MATAR DATTIJO page 57

969 35 0
                                    

💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
          *Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*

57

Saka kanshi yayi cikin dakin don ganewa idanunsa abinda yake xargi, yana dosar dakin yayi saurin ja da baya domin abinda yake tunani dai shi ya gani, cike da tuhuma ya fara magana da iznin wa kika dawo min gida har kika bude daki kika shiga ba tare da amincewata ba, a marairaice ta fara magana.

Na bi Allah na bi ka mijina dan Allah kayi hakuri ka yafe min a bisa dukkan abinda ya faru na aikata ne a bisa kuskure, naje wajen niimatullah ma na nemi yafiyarta kuma ta yafe min, saurin dakatar da ita yayi wannan yafiyar da tayi miki tsakanin ku ne ni bata shafe ni ba, kuma niimatullah ba tada hurumin baki umarnin ki xauna min a gidansa domin ba gidanta bane kuma ba xamanta kike yi ba, xamana kike yi don haka tun wuri ki tashi ki koma gidan ku ki cigaba da cin kwaki da xogale tunda haka kika xabar wa kan ki, yana gama fada ya fice a fusace. kifa kanta tayi jikin kujera tana kuka a xahiri take fadar ta cuci kanta tayi watsi da damarta da har ta kai mijinta bangon da baya jin rarrashinta.

A fusace dattijo ya shigo bangarena ganin yadda ya turo kofar falona da karfi nasan akwai maganganu a bakinsa sai dai yana shigowa ya ci karo da Inna sai kuma jikinsa yayi sanyi, a kunyace ya gaida ita sannan ya tashi ya shiga daki, har na share naki bin shi innah ta harare ni tare da cewa tashi ki bi mijinki, ban so ba na shiga dakin saboda bana son yayi min maganar hajiya maryam, cikin kasalalliyar murya nayi masa sallama a hankali ya dago ya kalle ni ba tare da ya amsa min ba kasancewar ran shi a bace yake, karasawa nayi kusa da shi na sake maimaita masa sallamar da nayi masa a wannan karon ya amsa sai dai bai dago kai ya kalle ni ba.

shiru muka yi na wani dan lokaci saboda ban san ta inda xan fara magana ba, don naga mutumin nawa yau a cikin xafi yake, a hankali na kira sunansa dattijona me yasa na ganka a haka ko wani ne ya bata min ranka? kansa a sunkuye ya amsa min kece kika bata min rai tunda kika sa wannan matar ta xauna min a gida ba tare da iznina ba.

Muryata a sarke na amsa masa wallahi ba ni bace dattijona innah ce taga halin da take ciki shi ne ta tausaya mata tace ta koma dakinta idan kaxo sai tayi muku sulhu, share xufar da ta cika masa fuska yayi tare da cewa babu sulhu tsakanina da Maryam ni kadai nasan irin axabar da na dandana a wajenta don haka har abada baxan so Allah ya kara maimaita min irin wuyar da na sha a hannunta ba.

cike da rarrashi nake masa magana, haba dattijo ya xaka kafe a kan magana daya kamar fadar Allah, tunda tayi kuskure a baya yanxu kuma ta dawo xata gyara kuskurenta ya kamata ka yafe mata, ko don yayan da ku ka haifa tare, mikewa yayi yana kallona da kin hakura kin rike maganarki niimatullah baxan taba jin wannan rokon naki ba,  ke kan ki matar nan ta kusa kashe ki amma kokari kike yi a dawo da ita wai ke mai kyakkyawar niyya ko? To ni dai take aure kuma nace bana yi ta tafi ta samu wani mijin mai irin halinta watakila xasu dai-daita ni dai na gama xama da ita, yana kammala maganar ya fita wajen innah yaje don su yi hira.

Tambayarta lafiyar jikina yayi da jaririna cikin sakin fuska ta amsa masa da lafiyar mu kalau, a cikin hirar tasu ta jefo masa tambaya wadda sai da tasa ya dauke wuta gaba daya, Alhaji ashe haka abu ya faru yau nake samun labarin cewa ka rabu da Maryam me yayi xafi haka? Kansa a sunkuye ya fara magana wallahi matsalolin ne suka ki ci suka ki cinyewa innah, kullum a cikin tashin hankali nake ni da niimatullah, gata nan, ya nuna ni da hannunsa duk tasan halin da ake ciki, kullum kokarinta ya xa a yi ta ga bayana wannan dalilin yasa na sallameta saboda tashin hankalin da nake ciki da yawa.

girgiza kai innah ta shiga yi, kayya abu ba dadi Alhaji amma da anyi hakuri kuruciya ce wata rana xata daina, kuma ko yanxu nasan tayi laushi ta gane abinda take yi ba mai kyau bane baxa ta Kara maimaitawa ba, kuma Alhaji idan aka fara tara yara ba a son saki duk abinda xai faru hakuri ake yi wata rana sai kaga ya xama labari.

cike da nutsuwa ya amsa da haka ne innah sai dai ita abin nata ya wuce lissafi, nayi hakurin har sai da ta kai ni bango.

Hakuri innah ta cigaba da bashi har sai da ya hakura ya sakko, umarni innah ta bani da naje na kirata, tashi nayi na nufi bangarenta inda na fada mata innah na kiranta.

*follow me on wattpad @jeeddahtulkheer Tijj*

*jeeddahtulkhair😘*

MATAR DATTIJO CompleteWhere stories live. Discover now