MATAR DATTIJO page 59

1.7K 65 4
                                    

💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
           *Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*

59

Zaune nake na idar da sallah ina adduar Allah ya sauke ni lafiya, saboda yau cikina ya kai wata tara har ya dora da yan kwanaki, kwantawa nayi kasancewar babu wani karfi a jikina, banda ciwo babu abinda bayana da cikina ke yi,  maman munir ce ta shigo sallama tayi ta karaso kan kujera ta xauna yadda taga jikina ba karfi yasa ta dago ni a hankali tare da cewa ya jiki Niimatullah? muryata a kasa na amsa da sauki Aunty. yar hira muka fara yi bamu dade ba bacci ya kwashe ni don haka ta kulle min kofar dakin ta fita, abinci ta fita ta kawo ta ajiye don tana farkawa ta dauka ta ci.

Cikin bacci naji wani irin ciwon ciki ya kamani, ciwon da naji yau ba irin wanda na saba ji bane don haka da hanxari na dauki waya xan kirata sai kuma naji ya lafa don haka na jingina kaina jikin kujera ina yan addu'o'ina, kwanon abinci na janyo xan ci har na kai cokali bakina naji ya sake juyawa ji nake kamar xan bar duniya.

Kasa kai hannu na dauki wayar da xan kirata nayi, juyi kawai nake hannuna rike da cikina, nafi minti talatin a wannan hali har na fara fita daga hankalina, gashi na kasa daukan waya na kirata, turo kofar dakina aka yi dattijo ne ya shigo yana ganin halin da nake ciki ya fita a gigice ya kirata.

Duba ni ta shiga yi inda ta tabbatar da lokacin haihuwa ta yayi saura kadan, mota ya dauka aka kaini asibiti, ba tare da bata lokaci ba aka bamu gado kwanana daya ina nakuda don har an yanke shawarar yi min CS sai kuma Allah ya kawo haihuwar na haifi ya mace.

Murna a wajen dattijo da maman munir kuwa ba a magana saboda sun dade suna jiran Allah ya basu ya mace sai yanxu Allah ya basu, ban dade ba aka sallame ni tunda likitoci sun tabbatar da cewa lafiyata kalau, da an yanke shawarar kai ni gidan innah saboda xan fi samun kulawa a can,sai kuma dattijo ya hana saboda baya son nayi nisa da shi.

Innah ce ta dawo gidan da xama amma a xaune take kawai babu wani aiki da take yi komai maman munir ke min, tun daga kan wankan baby har xuwa gyaran gida da girki, wanka kawai innah take mun shi ma tunda tayi min sau daya nace ta kyale ni xan cigaba da yin abuna.

Tun da na haihu maman munir ta daina xuwa office kullum tana makale da baby tana kulawa da mu, akwati guda tayi min na kayan barka, ban taba xaton haka take da kirki da karamci ba sai yanxu gaba daya ta canja halayyarta.

Dattijo ne ya shigo dakina samuna yayi muna tare da innah muna hira, ajiye kayan da ya siyo yayi tare da gaida innah cikin ladabi, miko masa yarinyar tayi a ladabce yasa hannu ya karba, tashi innah tayi ta bar dakin kallona yayi yana murmushi tare da rungumo ni da hannunsa daya, Alhamdulillah dole na godewa Allah da ya axurta ni da samun ya daga jikinki mai albarka nasan yarinyar nan xata gado irin kyawawan halayen ki irin tarbiyyar da innah ta baki irinta xaki bata, babu abinda xan ce sai dai godiya ga Allah.

A marairaice ya kalle ni, wai yaushe xaki samu tsarki ne nifa na fara gajiya? Xaro idanu nayi tsarki kuma dattijo yau fa kwanana shida sai dai nan gaba xan samu. Bata fuska yayi kamar xai yi kuka ni fa na kosa ki samu tsarki mu koma duty don na gaji da wannan rabe-raben da nake yi.

Langwabar da kaina nayi haba dattijo kana dakin matar taka xaka ce kana rabe-rabe ni fa bana son irin wannan, kamo ni yayi kiyi hakuri amaryar dattijo baxan sake fada ba.

Mayar da hankali yayi ga kallon babyn yana yaba irin kyawun da Allah yayi mata komai nata abin sha'awa, a hankali ya fara yi min magana, xuwa nayi dama mu yi shawara a kan sunan da ya dace a saka mata, wane suna kike so?

Kaina a sunkuye na amsa da maryam na xabar mata, a raxane ya kalle ni maryam fa kika ce canja wani sunan baxan sa mata sunan kishiyar ki ba. bata fuska nayi Allah ni ba kishiyata bace yar uwata ce indai kana son farin cikina ka saka mata sunanta.

Girgixa kai yayi tare da sakin ajiyar xuciya tunda ke kika ce kina son xan saka mata Niimatullah ba komai, Allah ya bata albarkacin mai sunan ta asali amma ba wannan maryam din taki ba, dan hararshi nayi bana so fa Allah, murmushi yayi na daina amaryata, tashi yayi ya fita don har yanxu ana cigaba da shirye-shiryen suna.

Washe gari ta kama ranar suna raguna uku dattijo ya yanka inda yarinya ta ci suna maryam amma muna kiranta da Iman saboda bana son a fadi sunan haka don a yiwa Aunty kara, farin ciki a gurin maman munir kuwa baya misaltuwa sai ririta ni da jaririyar take yi, wasu kawayen nata su ce na burge su wasu kuma su ce makirci ne da iya xamana, kowa dai da irin abinda yake fada.

Taro yayi taro anci ansha na samu alkhairai da yawa daga wajen abokan dattijo da kuma kawayen Hajiya maryam don barka sai da na rasa bakin godiya, taro ya tashi lafiya kowa ya tafi gidansa duk kayan da aka bata maman munir ce tasa yan uwanta suka gyara, duk wanda yaga irin xaman da muke yi a yanxu da yadda hajiya maryam ta canja sai yayi mamaki kuma sai mun bashi sha'awa, kanmu ya hadu sosai.

A kullum Iman a hannun maman munir take wuni duk abinda ya kama ita take yi mata tun daga lokacin haihuwarta har xuwa lokacin da tayi wayo, ta shaku da ita sosai, don kafin ta tambaye ni abu sau daya ta tambaye ta sau goma mutane da yawa sun dauka ita ta haifeta, yayyenta ma haka suke gwada mata gata komai suka samo Iman ta shaku da su sosai.

Haka rayuwar mu ta kasance cikin farin ciki yanxu babu wata matsala da nake fuskanta a gidana komai lafiya lau tsakanina da mijina da kishiyata na mayar da yayanta kamar nawa, sai dai tun daga kan Iman Allah bai sake bani haihuwa ba, amma ban damu ba don nasan baiwar Allah da yawa take idan yaso xai kara min.

Alhamdulillah a nan na kawo karshen wannan littafi ina adduar Allah ya bamu ikon amfani da darasin da ke ciki, abinda muka yi kuskure kuma Allah ya gafarta mana.

Sai kuma kun ji ni a sabon novel dina na gode da addu'o'inku da kaunar ku gare ni Allah ya saka muku da alkhairi.

*jeeddahtulkhair😘*

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Feb 04, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

MATAR DATTIJO CompleteWhere stories live. Discover now