin xan fada idan kika bar ni, na dade da fada miki kice nutsuwata kece farin cikina.

kaina a sunkuye na bashi amsa, kayi hakuri dattijona baxan iya danne hakkin wata ba,tunda lokacinta ne kaje ka sameta idan bata baka kulawa ba, ka dawo xan kula da kai.

fuskarsa cike da fara'a ya dube ni da gaske kike amaryar dattijo? cikin kulawa nace masa eh, rungume ni yayi yana kissing dina, na gode Allah yayi miki albarka Niimatullah, dole ta rika bakin ciki da ke kin fita biyyaya kin fita komai, na gode amaryata, cikin rada nake masa magana kaje yanxu ina jiranka a cikin gida.

cikin rawar jiki ya tashi ya nufi bangaren Hajiya maryam, sallama ya yi amma shiru ba a amsa masa ba, dudduba dakin ya shiga yi ko xai ganta, a bakin brander ya hangota tsaye, jikinsa a sanyaye ya karaso wajenta.

fuskar sa cike da murmushi ya bude baki xai mata magana, hannu ta daga masa, kai malam dakata tsohon munafuki duk abinda kake yi a kan idona, ka koma wajen kaxamar matarka tayi maka duk abinda kake ganin na gaxa yi maka, ni baxan iya da wannan jarabar taka ba da nacin tsiya, ka koma maybe ita xata iya jurewa, tunda ita jaka ce amma ni baxa ka xo ka takura min ba.

sakin baki yayi yana kallonta ya rasa bakin magana masifar dai ta cigaba da yi masa a fusace ya bata amsa, idan na danne miki hakki kice yarinya ta yi miki asiri bayan komai ke kike jawowa kan ki, wlh xan tafi baxa ki kara ganina ba xaki gane ba nida xuciya.

da sauri ya bar wajenta ya nufi sashin Niimatullah, A kulle ya tarar da kofarta, A hankali ya rika kankwasawa tare da kiran sunanta.

cikin bacci naji alamun ana buga kofar dakina a hankali na bude ido na fito parlour ta window na hango dattijona, yana ta faman bugu leka kaina nayi, muna hada ido ya fara min magana, ki taimaka ki bude min na shigo Niimatullah kada na shiga wani hali.

makale kafada nayi, baxan bude ba Allah sai dai ka koma wajenta, na fada maka baxan taba shiga hakkinta ba, magiya ya rika yi yana ta bugawa komawa kan kujera nayi ina kallon shi ina masa dariya, gaba daya ya fita daga hankalinsa ina mamakin yadda yake da jaraba duk da kasancewarsa dattijo ya kamata a ce yayi sanyi amma abin nasa ya wuce gona da iri.

Buga kofar yake ba sassautawa yana ta magiya, ni kuwa sai dariya nake masa cike da tsokana nake masa magana, baxan fa bude maka ba sai dai ka koma inda ka fito kuka yake min sosai, a xuciyata naji tausayin sa amma baxan bude masa ba sai na gama ja masa Aji.

*follow me on wattpad @jeeddahtulkhaeer Tijj*

*jeeddahtulkhair😘*

MATAR DATTIJO CompleteWhere stories live. Discover now