MATAR DATTIJO page 58

962 39 0
                                    

💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
           *Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*

58

Bata yi gardama ba ta biyo ni, jikinta a sanyaye take tafiya har muka isa dakina, da sallama muka shiga dakin gaba daya suka amsa mana na lura da dattijona sai hararta yake yi, ita kuwa yi tayi kamar bata ganshi ba sai muxurai yake yi, gefe muka samu muka xauna gaba dayan mu sunkuyar da kai muka yi muna jiran jin abinda xai fito daga bakin su innah.

Shiru suka yi na dan lokaci sannan innah ta katse shirun da aka yi tare da cewa, Hajiya kiyi hakuri na taso ki kina hutawarki, kanta a sunkuye ta amsa da ba komai innah, magana ta fara yi abinda yasa ku ka ga na tara ku a nan don na kawo karshen matsalar da ke faruwa a gidan nan saboda xaman ku babu dadi a haka, juyar da kanta tayi wajen dattijo Alhaji ina baka hakuri Allah ya huci xuciyarka dan Allah ka dawo da Maryam kayi mata afuwa Insha Allah xata gyara halayenta.

Sauke ajiyar xuciya yayi Shikenan innah ba komai na dawo da ita albarkacin ki wallahi da baki shiga maganar nan ba baxa ta dawo ba na rabu da ita har abada.

Godiya innah tayi masa tare da sa masa albarka juyawa tayi wajen hajiya maryam tayi mata nasiha sosai a kan biyayyar aure sannan ta umarceta da yin kawaici abisa dukkan abinda ta gani na rashin dadi.

hawaye ne ya rika sauka a kan fuskarta cikin rawar baki ta fara magana, na gode innah ashe dama abinda wasu mutanen ke fada gaskiya ne kishiya yar uwa ce ba abokiyar gaba ba, gashi nan na gani da idona sanadin niimatullah na dawo dakina na gode innah Allah ya saka da alkhairi Insha Allah duk nasihar da kika yi min xan yi amfani da ita.

Riko hannuna tayi niimatullah na gode dan Allah ki yafe min a bisa dukkan abinda ya faru a baya, ashe da nake gudunki ke alkhairi ce a gare ni na gode Allah ya hada kanmu hakuri ta juya ta bawa dattijo shi ma a nan take ya yafe mata tashi tayi ta nufi bangarenta tana kuka.

Tana shiga ta dauki waya ta kira kawarta zainab, bayan sun gaisa ta fara yi mata magana Gaskiya a yanxu na gano kishiya yar uwa ce yanxu ta sanadin niimatullah na koma dakina, tabe baki tayi tare da turo dankwali gaban goshi, wannan munafunci ne kawai tunda tasa a kore ki dole tasa a dawo da ke, tayi haka ne fa ba don Allah ba sai don kissa da kisisina ke ina kwakwalwarki take tafiya ne gaba daya kin manta da sharrin kishiya ko? Sauke ajiyar xuciya tayi

Wallahi sis zee Niimatullahi da iyayenta mutanen kirki ne mu ne muka yi musu mummunar fahimta da na tsaya na nutsu tun farko da abubuwan da suka faru a baya basu faru ba, da tana da mummunar niyya a kaina baxa ta yarda a dawo da ni, tunda babu kalar rashin kirkin da ban yi mata ba,kashe wayarta tayi don tana jin baxa ta iya jurewa sauraren  dukkan abinda take fada mata ba domin ita duk a matsayin soki burutsu ta dauki xantukanta, duk kiran da tayi mata a lokacin bata dauka ba ashe shiryawa take xata xo gidanta.

Bata dade da ajiye wayar ba ta iso, tun daga bakin kofa ta fara xaxxaga mata masifa, a kan me yasa xata amince da makircin da Niimatullah tayi  mata,duk kokarin da tayi don ta ganar da ita taki ganewa a ranar baran-baran suka rabu.

Tun daga wannan lokacin xamantakewar mu ta canja, kanmu ya kara haduwa duk abinda xai janyo mana fitina ina kokarin kauce masa sannan shi kansa dattijo ina kara saita shi a hanya wajen tsayar da adalci a gidansa bana yarda ya danne mata hakkinta ko yaya yake, ba karamin ji da ni take yi ba yanxu na xama masoyiyarta duk abinda xata yi sai ta nemi shawarata yanxu ta kai ta kawo ko unguwa xata je sai ta tafi da ni duk irin xugar da kawayenta ke mata ta toshe kunnenta muna xaune lafiya, dattijo kuwa kullum cikin saka min albarka yake saboda a yanxu ya fi jin dadin rayuwar gidan.

Innah bata dade ba ta koma gida ganin yadda xaman gidan yayi daidai don komai maman munir ke shigowa tayi min ko girki bata bari nayi, yayanta kuwa sun xama kamar nawa komai zasu gabatar sai da shawarata.

*follow me on wattpad @jeeddahtukhaeer Tijj*

*jeeddahtulkhair😘*

MATAR DATTIJO CompleteWhere stories live. Discover now