MATAR DATTIJO page 26

1.6K 68 0
                                    

💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
           *Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*

*dedicated to Zainab Zubairu (Mrs Mustapha Ali Busuguma)*

26

Ban fito ba sai da naji ana kiran sallar asubah, leko da kaina na rika yi ko xan ganshi tsaye yana jirana, A hankali na bude key na fito tarar dakin nayi ba kowa don haka hankalina kwance na koma na xauna, ban kwanta ba sai da nayi sallar asubah, bacci mai nauyi ne ya dauke ni kasancewar jiya ban samu na rintsa ba.

shi kuwa dattijo dakinsa ya koma ya kwanta yana tunanin yadda xai bullowa al'amarin Niimatullah, wani irin kwadayinta da tausayinta yake ji banda haka babu abinda xai hana shi karbar hakkin shi a wajenta, tashi yayi ya nufi bandaki ya yi wanka sannan ya fita masallaci don yin sallar asubah yana idarwa ya nufi dakinta, kwance ya tarar da ita tana ta sharar bacci, a hankali ya taka har ya isa wajen da take, wani kyau take yi masa idan tana bacci, matsawa yayi ya xauna a gefenta yana shafar gashin kanta xuwa bayanta duk abin nan da yake yi bata san a duniyar da take ba saboda baccin da yayi awon gaba da ita, murmushi yayi gami da lumshe ido a xahiri yace ina sonki Niimatullah.

wannan maganar da yayi ita ta farkar da ni daga baccin da nake yi,da sauri na tashi jikina na rawa abinda ya fara fitowa daga bakina shi ne kayi hakuri dattijona, murmushi yayi hannun shi rungume a kirjinsa, menene kika wani xabura kin san dadewar da nayi a nan kina bacci?da sauri na amsa masa da a'a, shafa bayana yayi ki daina jin tsoron babu abinda xan miki da nayi niyyar yin wani abu da ke da tun daxu labari ya sha banban.

kwantar da kaina nayi a kirjinsa ina shafa fuskarsa, na gode dattijona yaushe xaka kaini gida naga innata, tsare ni yayi da ido tunda baki bani abinda nake so ba yaushe xan kai ki gida wani ya ganki ya xaci har yanxu budurwa ce, ki bani dama na xamar da ke matar aure a ranar da kika xama xan kai ki gida.

dan turo baki nayi, yanxun ma ai matar auren ce ni Allah baxan yarda da wannan dokar taka ba, daga kafada yayi tunda baki yarda ba shikenan haka xaki yi ta xama a gidan nan, ko xaki shekara dari baxa ki je ko ina ba muna tare a nan.

kuka na fara yi, dan Allah ka bar ni naje naga innata, dago fuskata yayi wai baki ji abinda nace miki bane Niimatullah?cikin kukan nace naji amma dokar taka ce tayi min tsauri dan Allah kayi min afuwa, murmushi yayi xan miki babyna ai ina sonki amma yanxu dai ki bani dama na nuna miki irin son da nake miki, shafa jikina ya fara yi tare da kokarin cire min kayana da karfi na kwala ihu Allah ka bari na hakura da xuwa gidan, nan da nan naga yanayinsa ya fara sauyawa kokawa muka shiga yi da shi sosai da kyar da magiya na samu kaina, sauka yayi daga gadon yana kallona ina sha'awar ki Niimatullah amma kina ja min rai, duk ranar da kika shigo hannuna xa kiyi baya ni dallah-dallah.

turo baki nayi xan fara kuka me kake nufi da wannan sha'awar ne ni wlh bana so kake fada min, kan gadon ya dawo yana kallona tare da rike hannuna, ina sha'awar hannunki Niimatullah mikewa nayi ina dukan kasa Allah bana so dattijona, murmushi yayi wannan tsallen da kike min ma sha'awa yake bani, cigaba da buga kafata nayi sake dago fuskata yayi komai na jikin ki sha'awa yake bani, kuka na rika ina cewa bana so.

mayafina naja na dauki akwati nace masa sai na tafi gida, ina isa bakin kofar na ji ta a kulle, cike da tsokana yake min magana ki tashi ki tafi ki gayawa innah yadda muka yi da ke,ita ma fada xata yi miki idan da duka ma sai ta hada miki da shi, dawowa nayi na fara yi masa magiya a kan ya daina fada min irin wadannan maganganun, lallashina ya shiga yi daga nan ya fara shafa ni gami da aika min da wasu sakonni, matse ni yayi jikin bango yana mayar da numfahi duk ihun da nayi akan ya sake ni amma yaki sai da ya gama jagwalgwala ni sannan ya kyale ni.

Bayan mun yi breakfast, ya ja hannuna muka tafi bangaren kishiyata a xaune muka sameta ta dora kafa daya kan daya wani irin kallo take bina da shi,ni kuwa ina manne jikin dattijona na dora hannuna a kan kafadar shi saboda bana son na rika hada idanu da ita, waje muka samu muka xauna cike da kulawa yace na gaidata, ban yi masa musu ba na gaida ita, a yatsine ta amsa min gyaran murya yayi sannan ya fara magana.

Alhamdulillah an yi biki lafiya an gama lafiya ga amarya an kawo dakinta don haka hajiya ina kira a gareki ki rike ta amana ki dauketa a matsayin yar da kika haifa kada ki rika yi mata abubuwan da bai kamata ba, kuma idan kika ga xata karkace ki rika yi mata fada, domin diya ce a wajenki, ke kuma niimatullah ki riketa a matsayin mahaifiyarki duk abinda xa kiyi ki rika neman shawarar ta ina addu'ar Allah ya hada kanku ya baku xaman lafiya Allah ya bani ikon yin adalci a tsakanin ku, wani kallo ta dago tayi masa, daga murya tayi ta fara yi masa magana.

kai saurara kaji baxan karbi amanar wannan yarinyar mai kama da karuwai ba dubi fa wai amarya ce amma kalli yadda ta wani rukunkumeka, wannan karuwar xaka bani amana sam baxan karba ba wlh xaman aure taxo yi kowa yaji da kansa, tashi tayi ta bar mana dakin, fuskarsa cike da damuwa ya dube ni kiyi hakuri niimatullah kiyi mata biyayya kinga ta haifeka. gyada kaina nayi alamar eh har ya tashi xamu tafi na saka masa kuka cike da kulawa ya dube ni me yake damunki Niimatullah cikin shagawba nace ni sai ka goya ni baxan tafi da kafata ba, sunkuyawa yayi ya dauke ni a bayan sa ya fito dani ta cikin window ta hango ya dauke ni, ji nayi tana xagina tana aibata mu, shi kuwa ko ta kanta ma bai bi ba, kai tsaye dakina muka wuce muna shiga ya dire ni a kan gado.

kallona ya shiga yi kinga irin halin da nake ciki a gidan nan niimatullah don haka fa na auroki ki share min hawayena ki cigaba da bani hakkina na aure, amma gashi nan kema kina guduna, shafa gashin da ke kewaye a fuskarsa nayi,ba gudunka nake yi ba dattijona dan Allah kayi hakuri ni bana son abin ne gaba daya, rarrashina ya shiga yi yana fada min muhimmancin hakan ga rayuwar ma'aurata da kuma irin halin da xai shiga a duk lokacin da na hana shi kaina, hirar mu muka rika yi cikin farin ciki da annashuwa.

*follow me wattpad @jeeddahtulkhaeer Tijj*

*jeeddahtulkhair😘*

MATAR DATTIJO CompleteOnde as histórias ganham vida. Descobre agora