MATAR DATTIJO page 8

1.7K 77 0
                                    

💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
          *Adam*
*(Jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*

*dedicated to Aysha sani sagir*

8

kashe min idanu yayi tare da cewa, tausa nake so ki yi min yar amaryata, to cika ni xan yi maka, mike kafafun shi yayi yana cika ni na fita da gudu sai wajen innah a soro na sameta tana kadin lagwani, yadda ta ganni a guje yasa ta tsayar da abinda take yi, tambayata ta fara yi.

lafiya na ganki haka Niimatullah? kuka na fara yi mata, wallahi innah baxan sake xuwa wajen wannan mutumin ba Kullum naje sai..........kafin na karasa innah ta toshe bakina

kul na sake jin kin fadi sirrin mijinki, dukan kasa na rika yi da kafata ki daina cewa mijina, ni wallahi na fasa tunda abinda xai rika min kenan. A dai-dai lokacin da nake fada mata ya fito daga dakin ya same ni a soro, duk kunya ta kama shi,  kansa a sunkuye ya yiwa innah sallama.

Har ya kai bakin kofa na sake cewa innah kiyi masa fada ya daina yi min........ xan karasa kenan ta daki bakina me yasa bakya jin magana ne Niimatullah, ba nace miki ki daina fada min ba,shi kuwa gogan naku don kunya kamar ya nutse a kasa, magana innah ta fara yi masa.

kayi hakuri Alhaji har yanxu Niimatullah yarinya ce sai a hankali xata saba, kansa a kasa ya amsa mata da ba komai innah, shi yasa dama na dakatar da tarewar sai ta dada wayo. sallama yayi mata ya tafi.

yana tafiya na dubi innah, innata wai dame xan saba, naji kin fada masa kin ce ban saba ba? murmushi tayi da cin shinkafa mana, da ba likita yace ki rage cinta ba saboda basir? gyada kai nayi alamar eh, bayani ta cigaba da yi min

to shi kuma mijinki yana so ki rika ci shi yasa nace a hankali xaki saba, girgixa kaina nayi, au na gane innata.

karbar lagwanin nayi na fara tayata kadawa muna yi ina mata mitar dokar min bakin da tayi, hakuri ta rika bani saboda tasan rigimata xan iya kwana ina mata kuka.

shi kuwa Alhaji Sadeeq na komawa gida matarsa ta saka masa bala'i, kadan ka gani daga irin abinda nayi maka, saura ita kucakar yarinyar da ka auro, muddin ta shigo gidan nan xaman lafiyarka ya kare, daka mata tsawa yayi.

ki saurara na gaji da cin kashin da kike min, kin hanani hakkina kuma kin hana ni aure,so kike yi na lalace, na fara bin matan banxa? ki sani aure an riga da an daura shi sai dai ki rungumi kaddara.

bushewa tayi dariya, wannan kwailar da ka dakko yar cikinka,  ni baxa ta daga min hankali ba, yar shara da wanke-wankena xan mayar da ita sai me? kallon raini yake mata wannan yarinyar da kike gani ta fiki komai da komai, duk da cewa kin fita ilimi kin fita shekaru da wayewar rayuwa, amma kuma ta miki wayo domin ta fiki iya tarairayar miji, don haka kin ga nan gaba xata xame miki kadangaren bakin tulu.

shigewa daki yayi ya barta tana balbala masifa, yana shiga ya dauki waya ya dannawa Niimatullah kira.

sai da wayar ta dade tana ringing ina kallonta ban dauka ba, ya kira wajen sau uku innah ce ta dauki wayar da kanta ta manna min ita a kunnena.

Hello nace sannan ya fara magana, yau kin kunyata ni a gaban innah, Niimatullah ni fa mijinki ne duk abinda nayi miki babu haramci, turo baki nayi.

ni ina ruwana ko yanxu ka kara yi min abinda bana so sai na fadawa innata, haka kawai ina xaune lafiya xaka jawo min abin kunya nayi ciki.

murmushi yayi, har yanxu dai baxa ki daina wannan maganar ba ko Niimatullah, babu wani abin kunya da xa kiyi duk abinda ya faru tsakanin mu halal ne a musulunci.

sauke ajiyar xuciya nayi to ni na haramta ehe, dariya yayi xaki ga kin haramta idan kika shigo hannuna, baxan ma shigo ba gara ma ka sani.

kukan shagwaba ya shiga yi min a wayar wai naxo na taimaka masa, na kasa bawa kaina amsar irin taimakon da yake nufin nayi masa, don haka na kashe wayar gaba daya na kyale shi.



*Jeeddahtulkhair😘*

MATAR DATTIJO CompleteWhere stories live. Discover now