MATAR DATTIJO page 20

1.7K 73 0
                                    

: 💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
          *Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*

*ina gaida ku yan group din matar DATTIJO 1,2,3 ina tare da ku kuma ina jin dadin comments dinku ana mugun tare, masoya DATTIJO kwalelanku😜*

20

A soron na barshi
ya fi kusan minti talatin yana kuka cikin kukan yake kiran sunana, Niimatullah ki tausayawa rayuwata ki aure ni, ki tuna irin yadda nake sonki da kaunar Ki,tun lokacin da na fara ganinki, kika shiga raina kin samu gurin da baxa ki taba fita ba har abada. ke ta daban ce Niimatullah, kina da wata baiwa wadda ba kowace mace Allah ya bawa ba, ina samun nutsuwa idan ina tare da ke,kada ki guje ni Niimatullah ki kusanta da ni, zan wadatar da murmushi a saman fuskar ki,zan yi kokarin wadata ki da jin dadi daga cikin nau’ikan ababen jin dadin rayuwar duniya. Ina tsanin sonki babyna baxan iya barin ki ba ya karasa maganar tare da fashewa da kuka mai tsanani.

cikin gida na shiga ina xuwa na fada gado ina kuka, ban san halin da xan tsinci kaina ba idan aka raba ni da shi, shi ne mutum na farko da ya fara koyar da ni soyayya, a Kullum burinsa ya tarairayi jaririyar xuciyata wacce bata san komai ba sai soyayyarsa da karfi na rika fadar hakan ina cigaba da kukana, innata ce ta shigo inda nake saboda taji sambatun da nake yi dafa kafadata tayi tana rarrashina, kiyi hakuri Niimatullah indai Alhaji rabonki ne xaki aure shi,mu dai fatan mu ya  yiwa tufka hanci wannan matar tasa ta daina xuwa tana ci mana mutunci, nasan Malam xai sakko saboda yana son abinda kike so, a ranar cikin damuwa na wuni.

A bangaren dattijo kuwa yana komawa ya tarar da gidansa ba kowa, kwafa yayi ya samu kujera ya xauna a falo yana jiran dawowar matarsa, tunanin Niimatullah ya shiga yi da yadda xai shawo kan baba ya kyale shi ya tare da matarsa, baya jin xai iya rabuwa da ita saboda duk wani farin cikinsa ya hango shi a tare da ita, yana cikin  tunanin yaji wasu xafafan hawaye sun xubo masa, hannu yasa ya share gani yayi an tsaya a kansa, a hankali ya dago ,matarsa ya gani tsaye tana yi masa wani kallo a fusace ya mike yana nuna ta da hannu, ji yayi bakinsa na rawa saboda takaicin da ya cika xuciyarsa kasa ce mata komai yayi.

cike da gadara take masa magana, naje na lalata auren yar iskar yarinyar da kake so, saboda baxan taba iya sharing dinka da wannan kaxamar yarinyar ba, kuma wlh ka sani na rika yi maka haka kenan Har abada ba kai ba kara aure, duk inda kaje neman aure sai na rika xuwa ina ci musu nutunci a haka har su yi xuciya a fasa auren, mutumin banxa Kawai mara alkawari, a fusace ya dubeta.

ni kike kira da mutumin banxa Hajiya Maryam? tsare shi tayi da ido tana harararsa na fada duk abinda xa kayi sai dai kayi, karya nayi maka ba mutumin banxan bane kana tsoho ka auro yar cikinka saboda son xuciya da kwadayi an girma ba a san an girma ba, lalata aure yanxu na fara idan xaka nemi yan mata dari ni kuma sai na lalata auren har sai ka hakura ka daina.

komawa yayi ya xauna saboda idan ya cigaba da tsayawa tsaf xai fadi wani bakin ciki ne ya cika xuciyarsa cike da fushi ya mayar mata da amsa wlh ba dan arxikin yayan da kika haifa ba da xamana ya kare da ke yau,a matsayina na uban yayanki kike kirana da mutumin banxa saboda ba ki da hankali, auren Niimatullah ne bakya so kuma kisa a ranki kamar amarya ta tare a dakinta ne, kuma ki shirya ganin wulakanci kala-kala Allah dai ya kawota da alkhairi, da sannu sai na ganar da ke kuskurenki sai kin yi nadamar kirana da mutumin banxa shashasha mara amfani, sai kin xama tamkar shara a gidan nan dama ba ki da wani amfani a wajena banda bata min rai babu abinda kike yi mahaukaciya kawai, yana gama fada mata ya wuce dakinsa.

Yana shiga daki ya jawo waya ya kira Niimatullah, ina kallon wayar na ringing na kyaleta, sai da ya kira ni wajen sau biyar sannan na dauka, ina jin yanayin yadda yake magana nasan yana cikin matsananciyar damuwa, mun kai kusan minti daya ba tare da mun cewa juna komai ba, nice nayi karfin halin kiran sunan shi.

Dattijona!! cike da damuwa ya amsa min da na'am my Niimatullah, cike da damuwa nake masa magana, idan har akwai wani abu da xan roka a wajenka bai wuce na rokeka a kan, ka amince mu kasance tare ba har abada, domin tabbatuwar mafarkin da ya jima yana bayyana  a cikin baccina, ina sonka amma dole na barka tunda iyayena sun hango min matsala a tare da Kai.

Cikin sanyin murya yake min magana yanxu baxa ki tausayawa mijinki ba niima, ina cikin damuwa ko abinci na kasa ci, yanxu babu taimakon da xaki neman mana a wajen baba ya taimaka ya kyale mu muyi rayuwar farin ciki da juna,shikenan duk ginin da muka yi a baya ya rushe my Niimatullah, ki duba halin da xan shiga ki tallafi rayuwata, ji nayi hawaye sun fara xubo min hannu nasa na goge.

ina sonka dattijona amma baxan iya aurenka ba saboda mugun halin matarka saurin dakatar da ni yayi, tsaya Niimatullah bana son kina kawo tunanin wannan matar a ranki, babu abinda ta isa ta hana game da auren mu rayuwa mai dadi xa kiyi da mijinki, ki tallafi rayuwata ki shawo min kan innah da baba su yarda da ni, a sanyaye na amsa da to xan yi insha Allah sallama muka yi da shi ya kashe wayar.
ina  ajiye wayar bai fi da minti biyu ba naji  shigowar message din shi, a hankali nasa hannu na bude.

*Ina fatan xuwan ranar da xan kasance shinfide a saman kafadun ki na kwana a cikin dakin Ki, na kasance a tallafe bisa hannuwan ki,wato ranar da xa a kirani da angon ki. Ki duba kaunar da nake miki ki shawo min kan baba, ina sonki ki huta abar alfaharina*

Ina gama karantawa naji wani hawaye ya xubo min na tabbatar da cewa mijina yana sona idan na bar shi ban yi masa adalci ba.

Wajen innata na koma fadawa nayi jikinta ina kuka, cike da tausayawa ta dube ni, me ke faruwa da ke Niimatullah? cikin kuka na amsa mata da dattijona innah kada ya mutu ta sanadina na samu alhaki, yana cikin damuwa yace na roke ku,  ku janye maganar nan dan Allah.

cikin kulawa inna ta dube ni tare da girgixa kanta, kiyi hakuri Niimatullah xan samu malam nayi masa magana nasan xai janye idan yaga halin da kuke ciki,ni kaina bana son auren nan ya tarwatse saboda Alhaji mutumin kirki ne Kuma tsakani da Allah yake sonki kiyi hakuri Insha Allah xai sakko,  rarrashina ta rika yi har sai da hankalina ya kwanta.
wayar da ke gefen mu ce tayi ringing, hannu innah tasa ta dauka,sallama tayi cikin kulawa aka amsa mata tare da cewa dan Allah ina neman Niimatullah ne, da sauri innah ta miko min wayar na kara a kunnena tare da yin sallama

muryar matar da take min gyaran jiki naji cikin ladabi na gaida ta, tambayata dalilin da yasa kwana biyu banxo makaranta ba ta fara yi, muryata na hardewa na bata amsa saboda bakin cikin da ke cike a raina, an fasa auren shi yasa na daina xuwa.

A raxane ta tambaye ni me kike fada min haka Niimatullah bana son shirme fa, ina innar ki?cikin kuka nace gata nan kusa da ni, da sauri tace min mika mata wayar xa mu yi magana.

cikin girmamawa take wa innah magana, sannu baba ya gida ya yara, nice matar da nake gyarawa Niimatullah jiki naga kwana biyu bata xo ba shi yasa na kira nasan jiki da jini, sai kuma yanxu da na tambayeta dalilin rashin xuwanta naji tana min wata magana wai an fasa auren nata menene gaskiyar abinda take fada min baba? kana ganin Innata xaka gane tana cikin damuwa don damuwar har a maganarta ta bayyana, bayani ta fara yi mata ba karya Niimatullah ta fada miki ba gaskiya ne abinda ta fada, cike da mamaki take tambayar innata, to menene dalilin hakan baba?

sauke numfashi Innah tayi mun fasa ne saboda muna ganin hakan shi ne abinda xai fi xama Alkhairi a gare mu da kuma ita, mijin Niimatullah yana sonta nasan kema kin san haka, amma kishiyarta ce ba tada kirki xuwanta biyu gidan nan tana ci mana mutunci har tana ikirarin xata hallaka Niimatullah wannan dalilin yasa muka fasa.

cikin nutsuwa malama ta fara yiwa Innah bayani, ina ganin ba haka ya kamata a yi ba baba, tufkar kawai xa a yi hanci, amma batun a fasa ma bai taso ba, saboda xa a cutar da xuciyoyi biyu da suka dade suna son juna, tunda matsalar nan ba daga wajen bawan Allahn take ba bai kamata a fasa ba, saboda idan aka fasa an ji tsoro kuma an bata damar ta cigaba da yin haka nan gaba, ita wacece da xata ce ita kadai xata rayu da mijinta,tunda Allah ya bashi dama kuma yana da ra'ayin kara aure dole yayi, baxai yiwu a ce duk gyaran da muka yi ya tashi a banxa ba baba, gobe insha Allah xan xo tare da Alhajin duk inda matsalar nan take sai an warwareta, godiya Innah tayi mata sannan suka yi sallama.

ba karamin dadi naji ba da jin kalaman malama nasan tana xuwa komai ya xo karshe insha Allah.

*jeeddahtulkhair😘*

MATAR DATTIJO CompleteDär berättelser lever. Upptäck nu