MATAR DATTIJO page 10

1.8K 85 0
                                    

MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
           *Adam*
*(Jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*
             
                    *معذرة🤦🏼‍♀*
*masu yi min magana ta private su ga kamar wulakanci ne yasa bana son amsawa wlh matsalar network ne maganarku na shigowa amma tawa bata tafiya dan Allah a yi min afuwa ina kaunar ku kamar yadda kuke kaunata*

10

Bakin wani hotel muka Parker leko da kanshi yayi inda na sunkuyar da kaina, to mun xo amaryata sai ki tashi mu shiga, cikin tsiwa nace wlh ba inda xan je har sai ka mayar da ni inda ka dakko ni idan ba haka ba kuma sai dai mu kwana a nan,  murmushi yayi tare da kanne ido daya, menene idan mun kwana a nan ni tayi min dai-dai kinga sai nayi abinda naga dama da matata babu mai sa min ido.

Hararar shi na shiga yi, to yi din wallahi xaka janyo a fasa auren nan kowa ya huta, murmushi yayi min auren nan fa a hannuna yake amma kullum sai ki rika cewa a fasa, to ni baxan taba sakin ki ba mutuwa ce xata raba mu, yana gama fada min ya bude motar ya fito,  leko da kan shi yayi ta window ki fito idan ba haka ba kuma na dauke ki cak na kai ki inda xamu je.

Harararshi na tsaya yi gami da jujjuya idanuna, bismillah dauke ni din idan tsayawa xan yi ina kallonka, dariya yayi min wai me yasa bakinki baya mutuwa ne Niimatullah gaki yar mitsitsiya sai tsiwar tsiya da rashin ta ido, tunda kika ce min bismillah xaki ga aikin bismillah, bude murfin motar yayi daukana yayi can cak,da kafarsa ya mayar da murfin motar ya rufe, kokawar kwatar kaina na fara yi, amma na kasa, sai da ya kaini har cikin dakin da xamu sauka, sannan ya ajiye ni kuka na rika yi masa ina magiyar ya mayar da ni gida.

kumatuna ya rike yana min murmushi yau ina tsiwar taki Niimatullah? cikin kuka nace masa na daina baxan kara yi maka ba kayi hakuri, rungumo ni yayi ya hada ni da kirjinsa kin tabbatar da cewa baxa ki sake yi min rashin kunya ba kuma baxa ki sake yi min tonon asiri ba? da sauri na daga kai nace masa eh, murmushi yayi tare da cewa yau ba a turo min da dan bakin nan ba ko don ba a gidan innah ake ba? shiru nayi masa cikin shagwaba nace masa ina jin kishiruwa.

kallona yayi ya tsare ni da ido ba daxu na baki ruwa kika sha ba, wannan ba na bayarwa bane idan kuma kika sha min sai kin biya ni, da sauri nace eh bani na sha idan naje gida xan debo maka wani a randar innah.

dariya yayi min wa ya gaya miki irin wannan biyan xaki min da jikinki xaki biya ni saurin dafe kirjina nayi, dama ana iya biyan ruwa da jiki? murmushi yayi tare da cewa kwarai kuwa idan kuma baki yarda ba gashi kisha.

girgixa kaina nayi ka barshi ni bana so Allah, shafa fuskata yayi, yi hakuri babyna ai baxan iya hana ki kisha ruwana ba, ko don alfarmar yayana da ke jikinki, saurin xare idanu nayi wane yayan naka kuma? nan da nan na mike tsaye ina duba kaina, wayyo na shiga uku me xan je gida na fadawa innata, dama ta dade da fada min indai na bari aka taba ni xan iya samun ciki, watakila ma cikin yan biyar ne dani tunda kusan sau biyar kana taba ni.

Hankalina ya tashi sosai sai ihu nake shi kuwa yana gefe yana tuntsura min dariya, sai da nayi kukana na koshi sannan ya kira sunana cikin salon soyayya, Niimatullah a hankali na dago jajayen idanuna da suka sha kuka na dube shi, ki daina damuwa yanxu ba ki da komai a cikin ki sai nan gaba xaki samu ciki ki haifo min yaya kyawawa kamar ki, kin ji ko yar yarinya ta. cikin kuka nace masa to naji tashi mu tafi gida kada innata taga na dade, dagowa yayi daga kwanciyar da yayi,  mu tashi mu tafi fa kika ce? baki ga har kwanciya nayi ba to ina nufin tafiya ba yanxu ba har sai na koya miki hankali kin daina wannan surutun da kike yi, sai mun kwana daya a nan, da sauri na dago na kalle shi kayi hajuri nayi hankali wlh baxan sake gayawa inna ba, murmushi yayi naji kin yi hankali amma ni kudin kwana daya na biya mana baxan tafi ba sai na ci kudina don baxan yi asara ba, yana gama fada ya mayar da kansa gefe

kuka na fara yi Allah baxan kwana a wajen nan ba sai na tafi gida, bakin kofa na nufa na fara jijjiga kofar ina kokarin budewa amma na kasa saboda key din na aljihunsa, dawowa nayi na fara yi masa magiya, dan Allah kaxo ka bude min kaga magariba ta kusa.

lumshe idanunsa yayi ya dube ni, idan kina so na mayar da ke gida sai kin taimaka min, da sauri na karasa wajensa fada min taimakon da kake so nayi maka, xaune ya tashi ya dube ni, xo na fada miki a kunnenki, makale kafada nayi Allah a'a sai dai ka fada min a nan ina jin ka, murmushi yayi, me yasa kike jin tsorona haka Niimatullah alhalin ni ba dodo bane, bata fuska nayi to ai har gara dodon dama nasan dodo ne amma kai ka rika kama ni kuma bayan kasan haramun ne, murmushi yayi wato bakin ki baxai yi laushi ba ko, to sai gobe xaki tafi gida, kuka na fara yi har sai da nayi ya ishe ni sannan ya fada min irin taimakon da xan masa, tausa xaki yi min, amma da sharadi baxa ki ce min kin gaji ba, idan kika ce kin gaji sai kin kwana kina yi, da kyar naja kafa naxo kusa da shi na fara yi masa tausar,  xuciyata cike da tsoron kada ya kamo ni, bayan na gama masa ya tashi ya shiga wanka yana fitowa muka hau mota ga mayar da ni gida.

08094136204

*jeeddahtulkhair?*??????????

MATAR DATTIJO CompleteWhere stories live. Discover now