MATAR DATTIJO page 24

1.5K 66 0
                                    

💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
           *Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*

*dedicated to Salma Nura*

24

Washe gari ma sai da aka sake gyara ni sosai kyawuna ya kara fita duk inda ka kalle ni sau daya sai kso ka kara kallona, shi kuwa dattijona kullum yana kan hanyar xuwa ganina, a lokuta da dama idan yaxo da kyar yake tafiya, saboda yadda yake yaba kyauna kullum da rigima muke rabuwa.

yau da sanyin safiya na shirya don xuwan wajen kunshi, soro na fita na xauna na hada kaina da gwiwa saboda kaina yau ya dau caji, ina jin ciwo sosai a raina idan na tuna gobe xan bar gida, wasu xafafan hawaye ne suka rika kwarara a fuskata tambayar kaina na shiga me yasa har na amince da auren dattijo gashi nan yana son raba ni da rayuwar gidan innata, ji nayi an kira sunana a hankali na dago kaina, dattijona na gani tsaye yana min murmushi fuskar sa cike da damuwa yake tambayata lafiya kike kuka my Niimatullah?lumshe idanuna nayi cikin kuka na bashi amsa, ina ji a raina kawai xan fasa auren nan bana son rabuwa da innata, rarrashina ya shiga yi gami da kawo min hadisan da suke magana a kan muhimmancin aure a haka har hankalina ya kwanta xuciyata tayi sanyi.

Hannu yasa ya tayar da ni tsaye, ina rungume a jikinsa har muka isa bakin mota, bude min murfin motar yayi na fara shiga sannan ya shigo, kallona ya rika yi a xahiri naji yana godiya ga Allah,Allah na gode maka da wannan babbar kyautar da ka bani Allah ka bani ikon riketa amana, shafawa yayi sannan ya dube ni yana min murmushi

Kece kaddarar da na jima ina tsimayin tarar da ita a rayuwata, zan kasance a duk inda kike Niimatullah,zan tsaya a duk inda kika tsayar da ni. Ina sonki, adadin son da kalmomi ba zasu iya siffantawa ba,
xan kasance mai
baki kulawa da kuma kaucewa dukkan abinda zai sanya ki a damuwa fatana ki tabbata a cikin farin ciki,ban son irin dadin da xan ji ba idan na ganki gobe a dakina, fatana dai Allah ya bamu xaman lafiya.

amsa masa nayi da ameen muna xuwa ya sauke ni a kofar gidan,kudi ya dakko ya bani, cike da shagwaba nace masa baxan karba ba, dago fuskata yayi yana min murmushi ki karba my Niimatullah kinga ba a yin kunshi kyauta, langwabar da kaina nayi to ka rage kudaden sun yi yawa, murmushi yayi tare da cewa ban san me yasa kike tausayina ba Niimatullah, kaina a kasa na amsa masa saboda ka xama mijina kuma innah ta fada min tausayin miji abu ne mai kyau, girgixa kai yayi yana murmushi gaskiya innah ta iya tarbiyya Allah ya saka mata da aljannah da take kokarin saita min uwar yayana. fitowa nayi na shiga gidan kunshin.

ba tare da bata lokaci ba aka fara yi min, gaskiya kunshin yayi kyau domin ya dace da kafata sosai, da misalin karfe hudu ya iso daukana, tun daga nesa yake min murmushi jikina a sanyaye na karaso wajen sa tare da cewa an gama, shafa fuskarsa yayi tare da cewa miko min hannun na gani, makale kafadata nayi a'a baxan bayar ba, jan hancina yayi me yasa kike min rowar jikinki kin xama tawa fa Niimatullah babu abinda yayi saura.  cike da tsiwa nace Allah da akwai abinda yayi saura tunda saura kwana daya naje gidan ka, murmushi yayi tare da jan hannuna to naji taho mu tafi bana son wannan rigimar taki.

A kofar gida ya ajiye ni ya wuce gidansa, ina shiga gida nayi sallah na fada bandaki nayi wanka sannan na koma dakin innah na kwanta kasancewar yanxu bana son hayaniya nafi son na kebe ni kaina na rika tunanina, yau ko baccin kirki ban samu nayi ba saboda bakin cikin xan bar gidan innah cikin dare na tashi ina kuka ina bankwana da gadon da nake kwana.

rana bata karya sai dai uwar diya taji kunya, A yau lahadi 14-10-2018 ta kama ita ce ranar da xa a kaini dakina, da kyar aka yago ni nayi wanka saboda duk wata gwiwa ta jikina tayi sanyi, yan uwa da abokan arxiki daga gurare daba-daban sun halarci bikina, duk wanda yaji labarin irin son da dattijo ke min sai yayi mana fatan alkhairi da samun xuri'a ta gari, anci an sha duk abincin da aka ci a wajen dattijo ne yasa aka kawo mana daga 10 to 10 restaurant, an yi komai cikin rufin asiri.

xaune nake a daki na xuba uban tagumi ina tunani, cikin nutsuwa aka yi sallama a hankali na dago don ganin mai sallamar daya daga cikin kannen mahaifiyata ne, gefena ta samu ta xauna, tashi ki  kintsa Niimatullah an kawo motocin tafiya gidan ki, a xabure na dago na kalleta, tun yanxu xa a tafi ni gaskiya yayi wuri a bari sai an yi sallar magariba, cikin kulawa take min magana ki tashi mu je ga ruwa can an kai miki bandaki gara ki shirya da wuri yanxu xaki ga magaribar tayi, hawaye ne suka cika idona cikin kuka nake mata magana, wai dama da gaske ne sai an kai ni gidan mutumin nan Aunty, ni wlh ba inda xan je. lallaba ni ta shiga yi har sai da na tashi na tafi ina wankan ina kuka.

Bayan na kammala na fito na sanya kayana, wajen baba aka kaini inda ya fara yi min nasihohi masu ratsa jiki a kan biyayyar aure da kuma kyautatawa miji bayan ya gama aka kaini wajen innah don sallama da ita da kuma yi min nasiha.

muna hada ido da ita ta fara kuka da sauri na fada jikinta muka rungume juna, cikin kukan take min nasiha ki bi mijinki sau da kafa Niimatullah, duk abinda yace kiyi masa kiyi banda gaddama, sannan kuma ki xama mai hakuri da kau da kai, kada kice duk abinda kika gani sakin yi magana, kiji ki qi ji, ki gani ki qi gani, ki xama mace mai kawaici da hakuri, kada ki bari mijinki yaji wani abu mara dadi daga gare ki, ki kiyaye masa ganinsa da jinsa da hancinsa, abinda nake nufi da ki kiyaye masa ganinsa shi ne kada ki bari yaga wani abu na aibu a gare ki, abinda nake nufi da ki kula masa da jinsa,kada ki bari ki fada masa wata magana mara dadi da har xata bata masa ransa, duk abinda xai ji daga gare ki ya xama mai dadi ne, abinda nake nufi da ki kiyaye masa hancinsa kada ki bari yaji wani wri daga gare ki kullum ki kasance cikin tsafta da kamshi ki kula da tsaftar hakoran ki, Allah ya baki sa'a yasa kin shiga a sa'a Allah ya kare ki daga dukkan sharri yasa ki xama tsohuwar gidansa.

kuka sosai muka rika yi ni da innah da kyar aka raba ni da ita aka saka ni a mota, gidansa da ke unguwar bompai aka kaini bangare biyu ne a gidan, don haka bangaren kishiyata aka fara kaini inda aka damka mata amanata, a wulakance ta karbe mu amma duk da haka ba wanda ya kula da abinda tayi mana.

kai tsaye bangare na aka wuce da ni, ina shiga na godewa Allah da irin namijin kokarin da dattijona yayi min,ko iyayena masu hali ne iya abinda xa a saka min kenan a dakina komai yaji, daya daga cikin dakunana aka shigar da ni inda aka xaunar da ni bisa gado, bayan an yi addu'a an shafa kowa ya watse ya bar ni ni kadai, kuka na ne ya tsananta na rika kiran innata, tashi nayi na fara kewaye gidan dakuna ne guda uku gaba duyan su an saka masu kayan gado na alfarma, kujeru na ma duk masu kyau ne wadanda aka yi musu ado da yadi launin orange sai kuma pillow din su da suka kasance launin baki, kitchen dina ma cike yake da kaya gwanin sha'awa, taku naji alamar xa a shigo wajena da sauri na koma gado na nade kaina a mayafi.

*jeeddahtulkhairi😘*

MATAR DATTIJO CompleteWhere stories live. Discover now