MATAR DATTIJO page 7

1.8K 91 0
                                    

*Jeeddahtulkhair😘*
[9/30, 4:44 PM] itz B Y ebrerheem: 💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
          *Adam*
*(Jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*

*dedicated to Hafxiyya Nasidi*

*ina godiya masoya littafin Matar dattijo, tun daga kan masu kirana a waya da masu biyo ni private ina matukar godiya ALLAH ya bar xumunci*

7

Gaba daya naji auren ya bar kaina saboda cin mutuncin da matar nan tayi min, sai na gwammace xamana ba auren na hakura da samun ladan da ake samu kukana nake tayi inna na rarrashina.

yana kirana a waya na fara yi masa kuka, rarrashin duniya yayi min amma naki yin shiru,  cikin kulawa yake min magana, fada min damuwar ki Niimatullah, cikin shashshekar kuka nace ni dai na fasa auren nan ka sake ni na huta.

A firgice yace min me kika ce Niimatullah lafiyar ki kalau kuwa, kike wannan maganar? ta cikin wayar naji an daka masa tsawa, kayi asara tsohon banxa ka rasa wacce xaka auro sai kaxamar yarinya yar cikinka.

muryarsa na karkarwa naji ya ajiye wayar, daga lokacin bai sake kirana ba har sai da muka yi kwana daya a haka, sabo turken wawa kwana biyun nan da ban ji muryarsa ba har na shiga damuwa, ko makaranta na kasa xuwa ban tabbatar da irin kaunar da nake masa sai a yanxu da yayi nisa da ni.

A ranar da xamu cika kwana biyu yaxo gidan mu, kansa na gani daure da bandage, a hankali yake takawa da dukkan alamu yaji jiki, tausayinsa ne ya kama ni, da sauri na karasa wajensa ina tambayarsa dattijona, a hankali ya dago ido ya kalle ni, sake tambayarsa nayi me ya taba min lafiyarka haka? dago ido yayi tare da yi min murmushi, accident nayi jiya, sannu muka rika yi masa ni da innah, sannan na shimfida masa tabarma a daki.

shagwaba na fara yi masa ina kuka, shi ne ka tafi ka manta da ni ko, ka kashe wayarka baka neme ni ba.

Hakuri ya fara bani, ki saki ranki nayi miki bayani sannan ki daina wannan kukan kada ya taba min lafiyar ki, jiya mai mota ya ture ni ya take wayar da ke hannuna shi yasa ban kira ki ba. ban gamsu da kalamansa ba don haka na sake jefa masa wata tambayar da ta firgita shi.

to naji Allah ya kiyaye gaba, amma wacece wacce naji tana xagina tana xaginka? dabarbarcewa yayi anya kuwa, ni babu wanda ya xage ni ko ya xage ki, ina ganin matsalar network ne kin san wani lokacin yana hadewa.

girgixa kaina nayi sam ban yarda ba, gashi nan naji tana ce min kaxama, ni Allah na fasa auren baxan je a rika xagina ba, duk wankan nan da nake yi sau biyu a rana wata ta rika kirana da kaxama, rausayar da kansa yayi gefe yana ta kallona ina fada har da shure-shuren kafa, kiran sunana yayi cikin sassanyar murya da alama yana cikin damuwa

ki kwantar da hankalin ki Niimatullah idan kin tashi tarewa gidan ki daban xan miki, gyara xama nayi ina kallonsa.

gidana daban fa kace ni dai Gaskiya ban yarda ba, gara ka saka ni a gidan da mutane suke, kasan ni akwai tsoro, murmushi yayi tare da cewa,  Allah sarki wato shi yaro ala kulli halin yaro ne.

jawo ni jikinsa yayi na rika kokarin sai na kwace na matsa gefe amma na kasa, rada ya shiga yi min a kunne na, Niimatullah!!cikin sauri na amsa masa  saboda na kosa ya sake ni, cikin raunananniyar murya yake min magana.

xaki taimaki mijinki?? da sauri na dago ina ware idanu,  wane irin taimako kuma, dama ana taimakon dattijo kamarka? saurin rufe bakina yayi, daga yau na hana ki fadar dattijon nan, ki rika kirana da babynki. xaro idanu nayi kaine babyn nawa?? kafe ni yayi da ido eh mana wata rana har wanka da tsarki sai kin yi min, xa kiga rigima kala-kala a dakin mu.

tabe baki nayi Allah ya sauwake nayi maka wanka tabdi, cigaba da kokarin guduwa nayi shi kuwa ya rike ni gam,  yaki sakina kuka na fara yi masa ka sake ni ko nayi maka ihu na kira innata.

tsare ni yayi da kallo kira innar mana ai kowa ya shaida ke matata ce, ko ta ganni babu abinda xata ce.

bata fuska nayi xan yi kuka ni fa Allah ka sake ni, sake riko ni yayi tare da kallon fuskata.

ina jin wani abu a raina idan naga kin turo min wannan kyakkyawan bakin naki, sai naji kamar na shanye su, xaro idanu nayi ka shanye fa kace Allah ya sauwake maka,  ka cika ni na tafi fitsari nake ji, ki tsaya mana na fada miki irin taimakon da xaki yi min.

sunkuyar da kaina nayi kasa, ina jinka fada min dan Allah na gaji.

yan uwa a yi hakuri da typing kadan matsalar ba daga ni take ba, wayaa ce mai matsala idan nayi da yawa sai tayi deleting typing din gaba daya

MATAR DATTIJO CompleteWhere stories live. Discover now