MATAR DATTIJO page 46

1K 40 0
                                    

💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
           *Adam*
*(Jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*

*Gaskiya na kusa yin xuciya na daina typing kullum, sai na takarkare nayi rubutu hannuna ya rika xafi amma dan comments din da xa a yi min naji sanyi a raina ya gagara tunda abin haka ne nima xan fara jan aji
na daina yi kullum

46

Jikinsa ba karfi yaja motar ya tafi tare da tunanin irin hukuncin da su innah xasu yanke a kan auren su da Niimatullah, shi kanshi ya san ba a kyautawa Niimatullah ba, ana yi mata abubuwan da basu kamata ba saboda ana shiga rayuwarta, a xuciyarsa ya fara shawarar raba musu gida da Hajiya Maryam sai dai hakan ba mai yiwu wa bane saboda yana son kan yayansa ya hadu a nan gaba, idan ya raba gida da yayan maryam da na Niimatullah baxa su samu wata shakuwa ba,wannan dalilin yasa xai bar Niimatullah ta cigaba da xama a gidan da yake.

Kai tsaye office ya wuce don baya son ya koma gida yaga babu Niimatullah, gidan duhu xai yi masa, yana shiga ya xauna a kujera tunani ne ya mamaye xuciyarsa bai san ta ina xai fara magance wannan matsalar da take tunkaro shi ba, kwantar da kanshi yayi jikin table ya cigaba da aikin tunani.

*******

Baba na dawowa innah ta zayyane masa irin halin kunci da damuwar da nake ciki, da kuma baraxanar da Hajiya Maryam ke min a kan xata raba ni da duniya, kama baki yayi ya rasa bakin magana saboda abin ya daure masa kai, ajiyar xuciya yayi sannan ya fara magana cike da tausayawa yake kallona.

Lallai wannan aure ya cancanci a raba shi saboda tun kafin a yi auren nan take wannan furucin Allah bai sa ta cimma burinta ba, yanxu kuma ta dawo tana yi tunda ta kudurce a ranta sai taga bayan ki babu abinda xai hana ta yin hakan, to kinga tun kafin tayi aika-aika gara a yi miki gata a kashe auren ko me kika ce?kaina a sunkuye ban bashi amsa ba saboda ban san me xan ce masa ba, ina son mijina kuma ina tsoron Hajiya maryan ban san wane xabi xan dauka ba.

Shirun da yaji nayi shi yasa ya kara maimaita tambayar da yayi min, kin yi shiru Niimatullah? Kaina a sunkuye na amsa da duk hukuncin da ku ka yanke na karba baba,Allah ya xaba mana abinda ya fi alkhairi amsawa suka yi da ameen.

Tashi nayi na nufi soro hannuna rike da wayar innata number dattijo na fara laluba,kira daya nayi masa ya daga tare da cewa na kashe xai kira, ban fi second biyu da kashewa ba ya kira gaisawa muka fara yi cikin raunananniyar murya na fara magana da shi, dattijona kayi hakuri a yau nake son yin ban kwana da kai saboda innah da baba sun tabbatar min da cewa auren mu baxai yiwu ba dole na hakura da kai, yanzu haka na fara bawa xuciyata hakuri a kan rashin ka da xan yi, na karasa maganar ina kuka.

Cikin rawar murya ya fara min magana me kike fada min haka Niimatullah kina nufin na rabu da ke wannan magana ce wacce baxa ta taba yiwuwa ba,na dade ina fada miki rayuwata baxa ta taba tafiya daidai ba matukar bana tare da ke, don haka maganar rabuwa ma ki janyeta baxan taba sakinki ba ko me xa a yi min saboda ina sonki.

Kashe wayar yayi, duk kiran da nayi masa bai dauka ba, wannan rashin daukan wayar ba karamin damuwa ya saka ni ba, saboda ban san halin da ya shiga ba sanadin fada masa yadda muka yi da su innah.

Sunkuyawa nayi na sha kukana sannan na shiga gida saboda bana son nayi kuka a gaban su innah su gane cewa ina cikin damuwa, har yanxu dai tattaunawa suke yi a kan maganar komawata gidan dattijo, kuma suna nan a kan bakan su na aurena da dattijo ya kare, dakin baba na shige saboda idan na tsaya ina sauraren abinda suke fada xuciyata xata iya fashewa saboda baxa ta iya jurewa jin abinda suke fada ba.

Kiran wayar da ke hannuna aka yi ina dubawa naga dattijo ne ya kira a kasalance na dauka saboda ban san me xai fito daga bakinsa ba, cike da damuwa ya kira sunana tare da fadin kixo soro ina jiranki.

Jan kafa na rika yi har na isa soron saboda duk wata jijiya ta jikina a sanyaye take, tsaye na tarar da shi ya tsurawa kofar da nake shigowa ido muna hada ido naga hawaye na sauka a kan fuskar shi,da sauri naje na fada jikinshi ya rungume ni kamar xan tsaga jikin shi na shige, kuka muka rika yi gaba daya shaukin junanmu da soyayya sai ya tashi a lokacin ban taba jin ina son dattijo kamar yadda naji son shi ba yau, sai da muka yi kuka ya ishe mu sannan muka saki juna a hankali ya dago kaina yana dubana, yana hawaye yake min magana.

Me yasa a kullum kike son hukunta ni da rabuwa da ke, ko don na fada miki bana son kalmar shi yasa kullum take fitowa daga bakin ki, na dade ina fada miki baxan iya rabuwa da ke ba Niimatullah, matukar na rabu da ke rayuwata taxo karshe ban taba son wata mace kamar yadda na so ki ba, indai har kina sona son ba a iya baki ya tsaya ba ki bani hadin kai na kwatar mana yancin mu don mu cigaba da rayuwa har abada.

Share kwallar da ta cika idona nayi, cikin kuka na fara magana, wallahi ina sonka dattijona amma yanzu idan na bijirewa umarnin innah da baba a kan raba auren nan zasu tsangwame ni ne su ga kamar basu isa da ni ba.

Tallafo kaina yayi, matukar innah da baba sun san kina son mijinki baxa su tsane ki don kin koma dakina ba saboda sun san yadda so yake baxa su damu ba don kin nemi alfarmar cigaba da rayuwa da ni tunda sun riga sun san muna son junanmu.

ajiyar xuciya nayi ba tare da na amsa masa ba, kafe ni yayi da manyan idanunsa, idan baxa ki iya tunkarar su innah da wannan maganar ba ni xan je na warware dukkan abinda xai xo ya dame mu, halin maryam bai isa ya hana mu xaman aure ba,hawaye ya shiga share min sannan ya dago fuskata ya kalle ni...

Shiga ciki ki fadawa su innah xamu fita unguwa xuwa anjima xamu dawo, saboda muna cikin damuwa muna bukatar mu huta, xaro idanu nayi haba dattijona muna cikin wannan takunkumin xaka ce mu fita?.

Gyara tsayuwa yayi babu wani takunkumin da muke ciki ke matata ce ina da ikon tafiya da ke duk inda naga dama a fadin duniyar nan,don haka ki shiga ki shirya ki fito.cikin gida na shiga na tarar da su innah fada musu abinda dattijo yace nayi basu yi min musu ba na dauki mayafina na fita.

Rike hannuna yayi har sai da muka shiga mota cike da kulawa yake min magana, amma kin fadawa su innah ba yau xamu dawo ba ko? Turo baki nayi ni ai baka ce min kwana xa mu yi ba kawai kace na dakko mayafina.

Lumshe ido yayi to sati guda xa mu yi ina so na huta sosai na mance da wannan damuwar da nake ciki, bata fuska nayi xan yi kuka, haba dattijona ba fa haka muka yi da kai ba sai ka janyo innah tayi fushi da ni.

Jan kumatuna yayi ba fa wajen sabawa Allah kika tafi ba Niimatullah farantawa mijinki kika tafi yi,nasan ma innah baxa tayi fushi da ke saboda tasan duk inda kike kina tare da mijinki ne, yana gama fada ya yiwa motar key muka tafi.

*Follow me on wattpad @jeeddahtulkhaeer Tijj*

*Jeeddahtulkhair😘*

MATAR DATTIJO CompleteWhere stories live. Discover now