MATAR DATTIJO page 14

1.6K 71 0
                                    

💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
          *Adam*
*(Jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*

14

Tsayawa tayi ta kare min kallo sannan ta kira sunana cikin nutsuwa, Niimatullah!! A hankali na dubeta, sunanki mai dadi da kuma kyau, kamar yadda wannan sunan naki yake haka nake son mayar da ke, amma sai kin bani hadin kai,kuma sai kin saki ranki sannan xaki iya koyar komai don farantawa mijinki, duk abinda baki sani ba kada ki ji tsoron tambayata ki dauke ni a matsayin kawarki. kece mace ta nawa a wajen mijinki?? kaina a sunkuye na amsa mata da nice ta biyu, girgixa kai tayi, yayi kyau tunda kuwa haka ne dole ki lura ki xage damtse ki iya komai idan ba haka ba xaki xama yar kallo a gidan miji maybe akwai abubuwan da matarsa ta saba masa da shi matukar kika xama banxa bakya yi masa sama da abinda take yi xata kwace miki miji, kiyi amfani da kuruciyarki ki mallake mijinki.

Ajiyar xuciya tayi sannan ta sake jefo min wata tambayar kin tare a gidan mijinki? daga mata kai nayi tare da cewa a'a sai na kara wayo, murmushi tayi ai kuwa mijinki yayi dabara da ya kawo ki nan don xaki koyi wayon da ko a gidan mata dari xaki xauna kiyi xaman aure, amma fa darasin mu yana bukatar a cire kunya, kuma yana bukatar a rika gwadawa, dubanta nayi tare da tambayarta.
malama ya xa a yi na cire kunya innata ta fada min kunya adon mace ce, murmushi tayi tare da dafa kaina, a wajen mijinki kunya haram ce amma a wani wajen kunya aba ce mai kyau abinda hausawa suke nufi kenan.

wani abu ta dakko a kwalba ta tsiyaya min a cup, karbi wannan kisha tun Yanxu nake son na fara hada ki ta yadda xaki rikita tsohon nan, karba nayi na fara sha, ina kurba daya na fitar da shi, Allah baxan iya sha ba Aunty karbi kayan ki, bata fuska tayi haka xaki daure kisha dama ba dan kiji dadi xaki sha ba, sai dan farantawa mijinki, takura min tayi har sai da na shanye gaba daya.

bayan na gama sha ta mika min wani abu a roba karbi wannan turaren da xaki rika tsarki da shi ne, ina so ki rika kamshi ko ta ina, sannan ki nisanci tsarki da ruwan sanyi, da shan ruwan sanyi domin wadannan abubuwan suna taka muhimmiyar rawa wajen mayar da mace salam, sannan ki daina xama a kasa ba tare da shimfida ba ki daina yawo ba takalmi a tsakar gida hakan yana ragewa mace ni'imarta, ki daina wanka da ruwan sanyi, sannan ina so a Kullum ki dafa lalle ki rika wanka da shi hakan yana karawa mace dumin jiki, kuma kin san mace mai dumi darajarta daban take a wajen miji, yau nake so ki fara duk wadannan abubuwan da na xayyana miki bana son wasa, idan kika karya dokata guda daya xaki ga bacin raina, cike da ladabi na amsa mata baxan karya miki doka ba insha Allah.

Tafiya ta shiga koya min salo daban-daban, idan tayi wani abin har kunyar kaina nake ji, haka ta rika koya min kala-kala duk wacce aka koya min sai na gwada idan nayi dai-dai ta gode min idan nayi kuskure ta gyara min ta sake koya min, bayan mun gama ta kira dattijo yaxo don ya tafi da ni, bata dade da kiran shi ba ya iso.

Har bakin kofa ta rako ni, umartata tayi da na fara gwada abinda ta koya min tunda dai mallakina ne, dubanta nayi kamar xan yi kuka. Allah baxan iya ba Aunty kunya nake ji kiyi hakuri na fara gwadawa gobe.

hararata tayi, haka muka yi da ke Niimatullah, bana son taurin kai kiyi abinda nace kafin ranki ya baci, a hankali na fara wani irin taku mai cike da burgewa da kayatarwa, a hankali na bude hannayena na fada kirjinsa, shafa gashina kaina yayi tare da dago fuskata yana min wani kallo saurin kawar da kaina nayi saboda duk kunyarsa ta kamani, tafa min naji suna yi tare da cewa kin yi kokari Niimatullah, shi kuwa kin sakina yayi sai da muka fi kusan minti biyar a haka sannan muka hau mota muka tafi.

kallona yayi yana murmushi, lallai idan kika dade a makarantar nan abinda xa a min sai ya fi haka, gashi yau daga xuwa har na fara ganin canji,Gaskiya dole na karawa malama kudi don kwalliya ta fara biyan kudin sabulu, ina turo baki na dube shi.

nifa na fara gajiya da makarantar nan naga akwai takura komai aka koya wai sai an gwada ni Gaskiya baxan iya ba, gashi har wani abu mai daci ta bani da nace baxan sha ba ta takura min wai na faranta maka ne, ni wlh na gaji, shafa fuskata yayi to ai ta haka ne xaki kware Niimatullah idan bakya gwadawa ai sai ki manta, kuma menene don kin sha abinda xaki faranta min ki tuna ni fa aljannarki ne.

kuka na fara yi masa ni baxan koma ba Allah tunda haka ne, lallaba ni ya  shiga yi har sai da na yarda xan koma, yau har cikin gida ya kaini sannan ya tafi nasa gidan.

*jeeddahtulkhair😘*💋💋💋

MATAR DATTIJO CompleteWhere stories live. Discover now