MATAR DATTIJO page 17

1.6K 74 0
                                    


*[10/18, 11:22 PM] It'z B Y ebrerheem: 💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
          *Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*

*godiyata da tukwici na baxai yanke ba a gare ku sai dai kawai nace Allah ya bar xumunci*

*Et'z Yusuf*
*Abdurrahman ibrahim*
*it'z b y Ibrahim*
*na gode Allah ya bar xumunci*

17

Kai tsaye gida ya kaini, muna isa na bude kofar motar xan fita, ba tare da na kalle shi ba nace sai anjima, har nasa kafata a waje ya riko ni ya dawo dani hada fuskata yayi da tasa yana kallona, cikin siririyar muryarsa yake min magana, haka ake yiwa miji sallama Niimatullah? turo baki nayi to ai haka kowa yake yi, kokarin kwace hannuna nayi xan fita, dawo da ni jikinsa yayi tare da jan kumatuna yana murmushi, ke ba kowa bace da xaki rika yin abinda kowa ke yi, ke ta daban ce haka ma mijinki na musamman ne don haka yake bukatar komai na musamman daga wajen ki, domin son da yake miki ma na musamman ne, juyo ki kalle ni my Niimatullah nasan xaki tabbatar da hakan a idona.

ina kallonsa nayi saurin kawar da fuskata saboda yadda idanunsa suka canja, ni kaina baxan iya fassara irin kallon da yake min ba, murmushi yayi min tare da kwantar da ni a kirjinsa, me yasa har yanxu kike jin kunyata Niimatullah? ina ganin lokaci yayi da ya kamata ki daina jin kunyata, juyo ki dube ni, makale kafada nayi tare da cewa a'a, tallafo fuskata yayi tunda kunyata kike ji ina ganin yau xan tafi da ke na cire miki wannan kunyar saboda idan muka cigaba da kasancewa a haka xata cutar da ni, saurin dagowa nayi na dube shi, ka daina fadar irin wannan maganar Allah xan daina kula ka, shafa fuskata yayi ko kin daina kulani, ni sai na kula ki my Niima, dan turo baki nayi dama ba kada xuciya dattijon nan dariya yayi indai a kanki ne ba nida xuciya na yarda a kira ni da kowane irin suna.

rufe kofar motar yayi cike da mamaki na tambaye shi, a gida fa muke amma ka sake kulle mota, kallona yayi yana kashe idanu, ina bukatar ganin matata a kusa da ni shi yasa na kulle, yanxu ma tafiya xan yi da ke na shakata da abar alfaharina.

hawaye naji suna kokarin fito min a hankali na dube shi, kayi hakuri ka bani hanya na wuce gida kaga rana tayi kuma akwai aikin innah da ban karasa ba, jan kumatuna yayi yana min wani kallo, aikin mijinki ya fi muhimmanci fiye da wanda xaki je kiyi, dan yamutsa fuska nayi, aikin naka ne ya fi na innata muhimmanci lallai ma mutumin nan.

kafe ni yayi da ido, da ke baki sani ba lallai yarinyar nan kina ji da kuruciya, tunda baki sani ba yau xan ganar da ke, tare xamu tafi yanxu idan kin koma ki fadawa innah aikina kika tsaya yi xa kiji baxa ta ce komai ba saboda tasan matsayin miji a wajen matarsa, yana gama fada ya ja motar, hannunsa na rike ina kuka.

dan Allah ka tsaya kada ka tafi da ni, nasan kana da muhimmanci a wajena, Dariya yayi wanda har sai da fararen hakoransa suka bayyana, dadina da ke ga rashin kunya ga kuma tsoro, to ki kwantar da hankalin ki, ni ba siyar da ke xan yi ba kawai xan tafi da ke ne na nuna miki muhimmancin aikin miji.

hakuri na rika bashi amma yayi banxa da ni, tafiya mai nisa muka yi har muka iso wani katafaren gida wanda baxan iya bayyana ko a wane unguwa yake ba, kasancewar bana fita sosai, bude mana gate aka yi ya shiga da motar, muna yin parking wasu kyawawan yara maxa biyu suka iso wajen mu, da dukkan alamu suna farin ciki da ganinsa, sannu da xuwa suka yi masa tare da gaida shi, duk da cewa sun girme ni amma har kasa suka tsugunnah suka gaishe ni.

tambayar kaina na shiga yi wannan tsohon kuma ina ya kawo ni, kada dai fa a ce gidansa ya kawo ni, a hankali ya shafo fuskata mun iso my Niimatullah taso mu shiga daga ciki.

girgixa kaina nayi babu inda xan je ka shiga ka fito, kuma ina ma ka kawo ni ne?kallona yayi yana wani murmushi kawo ki nayi na siyar da ke tunda dai kin xama tawa, kuka na fara yi kayi hakuri kada ka siyar da ni dan Allah innata na sona ni kadai na rage musu kayi hakuri dattijona, dariya ya rika min har sai da ya sunkuya, sai da yayi dariyar ta ishe shi sannan ya dube ni, to baxan siyar da ke ba amma taso mu tafi.

makale kafada nayi babu inda xan je har sai ka fada min inda ka kawo ni, murmushi yayi gidan hutawar mu na kawo ki, kuma dole ki fito ko nasa a xo a dauke ki, saurin fitowa nayi saboda nasan kadan ne daga cikin aikinsa tsaf xai dauke ni, rike hannuna yayi har muka isa wani hadadden falo wanda yaji kayan ado na xamani, da gudu naga wata mata ta karso wajen mu Oyoyo uncle din yara, kamar su daya da dattijona komai da komai sai dai kawai ya dan fi ta hasken fata da kadan, cikin sakin fuska yayi mata magana, juyowa bangarena tayi tana dubana, sannun ki da xuwa amaryar mu, yau dai uncle ya cika alkawari ya kawo mana ke, cike da ladabi na gida ta, cikin kulawa take min magana da dukkan alamu tana da kirki, hannuna ya riko yana kallona.

Niimatullah wannan ita ce maimuna yar autar mu duk ita ce karama a dakin mu, cikin dasasshiyar murya nace to muka sake gaisawa, dattijo yana ji da kanwar sa kana ganin yadda suke hira xaka gane akwai shakuwa mai yawa a tsakanin su.

Hira naji suna yi a kan halayyar matarsa da irin abubuwan wulakancin da take masa, ni kuwa ina gefe ban sa musu baki ba, nunawa nayi kamar bana jin abinda suke fada, kwantar da kanshi yayi a kan kafadata a hankali na dan matsa saboda na lura shi bai fiye jin kunyar ido ba, murmushi yayi min tare da cewa munat kin ga dai amaryar tawa ko? fuskarta a sake ta bashi amsa na ganta uncle gata da kunya, jan hancina yayi, amma kuma akwai rigima da tsokana.

Dariya suka yi gaba daya, ai dole tayi rigima kasan amarya ce bata laifi, kaina a kasa na kasa dagowa saboda kunya, tambayar shi tayi, yaushe amaryar tamu xata tare ne, kamo hannuna yayi yana duban idona ni ko yanxu na yarda ta tare, na shirya tsaf na kula da matata, ita ce dai ban sani ba ko ta shirya

nade kaina nayi a mayafi, haka suka gama hirar su sannan muka tashi xamu tafi, kayayyaki masu yawa ta hado min har bakin mota ta rako ni da kyar na yarda na karbi kayan, muna shiga motar na fara harararshi, me yasa xaka min haka, dube ni fa ko kwalliyar kirki ban yi ba ka tashi ka wani kawo ni gidan kanwarka salon ta raina ni, yanxu duk kyan nan da kika yi ba kwalliya bane niimatullah? cikin tsiwa nace nafi son nayi gayu nayi kyau kada su ganni su ce min kaxama, murmushi yayi banda abin ki wa xai ganki ya kiraki da kaxama my niimah, Allah bakya rabo da rigima, kiran wayar shi aka yi yana dauka yaji innah ce ta kira.

tashin farko ta fara tambayar ina nake cike da ladabi ya amsa mata cewa na raka shi unguwa ne, bayan sun gama wayar na dube shi, kaga irin abin ko har innah ta gaji da jira ta kira, ni dai mu tafi dan Allah.

kamoni yayi ya kwantar da ni a kan wuyan shi, kin xama mallakina fa Niimatullah duk inda xan kai ki innah baxa ta ce komai ba, yanxu ma da kika ga ta kira don ta tabbatar da lafiyar mu ne, marairace masa nayi kamar xan yi kuka.

to naji ni dan Allah mu tafi, cike da kulawa yace min xan kai ki gida amma da sharadin sai kin min kiss, kuka na fara yi ina shure-shure ni baxan maka ba Allah na gaji da wadannan tsare-tsaren naka, kullum da abinda xaka ce nayi maka sai kace haka innah tace ka rika yi min.

tsura min ido yayi yana kallon ina ta abubuwana sai da na gama ya min magana idan xamu kwana a nan indai baki yi min ba baxan kai ki gida ba sai dai mu yi bacci a mota, da naga babu sarki sai Allah na kama hannun shi nayi masa, duk wanda nayi masa sai yace bai yi ba, sai da na yi masa kusan sau goma sannan ya yarda muka tafi.

MATAR DATTIJO CompleteWhere stories live. Discover now