MATAR DATTIJO page 6

1.7K 88 1
                                    


*MATAR DATTIJO* 💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
         *Adam* *(Jeeddahtulkhair)*

*dedicated to Aysha sabo Abdullahi*

6

Da sallama na shiga dakin tarar da shi nayi xaune ya tsurawa kofar da nake shigowa ido, ina tafe ina tuntube saboda jarababben kallon da ya takura min da shi.

har kasa na tsugunnah na gaida shi, cikin sakin fuska ya amsa min, gefe na samu na xauna, matsowa yayi daf da ni, ya dan riko hannuna saurin janye hannun nayi tare da matsawa gefe, cikin rashin kunya nake masa magana.

"me yasa xaka taba ni sai ka janyo min nayi cikin shege" saurin toshe min baki yayi, ni mijinki ne idan na taba ki ba komai, kuma wai wa ma ya gaya miki idan na taba miki hannu xaki samu ciki? turo baki nayi,  innata ce tace kada na bari wani namiji ya taba min hannuna ana yin ciki.

murmushi yayi tare da cewa wannan shirmen naki yana burge ni Niimatullah, harararshi nayi nice ma nake yin shirmen ko? tashi nayi xan bar dakin kamo ni yayi ya xaunar da ni yana sumbatata.

kwala ihu nayi ka sake ni sai ka janyo nayi cikin shege ko? kafe ni yayi da manyan idanunsa, kada na sake jin kalmar nan a bakin ki indai ni ne xan miki ciki, to ba shege bane da uban sa kuma nine uban nasa, don haka kada na sake jin kin ambaci shege a nan.

gyada kaina nayi alamar eh, sake matsawa nayi daga gare shi, cikin shagwaba da narkar da murya yake magana.

me yasa kike guduna *MATAR DATTIJO* ko har yanxu babu soyayyata a ranki, a'a nace masa a takaice.

Bayan mun gama gaisawa ya miko min wrippers na dari biyu, karbi wannan ki siya duk abinda kike bukata, makale kafada nayi cikin shagwaba nace ka barshi ba abinda nake bukata komai innah da baba suna yi min, ajiye min yayi tare da cewa yanxu nauyin ki ya bar kan baba ya koma kaina don haka ya xama wajibi a gareki ki karba.

fita yayi ya bar dakin ni kuma na bishi a baya, har kasa ya tsugunna ya yiwa innah sallama sannan ya tafi.

jingina kaina nayi kan gwiwar innah ina mata magana
innata haka kawai sai wannan Dattijo ya rike min hannu, Allah yasa dai ba nida ciki, bina tayi da kallo ta rasa bakin magana, mikewa nayi ina duba cikina duba min innah ko na samu ciki har sai da guntun hawaye ya fito min.

ganin na tayar da hankalina ne yasa ta bani amsa wannan mijinki ne ko ya taba ki ba komai, wani namijin ne daban aka hana ya taba ki kin ji ko?

to nace amma xuciyata bata gama amincewa da amsar da ta bani ba, ko da naje islamiyya sai da na tambayi kawata ita ma irin amsar innah ta bani, kasancewar ta fini wayo da shekaru.

A kan hanya wata mota ta Parker a gaban mu wasu fararen mata ne guda biyu suka fito daga cikin motar, shan gaban mu suka yi tare da cewa wacece Niimatullah??

jikina na 6ari na amsa da gani nan, jawo ni daya daga cikin matan tayi ta shiga duba ni sama da kasa, daga karshe ta bushe da wata dariya, dayar ce tayi magana.

Tabdi Gaskiya dadyn munir ya raina miki hankali, ya rasa wacce xai auro miki a matsayin kishiya sai wannan kwailar kaxama da ita, dubeta fa ko nonon arxiki ba tada shi, sake bushewa da dariya suka yi suka tafa, dayar ce ta tabe baki tace.

nima dai haka na gani me xai yi da wannan yar tayin yarinyar, ga ta da gani ko tsaftar arxiki bata isheta ba, amma dai tana da kyau ba laifi.

Haka suka gama ci min fuska tsaf sannan suka sake ni suka shige mota suka tafi, kuka na fara yi abokan tafiyata sai tambayata suke a ina na samo wadannan marasa mutuncin matan, kasa basu amsa nayi saboda nima ban san su ba ban taba ganin kalar su ba.

ina xuwa gida na fadawa innata abinda matan suka yi min, fargaba ce ta kama innah saboda tasan babu mai yin wannan aikin idan ba matar Alhaji sadeeq ba, rarrashina ta shiga yi.

kiyi hakuri Niimatullah kada kisa damuwa a ranki, Insha Allah sai kin xamewa matar nan dan hakin da ka raina.


MATAR DATTIJO CompleteWhere stories live. Discover now