MATAR DATTIJO Page 13

1.7K 78 0
                                    

💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
          *Adam*
*(Jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*

*dedicated to Amina Bashir (maman siyama)*

13

Suna kammala wayar ya ja motar shi ya wuce gida, yana driving yana tuna irin hirar da suka yi da  Niimatullah, ba karamin shiga ransa tayi ba, ji yake kamar ya jawo lokacin da xata tare a gidan sa.

A bakin kofar parlour ya ci karo da matarsa xaune a kan kujera ta dora kafa daya kan daya, tana harare-harare tare da turo dan kwalinta gaban goshi, da sallama ya karaso wajenta wani mummunan kallo tayi masa tare da kawar da kanta gefe guda, cikin tausasa murya yake mata magana, sannu da gida maman munir a fusace ta amsa masa, kaine da sannu tunda kai ka dawo daga wajen kaxamar matarka wacce ilimin addini da na boko bai wadaceta ba, wallahi ina ganin kokarin ka da har kake iya kula wannan jakar da bata san kanta ba, ka xubar da ajinka da nawa, ka rasa wadda xaka hada ni kishi da ita sai yar matsiyata, wadda iyayenta ke rayuwar wahala, tunda aka haifi yarinyar nan nasan bata san menene dadin duniya ba saboda talauci, amma don ka raina min hankali xaka hada ni da ita salon ta shafa min kwarkwata da kudin cizo. tana gama magana ta cigaba da girgixa kafarta.

ji yayi xuciyarsa na tafasa kamar xata tsaga kirjinsa ta fito saboda irin maganganun da take fadawa wacce ba shi da tamkarta a rayuwarsa, cikin fushi ya mayar mata da martani.

kucaka, kuma kaxamar da kika raina kike ganinta a banxa ta fi min ke a yanxu domin a  inuwarta nake samun nishadi da jin dadin rayuwa, dadin da ban ji shi sama da shekaru talatin ba yanxu na same shi a wajen jaririyar yar da kika haifa, kin yi sake yar cikin ki ta kwace miki miji, domin da ke da babu duk daya na dauke ku a cikin gidan nan.

Baki ajiye komai ba sai girman kai da raina miji, da kwalliyar banxa amma ta bangaren ibada salam ba dadi, yana gama fada ya saki wani shu'umin murmushi.

zan baki shawara daya kije wajen Niimatullah ta koya miki iya xama da miji da tarairayarsa, kuma ki lallabata tayi miki addu'a Allah ya axurta ki da irin ni'imomi da baiwar da Allah yayi mata, domin bakin Niimatullah mai kyau ne ina da yaqinin addu'arta xata karbu saboda farantawa mijinta da take yi.

sake juyawa yayi ya kalleta, hannunta dafe da kirjinta ta rasa bakin magana, tunda na samu Niimatullah nasan menene dadin aure, ashe da duk hakuri nake ina rayuwa da dusar mace ban sani ba.

Hannu ta dora a ka ta fara rusa ihu tana ci masa mutunci tunda suke da shi bai taba tsayawa ya fada mata magana irin na yau ba, shi kuwa shigewa daki yayi saboda yasan ya gama munana mata, a falo ta kwana tana masifa ko bacci bata iya yi ba. kalmar da ya fada mata ita tafi tsaya mata a rai domin ta maimaita kalmar wajen sau goma, yanxu saboda wannan yar iskar yarinyar xaka rika kirana da dusa, Allah ya isa tsakanina da kai, kuka ta rika yi shi kuwa yayi kwanciyarsa bisa gado yasan baxa ta kara marmarin xagin Niimatullah a gabansa ba tunda ya yiwa tufkar hanci, ajiyar xuciya ya sauke sannan ya juya yayi kwanciyarsa.

washe gari da wuri na kammala shiryawa na gyarawa innah dakinta, saboda nasan dattijona yana kan hanyar xuwa ya tafi da ni wajen koyon gyaran jiki, kusa da innata na xauna ina jiran karasowar sa, horn din mota naji don haka na saka takalmana, sallama na yiwa innah sannan na fita.

tarar da shi nayi jingine da motarsa ya harde hannayens a kirjinsa, tunda na taho daga nesa yake sakar min wani kallo tare da yi min kyakkyawan murmushi, daga nesan na tsugunnah na gaida shi, cike da kulawa ya amsa min ,bude murfin motar yayi na shiga, sannan shi ma ya shigo, kafin ya ja motar mu tafi sai da ya kare min kallo yana min magana kasa-kasa wacce bana fahimtar abinda yake cewa, dago fuskata yayi yana min wani kallon da ke sanyaya min jikina, cike da kulawa yake min magana.

ki tsayar da hankali ki koyi yadda xaki tarairayi marainiyar xuciyar mijinki kin ji my Niima, gyada kai nayi kawai ba tare da nayi magana ba, sai da ya gama yi min nasiha sannan muka dau hanya.

muna isa ya juyo ya dube ni har mun xo babyna, sannu da driving nayi masa sannan ya xagayo ya bude min kofa, hannuna ya rike muka shiga har Office din matar da xata koyar da ni, a xaune muka sameta tana cike wasu forms, cikin girmamawa ta gaida dattijona, hannu biyu ta karbe mu, cike da kulawa ya nuna ni,wannan sabuwar amaryata ce, an daura min aure da ita amma bata tare ba, don haka ina so a koya mata komai kafin lokacin da xata je gidana, a koya mata da kyau yadda xata kware a komai fiye da macen da ta dade a gidan miji, kuma special class nake so a sakata, ina ganin xata fi sakewa idan bata ganin idon jama'a.

cikin  sakin fuska ta bashi amsa, lallai Alhaji kana so amaryar nan taka ta kwace gida tunda ka kawo ta nan, murmushi yayi ba tare da yace komai ba.

kada ka damu Alhaji xaka ga yadda xata dawo wallahi komai nata sai ya canja, har sai ka dawo kayi min kyauta ta musamman saboda yadda xan kula maka da amaryarka, dan wasa da dariya suka yi ni kuwa ina gefe ina sake-sake a xuciyata, ita kuwa wannan matar me xata koya min haka da har xata canja ni??

kudi mai yawa ya xaro ya bata sannan ya mika mata form din don yin submiting, tashi yayi xai tafi karasowa yayi wajena ya rike hannuna ya kai ni kusa da ita.

ga amanata nan a kula min da ita, sumbatar goshina yayi sannan ya tafi da niyyar idan an tashi xai dawo ya dauke ni.

MATAR DATTIJO CompleteWhere stories live. Discover now