MATAR DATTIJO page 56

913 31 0
                                    

💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
          *Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*

56

Ina shigowa daki na dauki wayata na duba, kiranta na gani kusan missed calls biyar ban samu damar bin ta a lokacin ba, kasancewar bana jin dadi ko na kirata baxan samu damar yi mata magana ba.

Kwantawa nayi don baxan iya cigaba da xama ba saboda ciwon da jikina ke yi, tun daga lokacin da ta dake ni ban sake jin karfin jikina ba nayi shiru ne kawai ban fadawa dattijo ba,don kada ya kara daukan xafi yaki dawo da ita, kiran wayar shi nayi na fada masa yanayin da nake ji a jikina, cike da tausayawa yake min magana tare da cewa xai dawo ya kula da ni, dakatar da shi nayi don bana son ya dawo gida ya bar aikinsa, rokon shi nayi a kan ya bari na tafi gidan innah, hana ni tafiyar yayi don baya son ya ga ina xirga-xirga, kiran innah yace nayi taxo taga jikin nawa.

Ina kiranta ta dauka, cike da shagwaba nake fada mata abinda ke damuna a cikin mintuna kadan ta iso, cike da mamaki ta shigo dakina tare da tambayata ina uwar gidanki take naga wajenta a kulle kuma alamu sun nuna babu mutum a ciki.

Sakkowa nayi na dawo inda take xaune, kwantar da kaina nayi a kan cinyarta ina kallon fuskarta nake magana, dattijo ya sallameta innah, a raxane ta dube ni yaushe wannan al'amarin ya faru Niimatullah amma baki sanar da ni mun shiga cikin maganar ba?

Wallahi innah nayi shiru da xancen ne saboda naga baya son maganar shi kansa bai fadawa kowa ba, cike da tausayawa take magana amma ban ji dadin faruwar wannan abu ba idan aka fara tara iyali hakuri ake yi, amma xan same shi nayi masa magana gara ya dawo da ita saboda yayanta.

Hirar da muka rika yi kenan ni kaina ina so ta dawo saboda baxan iya da hidimar dattijo ni kadai ba, yamma nayi ta fara shirye-shiryen tafiya.

Riko kafarta nayi tare da cewa ina xaki je innah? Kallona tayi tana murmushi ya naga kin rike ni Niimatullah ko so kike tsohuwar kafar tawa ta karye? Langwabar da kaina nayi xan yi kuka, ni Allah babu inda xaki je innah a nan xaki kwana kina ganin har yanzu ban warke ba amma xaki tafi ki barni. Kuma ai kin ce xaki tsaya kiga dattijo ku tattauna a kan dawo da Aunty idan kika tafi yanxu yaushe xaku yi maganar?

Dawowa tayi ta xauna, dafa kafadata tayi, ban fadawa malam xan kwana ba Niimatullah idan na xauna kin ga ban yi dai-dai ba.

A shagwabe nake mata magana haba innah indai baba ne nasan baxai hana ki kwana ba, wayarta na dakko bari na kira shi nayi masa magana nasan Allah baxai ki yarda ba.

Kira daya nayi masa ya dauka, fada masa nayi innah xata kwana ai kuwa naci sa'a bai hana ba, innah bata so ya yarda ta kwana ba saboda bata son dattijo ya rika yin rashin kunya a gabanta.

Innata na kalla ina dariya naji dadi baba ya bari ki kwana yau a dakina xaki kwana kuma a kan cinyarki, ture ni tayi tun wuri gara ma ki sani baxa ki kwana tare da ni ba dakin mijinki xaki tafi.

Bata fuska nayi haba innah yaushe rabon mu kwana tare, ni gaskiya da ke xan kwana, tabe baki tayi sai ki kwana mu gani, ni fa idan kika takura min kika ce sai kin kwana tafiya ta xan yi, gara ma tun wuri ki canja shawara shiru nayi tare da kwantawa a kan cinyarta.

Sallama muka ji gaba daya muka mayar da hankali ga mai yin sallamar, Hajiya maryam muka gani gaba daya ta canja wahala ko ta ina ta bullo mata, da fara'a ta karaso inda muke, cike da mamaki nake kallonta ko menene ya dawo da ita?

Karasowa tayi ta xauna gaisawa suka yi da innah sannan nima na gaisheta, hawaye naga yana sauka a fuskar ta cikin kuka ta fara magana, dan Allah kiyi hakuri ki yafe min Niimatullah duka abinda nayi miki kiyi hakuri, insha Allah hakan baxa ta kara faruwa ba.

Cike da tausayawa innah ta dube ta, komai ya wuce Hajiya kuma nima yau naxo gidan nan naga bakya nan nake tambayar Niimatullah ko kina ina sai tace wai kun rabu da Alhaji, gaskiya ban ji dadin faruwar hakan ba, kuma insha Allah xan shiga ciki mu sasanta.

Godiya tayi sannan ta tashi ta tafi, wajen yayanta ta nufa inda ta roke su da su bata mukullin bangarenta ta shiga, da kyar suka bata budewa tayi ta shiga ciki.

Dattijo na isowa yaga wajen Hajiya maryam a bude cike da mamaki ya bude kofar don ganin wanene a ciki.

*Follow me on wattpad @jeeddahtulkhaeer Tijj*

*jeeddahtulkhair😘*

MATAR DATTIJO CompleteWhere stories live. Discover now