MATAR DATTIJO page 4

2K 102 1
                                    


[9/27, 3:04 PM] Itz B Y ebrerheem: 💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
          *Adam*
*(Jeeddahtulkhair)*

4

Ina cikin bacci naji wayar innata tayi ringing, a cikin baccin na rarrafa na dauka, bakuwar number na gani, da farko har naki dauka sai aka dame ni da kira na saka wayar a kunnena, sallama nayi cikin dasasshiyar murya,  wata iska naji an hura min cikin kunnena wanda har sai da sautin ya tsirga min cikin jikina, cikin sassanyar murya aka amsa min sallamata tare da cewa na tashe ki kina baccin ki ko??

shiru nayi ba tare da na bada amsa ba, cikin raina nace lallai dattijon nan ya fiye nacin tsiya.
shirun da yaji nayi ne yasa ya cigaba da magana.

kiyi hakuri gimbiyar mata, nasan dama dole xan dame ki saboda tunda na ganki kika kwance min tunanina, yanxu haka na kasa bacci saboda tunanin ki,  nasan baxan iya lafiyayyen bacci ba idan ban ji muryar ki ba.
cikin tsiwa nake masa magana, to kaji muryar tawa sai me? murmushi yayi wanda har sai da naji sautinsa a kunne na, Niimatullah sarkin tsiwa, kiyi hakuri ki rage wannan tsiwar taki, idan ba haka ba kuma na kamaki a dakin mu xa kiyi bayani ne. hararsa na rika yi kamar yana kallona Allah ya sauwake naje dakin dattijo, na fada maka ni matar yaro ce ehe.

dariya yayi wannan tsiwar taki ba karamin burge ni take yi ba Niimatullah, haushi ya bani na kashe wayar, shi kuwa sai juyi yake bisa gado duk ta tayar masa da wani sabon kwadayi, shaawarta da shaukinta sun mamaye shi a ranar da kyar ya iya bacci saboda tunanin Niimatullah har sai da yayi ciwon mara, kasancewar matarsa bata damu da kulawa da hakkinsa ba, burinta a Kullum bai wuce ta karbi kudi a hannunsa ba, wannan ne kawai amfaninsa a wajenta amma duk wani hakki nasa tasa kafa ta shure.

washe gari da safe nake fadawa innata yadda muka yi da shi, murmushi tayi tare da ce min ke yanxu wane hukunci kika yanke a kan son shi, bata fuska nayi ni Allah bana son shi innah, baki ga gemunsa ba duk furfura, dariya na bata har sai da ta kusa tuntsirewa, menene da farin gemun nasa Niimatullah, indai xa a samu xaman lafiya ai babu wani abu, ke dai kiyi addu'a Allah ya zaba abinda ya fi Alkhairi.

tashi nayi na fara shirin tafiya makaranta, naxo daukan jakata kenan wayar innah tayi ringing a hankali na mika hannu na dauka, number da ta kira ni jiya na gani, wurgi nayi da ita gefe guda,  innata ce ta lura da abinda nayi cikin tausasa lafazi take min magana.

ya kika jefar min da waya Niimatullah? turo baki nayi wannan mayen ne ya kira ni, ni dai tun wuri kiyi masa magana ya daina kula ni, ba aure xan yi yanxu ba sai na kara girma. kallona innah tayi banda wannan girman da kika yi wane girma kuma xaki kara yi Niimatullah? tabe baki nayi ni dai ban girma ba innata abinda ko girki ban iya ba, ajiyar xuciya innah tayi, har yanxu yarinta na damun ki ni'ima Allah ya kara miki nutsuwa.

ba Ameen ba innah indai don a aura min wannan dattijon ne baxan taba hankali ba, naira goma ta bani sannan na dauki flask din abincina, a damuwa na kasance a makaranta domin kwakwalwata ta daina karbar komai saboda maganganun da aka bijiro min da su.

yau ma da yamma yaxo gidan mu har tsakar gida ya shigo don gaisawa da innah, tarar da ni yayi ina ta sharawa jikina ruwa duk na jika kayana, kallona ya shiga yi ya kasa dauke idonsa daga kaina, da dukkan alamu ina burge shi, magana innah tayi min Niimatullah baki ga bakonki ba, shiru nayi mata na cigaba da abinda nake yi. A soro tayi masa shimfida komawa yayi ya xauna yana jiran fitowa ta, wajena innah ta dawo tayi min magana, ban saurareta ba na cigaba da tsallena ina shara ruwa a kaina, duka ta kai min Allah yasa na kauce bata same ni ba, fada ta shiga yi min

wuce daki ki kintsa kin bar bawan Allah a tsaye, dukan kasa na rika yi da kafafuna, ni Allah ki kyale ni innata. lallaba ni ta rika yi har sai da na cire jikakkun kayan da ke jikina na sanya wasu na tafi wajen shi.

xaune na tarar da shi ya hada kai da gwiwa, yana dago manyan idanunsa ya kalle ni naga ya tafi wani xuxxurfan tunani, shauki da begen Niimatullah ya cika masa xuciyarsa a duk lokacin da yaga yarinyar wata jaraba ce ta musamman ke kama shi ya rasa dalilin da yasa yake shaawarta haka, tsayawa nayi a kansa tare da cewa gani, wani tattausan murmushi ya sakar min gami da kashe min manyan idanunsa, Niimatullah!! ya kira sunana da tattausar muryar sa, guri na samu na xauna raina a bace yake saboda irin kallon da yake min, tsare ni yayi da ido har sai da na tsargu na rasa me yake kallo a tare da ni, gyara xama nayi na sunkuyar da kaina kasa.

Yar amaryata naji ya kira ni, cikin tsiwa nake masa magana,  kada ka sake ce min amaryarka ni ta mai rabo ce, murmushi yayi ai nine mai rabon, jira kawai nake baba ya dawo nan da sati daya nake son a yi mana aure, saboda hakurina ya fara karewa na kosa naji matata a kusa da ni, saurin xare ido nayi, a kusa da wa xaka xauna tabdi? murmushi yayi tare da bani amsa a kusa da ke mana, tsaki naji Allah ya kare ni daga auren *Dattijo* ragowar wata, ni sai yaro danye sharaf kamar ni, murmushi yayi xaki gane amfanin dattijo da dadinsa wajen ibadar aure ke dai kiyi fatan xuwan ranar da xan kasance da ke.

mikewa nayi na tafi gida saboda kaina baxai iya daukan maganganunsa ba, kirana ya shiga yi nayi banxa da shi na  wuce gida, haka ya hakura ya kyale ni.


MATAR DATTIJO CompleteWhere stories live. Discover now