MATAR DATTIJO page 45

1.1K 48 0
                                    

💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
          *Adam*
*(Jeeddahtulkhair)*

*Follow me on instagram @jeeddahtijjani*

45

A bakin gidan innah muka tsaya, mun fi minti biyar a tsaye bamu ce da juna komai ba, kifa kanshi yayi jikin sitiyarin mota ban san me yake tunani ba, a hankali nasa hannu na dago kanshi, kallo daya nayi masa nasan yana cikin damuwa fuskarsa duk ta jike da gumi idon shi yayi ja, cikin dasasshiyar muryata na fara tambayarsa, lafiya naga duk ka shiga damuwa dattijona? A hankali ya bude ido ya dube ni, muryarsa na rawa kamar xai fashe da kuka yake min magana.

Idan nace bana cikin damuwa nayi karya Niimatullah, babban tashin hankalina bai wuce rabuwa da ke ba,na rasa me wannan matar take so da ni kokari take ta tarwatsa min rayuwata, duk inda tasan xan samu farin ciki sai tayi kokari ta raba ni da wajen, ba ke kadai ce matar da na fara nema da aure ba, na auri mata wajen sau biyar duk bala'inta ya Kore su, ke din da nake fatan samun farin ciki a wajenki tana neman raba mu, yanzu da wane ido xan kalli innah duk nacin da tayi min a kan na barki a gida naki amincewa, yanzu kuma daga tafiyar mu kawai sai taga mun dawo, kuma duk Wanda ya kalle ni ko ya kalle ki ya san ba dadi ne ya dawo da mu ba, ni wallahi kunyar innah nake ji, ban san da wane ido xan kalleta ba.

Gashi bana so nayi nisa da ke nafi son kullum na rika kallon ki a gefena,kin san dai yadda mijinki yake da yawan bukatar ki a kusa da shi, nasan babu inda xan je na samu farin ciki idan ba wajenki ba.

Ajiyar xuciya na sauke saboda tausayin dattijona da ya kama ni wannan matar tasa ta xame masa masifa, bata son xaman lafiya gaba daya tana shiga hakkinsa sosai kasancewar shi ba mutum ne mai son tashin hankali ba,amma da wani ne tuni ya sallame ta, dago fuskata yayi yana kallona ya naji kin yi shiru Niimatullah?

Rausayar da kaina nayi gefe guda, tare da lumshe ido tausayin ka nake ji dattijona, ina tunanin halin da xaka shiga idan bana nan amma xan baka shawara kaje ka nemi sulhu da matarka don ina kyautata xaton idan baba yaji irin xaman da nake yi a gidanka baxai bari na koma ba, saboda yanxu duk abin nan da ake yi bai sani ba...

Cikin tashin hankali ya dube ni, kada ki sake fadar irin wannan maganar Niimatullah, baba dattijo ne yasan halin mata da irin kulle-kullen da suke yi wa kishiyoyi baxai fara raba auren mu ba, saboda yasan muna son juna, kuma xai tausayawa halin da xan fada idan aka raba ni da ke, ina sonki Niimatullah baxan iya rayuwa babu ke ba, bazan daina sonki ba, ko da a ce za a sanya mashi a ciro zuciyata daga cikin kirjina, zan hadiye dukkan wani zafi, zan jure kowace irin azaba matukar  xan cigaba da rayuwa da ke, ina fatan kema zaki kasance cikin sona na tsawon rayuwa.
Ya karasa maganar yana share kwallar da ta cika masa idanu.

Cike da tausayawa na dube shi Idan har akwai wani abu da zan roka a wajen ka, bai wuce na roke ka a kan, ka amince mu kasance tare ba har abada, bana jin xan iya nisa da kai ko na minti daya, rayuwata xata kasance cikin kunci matukar bana tare da kai ina fatan kasancewa a kirjinka har abada Ina sonka dattijona.

Kamo ni yayi ya rungume a kirjinsa naji dadin kalamanki Niimatullah kin kwantar min da hankalina kuma kin yaye min dukkan damuwata,wannan dalilin ya tabbatar min da cewa ina rayuwa da mace ta gari mai son farin cikina, daga hannu yayi sama yana addua, ya Allah kada ka nisanta ni da wannan baiwar taka kai kadai kasan adadin yadda nake sonta, ya Allah kada ka jarrabe ni da rashinta ko na minti daya ne, yana gamawa ya shafa ya kara makale ni a jikinsa, min fi minti talatin muna soyayya sannan ya dago ya dube ni.

Tashi ki shiga ciki amaryar dattijo, cike da shagwaba na langwabar da kaina ni Allah sai ka raka ni, me xan je na fadawa innata, cikin marairaicewa yake min magana tare da saka hannuna a cikin nashi.
Kiyi hakuri Niimatullah wallahi kunyar innah nake ji ban san da wane ido xan kalleta ba kinga dai yadda muka yi da ita kafin ta kyale ni na tafi da ke.
Shagwaba na rika yi masa Allah sai mun tafi tare ko kuma a hakura mu koma gida, tallafo kaina yayi kin san dai ina sonki ko amaryata, gyada kai nayi alamar eh, gyara xama yayi to ki nutsu ki saurare ni, tunda ina sonki baxan kai ki wajen da xa a hallaka ki ba, ko so kike mu koma maryam ta rika gana mana axaba? kaina a sunkuye na amsa masa da a'a.

Cike da kulawa ya sake kallona to tunda haka ne dan Allah ki tashi na raka ki soro ki je wajen innah kullum xan rika xuwa ina ganinki...

A sanyaye na fito daga motar rako ni yayi har soro sannan ya xaro kudi ya bani yayi min sallama ya tafi.

Da sallama na shiga gidan sai dai shiru ba a amsa min ba don haka kai tsaye na wuce dakin innah tarar da ita nayi tana bacci don haka ban tashe ta ba, nima na samu waje na kwantar da kaina.

Sai da tayi baccinta ta koshi sannan ta tashi tana bude ido muka yi ido hudu da ita cike da damuwa ta tashi ta xauna ta fara tambayata lafiya naga kin sake dawowa ko jikin ne?

Murxa ido na fara yi xan yi kuka, cike da kulawa ta sake tambayata me yake faruwa naga kina murxa ido xa kiyi kuka? Rausayar da kai nayi tare da cewa ba komai innah, bata fuska tayi a babu komai ake samun komai kinga Niimatullah bana son rufa-rufa ki fito ki fada min gaskiyar abinda ya sake dawo da ke, ko baki fada min ba nasan ba lafiya ce ta dawo da ke ba kawai dai na tambaye ki ne saboda na tabbatar da abinda xuciyata take tunani.

Bayani na fara yi mata ina maganar ina hawaye sai da na kammala gaba daya ta sauke ajiyar xuciya.

Ni fa wannan auren ya fara fita daga raina Niimatullah kullum cikin fitina mijinki bai hana ki jin dadi ba amma wata kishiya ta takura miki,ni da iya kishi kadai take yi baxan damu ba saboda kishi kumallon mata ne duk macen da aka yiwa kishiya dole tayi, amma ita wannan nata ya wuce ka'ida saboda Neman lafiyar ki take yi, ashe gaskiyar malam da yace baxa a yi auren nan ba tun a farko ashe irin wannan yake gudu, ban gano illar hakan ba sai yanxu, gaskiya baxa ki koma ba Niimatullah kin dawo kenan bari na jira Malam din ya dawo mu yi maganar yanxu yaje jana'iza, tayi na farko tayi na karshe baxa ta hallaka mana ke ta cuce mu ba.

Gabana naji yana dukan uku-uku saboda tunda nake da innah ban taba ganin ta dau xafi irin na yau ba addua na rika yi Allah yasa kada a raba aurena da dattijo saboda yana sona yana nuna min kulawa.

*follow me on wattpad @jeeddahtulkhaeer Tijj*

*jeeddahtulkhair😘*

MATAR DATTIJO CompleteWhere stories live. Discover now