MATAR DATTIJO page 35

1.5K 50 0
                                    

💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
         *Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*

*Gaisuwa ta musamman gare ku masoyana*
fareeda sulaiman(yar pot)
Sakinatu Umar (Ummu Abdurrahman )
maman sharifa
Amsopy
Dija Misku
momyn farhan
Khadijah ummi
Hamamatu khalil (maman jadda)
maman Namanxo
jannah
maman abulkairi
haleema Abba
hajara chuss
rahma haruna
ummu Mimi
rukaiya Ali
maman rai'z
Hauwa'u usman
Zainab A Adam
Maman muneefa
Haulat Alqaseem
Hassana tafarki
Aisa
Maman Mubeenah
Autar kibiya
Bilkisu M Ladan
Asma'u (asmaa)
Hauwa Ali
mmn Abdussamad
Haou Douang
Hauwa sadi Ibrahim
Aisha usman
Rukaiya Ibrahim Auta
Asmau Dauda

35

Tun a daren na fara xaben kayan da xan saka, dattijona ya lura da irin rawar kafar da nake yi kallona kawai yake yana murmushi tare da xaulayata, baxan dai bari ki kwana ba kina xuwa xaki dawo, marairacewa nayi na fara rokonsa dan Allah ka bar ni na kwana dattijona kaga na dade rabona da ganin innata, murmushi yayi tare da shafa fuskarsa kina tunanin xan iya hakuri da ke ki tafi wani wajen ki kwana?sam baxan taba iya haka ba sai dai idan nima gidan innar xan xo mu kwana daki daya, xaro ido nayi tare da cewa daki daya fa kace Allah sai dai ka kwana a soro, dariya yayi tunda na aure ki ai na wuce kwanan soro, sai dai innah ta bamu gadonta mu kwana, tabe baki nayi tare da cewa Allah ya kiyaye ni baxa a yi wannan rashin kunyar da ni ba. lumshe idanu yayi yana murmushi tunda baxa a yi haka da ke ba, nima baxan bari ki kwana ba, idan naga dama ma sai nace an fasa tafiyar don kin san bana son missing din ki, kuka na fara yi ina shure-shuren kafa kayi Hakuri dattijona kada kace an fasa, murmushi yayi to shikenan na hakura amaryar dattijo.

washe gari da safe da wuri na tashi na kintsa nayi wanka, tashin dattijona nayi na raka shi bandaki shi ma yayi wankan, wani tsadadden less na sanya sky blue dinkin kayan yayi kyau, sannan na dauki mayafi sky blue shi ma na saka, kayan sun karbe ni kwarai da gaske, shi kuma dattijona fararen kaya ya saka, hannuna ya rike yana kallona yau dai Allah ya nufa xa a je a ga innah, sunkuyar da kaina nayi wani nauyin sa ne ya kama ni, rungume ni yayi yana sumbatar goshina kin yi kyau amaryata kamar yau aka kawo min ke daki, Kullum kara haske kike kina dada kyau, murmushi kawai nake yi na kasa bashi amsa.

Jan hannuna yayi muka fita bakin mota, tarar da Hajiya maryam muka yi tare da wata kawarta suna hira,suna ganin mu suka tsaya suka rike baki, gulmar suka far y ni da dattijo, ina ganin irin kallon da suke mana na kara narkewa a jikinsa ina yi masa shagwaba, shi kuwa sai rarrashina yake bai ma lura da su ba, cike da gadara kawar Hajiya maryam ta fara magana.

Yanxu Hajiya haka xaki xuba ido ana yi miki bariki a gida, wallahi ilimin ki bai miki amfani ba da har kika tsayawa wannan kucakar xata kwace miki miji, kin yi sake wlh kin bani kunya, wannan idan gidana taxo ko sati daya baxa tayi ba xata kama gabanta.

sauke ajiyar xuciya tayi sannan ta mayar mata da amsa, ai tsayawa nayi naga gudun ruwan su daga ita har shi din kallon su nake, amma wlh wata uku na basu, baxa ma tasan lokacin da xata ji kafarta a waje ba, hannu ta mika mata suka tafa, ni kuwa wani kallon raini nayi musu na watsar da su.

maganar da tayi ne yasa ya gane suna tsaye, juyowa yayi ya kalle su yayi murmushi sannan yaja hannuna muka shiga mota, kullo kofar yayi sannan ya dube ni cike da tausayawa yake min magana, kiyi hakuri da dukkan abinda maman munir xata yi miki, Allah yana tare da ke murmushi nayi tare da shafa fuskarsa ni dama ban damu ba babyna tunda na aure ka nasan xan hadu da wannan kalubalen tunda kana sona ba ni da wata damuwa, da a ce matsalar daga wajenka take da shi ne hankalina xai tashi,amma tunda kana son farin cikina taje tayi taga xata iya ne.

rungume ni yayi sosai ina sonki Niimatullahina saboda nutsuwar ki da kaifin hankalin ki, xan cigaba da rike ki amana insha Allah.

key ya yiwa motar muka kama hanyar tafiya gidan innah, kafin mu je sai da muka biya super market muka yi musu siyayya masu yawa, tun daga kan kayan abinci har xuwa kayan amfani na yau da kullum, xan iya cewa yar karamar gara muka hada musu.

A bakin kofar gidan muka yi parking, na kosa dattijona ya bude min kofa na shiga gida naga innata, cike da kulawa ya dube ni to amaryar dattijo mun xo ina so na dauke ki a bayana na shigar da ke har dakin innah saboda tasan na rike mata amanar jikarta, makale kafada nayi cikin shagwaba nace Allah baxai yiwu ba sai kace wata yar baby, jan kumatuna yayi yana murmushi to da mecece idan ba babyn ba, ko gani kike kin girma amaryar dattijo?da sauri nace eh mana Allah na girma, murmushi yayi to shikenan ni dai ban yarda ba tunda nasan har yanxu ke yarinya ce, kuma nasan kafin na matsa daga wajen nan ma xaki gwada min kuruciya.

bude min kofar yayi muka fito tare, ban tsaya mun jera ba na kwasa da gudu na shiga gida, bina yayi da kallo yana murmushi,a daki na tarar da innahtana kadin lagwani, da sauri na fada kanta ina murna, cikin fara'a ta dube ni.

sannu da xuwa Niimatullah ashe kina tafe, yau dama har mafarkin ki nayi, cike da shagwaba na dube ta nayi kewarki innata na xaci kullum xaki rika xuwa kina ganina Allah yanxu bakya sona kamar da.

murmushi tayi ba haka bane Niimatullah idan ina xuwa kullum ai akwai matsala, kuma ina so ki saba da xaman auren shi yasa amma ai ina sonki yar jikallena, tashi nayi na cire mayafina na shiga dudduba dakin.

wlh innah komai ya canja min a gidan nan ji nake kamar na shekara daya rabona da gidan, ba ki da wani dan kayan dadi ki bani.

dariya tayi min banda rigimar ki Niimatullah me xaki samu a dakin tsohuwa, shagwaba na fara yi ni Allah ki bani abu naci innata, goro ta miko min karbi kici tunda kwadayi kike ji, ko dai kin samu karuwa ne Niimatullah?da sauri na dubeta wace irin karuwa innah? murmushi tayi ciki mana, langwabar da kaina nayi ni ba ni da komai innata.

wai ina baba ne ban ji motsinsa ba, tashi innah tayi yana dakinsa yana bacci kuma kin san dokarsa ce idan yana bacci ba a tashinsa, gyada kaina nayi tare da cewa haka ne na sani kawai dama na tambaya ne.

jakata na jawo na shiga fito da kudin da dattijo ya bani, yace na bawa su innah godiya ta rika yi tana sa mana albarka, tambayata tayi ina mijin naki yake, ko ba shi ya kawo ki ba? sai a lokacin na tuna da na bar shi a waje, da sauri na amsa mata subhanallah na manta na bar shi a waje, salati innah ta fara yi oh!! ni Allah ya shirye ki Niimatullah.

A jikin mota na same shi ya rungume hannun shi a kirjin shi, murmushi yayi min tare da girgixa kan shi,wato an manta da ni an tafi wajen innah ko? sunkuyar da kaina nayi tare da riko hannun shi kayi hakuri ban manta da kai ba, innata tace ka shigo ku gaisa, tare muka shiga da shi har cikin gida, bayan sun gaisa ta fara yi masa godiyar abin arxikin da yayi musu.

kansa a kasa ya bata amsa babu komai innah ai ni da ku mun xama daya, yara yasa suka rika shigo da kayan da ya siyo musu, nan ma dai godiyar innah tayi masa sannan ya tashi ya tafi.

binsa nayi don yi masa sallama a soro muka tsaya, cike da marairaicewa ya dube ni, bana son barin ki my Niimatullah ji nake kamar na dauke ki mu tafi tare, rungumo ni yayi yana sumbatata ki kula min da kan ki matata, anjima da misalin karfe biyar xan xo mu tafi gida,  sallama muka yi sannan ya wuce ya tafi.

wajen innah na koma dora kaina nayi a cinyarta muka fara hira, cike da kulawa ta dube ni gaskiya mijin ki na sonki Niimatullah, ki cigaba da yi masa biyayya dukkan abinda yake so kiyi masa domin aljannar ki a karkashin sa take.

cike da shagwaba nace ina masa komai innata,amma matarsa ce ta takura min ran nan har marina tayi, sannan yau da muka fito ta fada min wai wata uku ta bani daga haka xata fitar da ni, ni na fara jin tsoro lamarinta innata, na karasa maganar ina kuka.

rarrashina ta shiga yi Allah yana tare da ke Niimatullah babu abinda ta isa tayi miki, fatana dai kawai ki dage da addu'a da kiyamullaili kada ki rika sake da karatun kur'ani Allah xai baki kariya daga dukkan sharrinta, ai babu wani abu da ya fi karfin Allah.

maganganun innah sun kwantar min da hankali sosai, don haka cikin farin ciki muka cigaba da hira.

*follow me on wattpad @jeeddahtulkhaeer Tijj*

*jeeddahtulkhair😘*

MATAR DATTIJO CompleteWhere stories live. Discover now