MATAR DATTIJO page 54

1K 38 0
                                    

💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
           *Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

*Follow me on instagram @Jeeddahtijjani*

54

Dattijo ne xaune a harabar gidansa yana hutawa, sanye yake da farar jallabiya hannun shi rike da news paper yana karantawa, gaba daya hankalin shi a kan takardar da yake dabawa yake, cikin nutsuwa yayansa suka karaso wajen da yake xaune, cike da ladabi suka tsugunnah sannu da hutawa daddy cikin sakin fuska ya amsa musu, sannan suka nemi kusa da shi suka xauna, sun dan taba hira tare da dan barkwanci sannan munir ya fara yi masa magana.

Dama daddy xuwa muka yi mu kara baka hakuri a kan abinda mama take maka, mun san kana hakuri da halayenta amma ka kara yi, saboda hannunka baya rubewa ka yar daddy, sannan kuma idan tana tare da kai da Aunty tana ganin yadda ku ke mu'amala da kyakkyawar dabi'a ina ganin xata canja wasu dabi'un nata.

A hankali ya dago ya dubi yaran nasa har cikin ransa yake jin kalaman sa na ratsa duk wani jini da tsoka na jikinsa, tabbas shi kansa yasan yayi sa'ar yara masu hankali da xurfin tunani, kuma xai so a ce da mahaifiyar su suke rayuwa amma halinta ya janyo ya rabu da ita, sauke ajiyar xuciya yayi sannan ya bashi amsa.

Tabbas dukkan abinda ku ka fada gaskiya ne, amma lamarin mahaifiyar ku yana bukatar dogon naxari ba abu ne da xa a yi shi da gaggawa ba, naji dadin wannan tunatarwar da ku ka yi min, Allah yayi muku albarka kuma xan duba wannan maganar taku da idon basira insha Allah, amsawa suka yi da ameen sannan suka mike, bin su yayi da kallo har suka shige bangaren su ba karamin tausayi suka bashi ba, amma yana ji a ransa baxai iya cigaba da rayuwar aure da mahaifiyar su ba.

Har ya mayar da hankali kan takardar yana karantawa yaji baxai iya cigaba da karatun ba, saboda tunani da tausayin yayansa, tashi yayi ya nufi wajen Niimatullah.

A kulle ya tarar da kofarta don haka yayi sauri ya tura don ya san bacci take yi indai yaji kofarta a kulle, saka kanshi yayi ya shiga dakin tare da sallama.

Ina jin maganar shi na narke a cikin bargo ina dan numfarfashi, saboda nasan matukar ya shigo ya tarar da ni a xaune tara min gajiya xai yi. Jin ban amsa sallamar bane yasa shi shigowa cikin bed room din, a cikin bargo ya iske ni ina ta faman numfarfashi, maimakon naga damuwa a ransa sai naga yana murmushi, bata rai nayi xan masa kuka.

Kana ganin ba nida lafiya shi ne xaka yi min dariya, karasowa yayi yana murmushi tare da jan kumatuna nasan abinda kike gudu fa amaryar dattijo shi ne xaki shirya min wannan law din ko? to ai na gane nufin ki. Langwabar da kai nayi tare da dora hannuna a jikinsa Allah da gaske nake bana jin dadi dattijona taba ka ji, hannunsa ya dora a wuyana ni ban ji komai ba Niimatullah kawai don kada ki kula dani ne, kuma dole a bani hakkina saboda yanzu ne lokacin da ya kamata mu ci amarcin mu tunda wannan jarababbiyar bata nan.

Kukan shagwaba na fara yi masa ni Allah baxan yarda ba, idan kuma kaje kayi abinda cikin ya xube ba ruwana, cike da xaulaya ya bani amsa to menene idan ya xube sai na kara yin wani tunda dama na farkon ma ni nayi abuna.

Tashi nayi xan gudu da sauri ya riko ni ya manna ni da kirjinsa, ina xaki je amaryar dattijo? Bata fuska nayi wani dakin xan tafi tunda nan ka takura min, murmushi yayi tare da rike hannuna haba Niimatullah me yasa har yanzu kika kasa sabawa da halin dattijon ki, ni fa haka Allah ya halicce ni da tsananin bukatar ki baxan iya rayuwa ba tare da soyayyar ki ba, hawaye na fara yi wlh yau a gajiye nake dattijona babu abinda xan iya yi, sumbatar goshina yayi tunda kin gaji na hakura amma fa ki sani bashi kika ci akwai ranar da sai kin biya gaba daya.

Da sauri na amsa da eh na yarda xan biya, cika ni yayi na koma na xauna wayar shi ce tayi ringing hannu yasa ya dakko yana dubawa ya hasko min kalli number wa kike gani? cikin sassanyar murya na amsa masa da number Aunty ce, ajiyeta yayi a gefe tare da cewa baxan duba ba don ni yanxu na kulle babin rayuwarta.

Rarrashin shi nayi a kan ya dauki wayar amma yaki dauka, sai da tayi masa missed calls sama da goma, tana sake kira na dauka ina yin sallama naji muryar namiji kuma da alama ya manyata, da sauri na mayar da wayar kunnensa cikin ladabi naji yayi sallama magana suka fara yi wani abin yana bada amsa wani kuma naji yayi shiru, bayan sun kammala ya fada masa cewa xai xo yanzu.

Bayan sun gama magana yake fada min cewa baban maman munir ne, yana min magana ne a kan abinda ya hada ni da maryam na fada masa yanxu xan je nayi masa bayani, ;amma wlh baxan dawo da ita ba saboda shi ma yasan halinta.

Lallaba shi na shiga yi don Allah kayi hakuri hubbyna ka dawo da ita dakinta ko yanxu ai ta gane kurenta idan har aka ce xa a yi muku sulhu kada ka vki amincewa saboda sulhu alkhairi ne, kuma na tabbatar da cewa baxa ta kara aikata kuskuren da tayi a baya ba.

Murmushi yayi kina bani mamaki Niimatullah ina rasa wace irin xuciya ce da ke, ke da xaki ce kada na dawo da ita amma ke kike bani hakurin na mayar da ita dakinta, lallai a gaishe ki amaryar dattijo.

Hular shi ya saka, tashi nayi xan masa rakiya ya dakatar da ni yace nayi xamana, sallama muka yi ya tafi addu'a na rika yi wa maryam Allah yasa ya mayar da ita, saboda ina son yayanta su cigaba da rayuwa da ita.

*follow me on wattpad @jeeddahtulkhaeer Tijj*

*jeeddahtulkhair😘*

MATAR DATTIJO CompleteWhere stories live. Discover now